Me ya sa ƴan arewa ke nuna damuwa kan shugabancin Najeriya a 2027?

Asalin hoton, Social Media
Ƴan arewacin Najeriya na tafka muhawara kan ɓangaren da mulkin ƙasar zai koma a shekarar 2027, wani abu da wasu ke ganin kamar ya yi wuri kasancewar gwamnatin da ke kan mulki ba ta cika shekaru biyu a kan karaga ba.
To sai dai masana kimiyyar siyasa na ganin akwai hikima a hakan bisa dogaro da abin da Hausawa ke cewa "da zafi-zafi a kan daki ƙarfe".
Malam Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano, ya ce babu mamaki idan ƴan arewacin ƙasar suka nuna damuwa dangane da yankin da zai jagoranci ƙasar a 2027.
"Ina ga dole ne a samu damuwa dangane da mulkin Najeriya a 2027 daga al'ummar arewacin ƙasar duba da yadda ba su ne ke jagoranci a yanzu ba."
Dalilai biyu da suka sa ake tattauna 2027 tun yanzu
Malam Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa a Najeriya ya ce akwai dalilai guda uku da ke sa ƴan Najeriya fara tattauna batun shugabanci tun da wurwuri.
- Rashin adalci: Malam Kabiru Sufi ya ce yana ganin babban dalilin da ke sa ƴan arewacin ƙasar tunanin mulki a 2027 ba zai rasa nasaba da yadda ɓangaren ke kallon cewa ba a yi masa adalci ba. Kuma ko da dai ɓangaren ba zai samu mulkin ba amma yunƙurin zai iya sa wa a zauna da al'ummar arewacin a tattauna da su kan abin da suke so har ma ta kai ga an yi musu adalci.
- Samun rabuwar kai da rashin samun gamsuwa: Malam Kabiru ya ce yawanci "idan ka ga irin haka, wato a fara tattauna mulkin wa'adin gaba tun gabanin kammala wa'adin da ake ciki na da alaka da yadda ƴan siyasa ke nadama dangane da abun da suka zaɓa kuma hakan ne ke sa ƴansiyasa ƙoƙarin sake shiri da wurwuri.
Daga ina batun ya samo asali?
Al'amarin dai ya fito fili ne tun bayan da sakataren gwamnatin ƙasar, George Akume ya gargaɗi ƴan arewacin ƙasar cewa su jira har zuwa shekara 2031 kafin su fara maganar sake shugabancin Najeriya.
Mista Akume wanda ya faɗi hakan a wata hira a gidan talbijin ya ce "lokacin arewa bai yi ba. Wannan roƙona ne gare su. Kada ku bari a wargaza ƙasar nan saboda muradanku. Wannan shawarata ce ...".
To sai dai wannan gargaɗi na George Akume ya janyo martani daga ƴan arewacin ƙasar daban-daban kamar tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar da wasu ƙungiyoyin arewacin Najeriyar.
Ƴan baruwanmu
To duk da cewa ƴan arewacin ƙasar na ta tofa albarkacin bakinsu dangane da ɓangaren da zai shugabanci Najeriya a 2027, akwai ƴan yankin da suke ganin cewa sam bai dace a mayar da siyasar Najeriya ta ɓangaranci ba.
Sanata malama Ibrahim Shekarau tsohon gwamnan Kano kuma tsohon ɗantakar neman shugabancin ƙasar, na ɗaya daga cikin masu wannan ra'ayi.
Da ya ke tsokaci game da kiraye-kirayen mayar da mulkin Najeriya ga wani ɓangare na ƙasar a hirar sa da gidan talabijin na Channels a Najeriya, Malam Shekarau ya ce "Ya kamata jam'iyyu su fitar da tsari mai kyau na zaɓen wanda ya fi cancanta a tsakanin ƴan takara. Wannan zai bai wa ƴan Najeriya damar darjewa a tsakanin su, domin zaɓen wanda ya fi dacewa da zama shugaban ƙasa''
Malam Shekarau ya ce batun yankin da shugaban ƙasa ya fito ba shi da wani muhimmanci a tsarin shugabanci na gari.
Fa'ida da Illar tattauna 2027 a yanzu
Masana kimiyyar siyasa Farfesa Yahaya Tanko da Malam Kabiru Sufi sun ce mayar da hankali kacokan kan shugabanci a 2027 ƙasa da shekaru biyu bayan kama aikin gwamnati mai ci ka iya haifar da matsi ga ƙasar.
"Ɗauke hankalin gwamnati daga ayyukan da suka kamata ta yi zuwa harkar siyasa inda ake amfani da hukumomi su fara fitar da kuɗaɗen da ya kamata a yi amfani da su wajen gina su fara yin harkokin siyasa da su."
Sai dai kuma masanan sun yarda cewa fara tattauna irin wannan batu da wuri na da tasa fa'idar musamman wajen tilasta gwamnatin samar da irin adalcin da ɗaya ɓangaren yake zargin ana yi masa saboda ƙoƙarin kwantar musu da hankali ta yadda idan zaɓe ya zo gwamnatin ba za ta samu matsala ba.










