Man Utd ta sa Rashford a kasuwa, Salah zai ci gaba da zama a Liverpool

Rashford

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United ta sa ɗan wasanta na Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27 a kasuwa kuma za ta amince da zabtare farashinsa a watan Janairu. (Guardian)

Ɗan wasan gaba a Liverpool da Masar Mohamed Salah, mai shekara 32, na dab da sa hannu a sabuwar yarjejeniyar tsawaita zamansa da ƙungiyar. (Marca - in Spanish)

Southampton na duba yiwuwar gabatar da tayi kan kocin Sheffield mai shekara 35 Danny Rohl daga Jamus bayan korar kocinta Russell Martin. (Times - subscription required)

Kungiyoyin Bayern Munich da Real Madrid da Manchester City sun cire rai a farautar ɗan wasan Jamus mai shekara 21, Florian Wirtz, bayan Bayer Leverkusen ta shirya tsawaita kwantiraginsa har zuwa 2028. (Sky Germany)

Ɗan wasan Ingila Raheem Sterling, mai shekara 30, ba shi da niyyar katse zaman aronsa a Arsenal duk da kalubalen da ya ke fuskanta. (Standard)

Mai tsaron baya a Arsenal, Jakub Kiwior ɗan shekara 24, ya yanke hukuncin rabuwa da ƙungiyar a watan Janairu, kuma Napoli ta nuna zawarcinta kan ɗan wasan daga Poland. (Il Mattino - in Italian)

Manchester United na farautar ɗan wasan Olympiacos na Girka Charalampos Kostoulas, mai shekara 17. (Sun)

Brighton ta gabatar da tayi fam miliyan 20.7 kan ɗan wasan Brazil mai shekara 18, Vitor Reis, sai dai ƙungiyarsa ta Palmeiras tayi watsi da tayin inda take cewa ba ta da niyyar cinikinsa a yanzu sai bayan gasar kofin duniya ta kungiyoyi. (ESPN Brazil - in Portuguese)

Arsenal na bibbiyar ɗan wasan tsakiya a Faransa da Sevilla Lucien Agoume, mai shekara 22, domin maye gurbin Thomas Partey na Ghana mai shekara 31.(FootballTransfers)

Ɗan wasan Faransa da Al-Ittihad Karim Benzema, mai shekara 36, na son ritaya a kakar 2024 zuwa 25. (Relevo - in Spanish)

Tsohon ɗan wasan tsakiya a Sifaniya Cesc Febregas da yanzu kuma ke aikin horas da Como, ya bai wa Dele Alli mai shekara 28 damar ya zo ya rinka atisaye daga watan Janairu, yayinda ɗan wasan ke kokarin farfaɗowa. (ESPN)

Mai tsaron raga a Jamus Manuel Neuer, mai shekara 38, na shirin tsawaita zamansa a Bayern Munich. (Sky Germany)