Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo maku rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/07/2023

Taƙaitattu

  • NAFDAC ta ƙwace haramtaccen maganin feshi na naira miliyan 20 a Sokoto
  • NCAA za ta hukunta kamfanonin jirgin sama da ba su mutumta ƙa'idar lokaci
  • Shugaba Biden ya ƙaddamar da taron NATO karo na 75
  • Shugaban Brazil ya yi kiran gudanar da zaɓe mai inganci a Venezuela
  • An gano ƙarin gawawwaki bayan harin Rasha a Ukraine
  • Za a ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza
  • NERC za ta hukunta kamfanonin rarraba lantarki kan karancin wuta a Najeriya

Rahoto kai-tsaye

Daga Badamasi Abdulkadir Mukhtar da Umar Mikail da Aisha Babangida

  1. An gano ƙarin gawawwaki bayan harin Rasha a Ukraine

    Ma'aikatan gaggawa sun gano karin gawawwakin da barazaguzan gine-gine suka binne, a wata unguwa a birnin Kyiv na Ukraine, wanda hare-haren makamai masu linzami da Rasha ta kai a ranar Litinin ya daidaita.

    Wannan ya kawo adadin wadanda suka mutu a Ukraine a harin na Rasha zuwa 43 a babban birnin kasar.

    An kwashe yawancin matasan da suka ji mummunan rauni daga a wani asibitin Yara da aka lalata a Kyiv, zuwa wasu asibitocin na daban.

    Shugaba Zalensky wanda ke Amirka domin halartar taron kungiyar tsaro ta NATO, ya yi alkawarin sake gina asibitin da sauran gine-ginen da harin na Rasha ya lalata a ranar Litinin.

  2. Shugaban Brazil ya yi kiran gudanar da zaɓe mai inganci a Venezuela

    Luiz Inacio Lula da Silva

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, ya ce ya na fatan a gudanar da zaben shugaban kasa da za a yi a watan nan a Venezuela cikin Lumana, duk da damuwar da 'yan adawa ke nunawa kan yadda ake muzguna musu.

    Da ya ke jawabi a lokacin ziyarar da ya kai Shuga de Silver, ya ce daidaituwar siyasar Venezuela za ta kawo zaman lafiya a kudancin Amirka.

    Ya kara da fatan dukkan wadanda za su fafata a zaben za su rungumi yadda sakamakon zaben ya kasance.

    Shugaba Nicolas Maduro, wanda tun shekarar 2013 ya ke karagar mulki na neman wa'adi na uku ne.

    Kuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuna dantakarar babbar jam'iyyar hamayarra Edmundo González, na sahun gaba, sai dai magoya bayan sa na cike da fargabar gwamnati ka iya dagula lamura a lokacin zaben.

  3. Shugaba Biden ya ƙaddamar da taron NATO karo na 75

    Biden

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Joe Biden na Amirka ya kaddamar da taron kungiyar tsaro ta NATO a karo na 75, tare da alkawarin karin makaman kariya ga Ukraine ciki har da batiran makamai masu linzami.

    A jawabin bude taron kolin mai karfi, Mr Biden ya ce a yanzu kungiyar NATO ta yi karfi fiye da lokutan baya, saboda yadda kasashen kawance ke kashe kudaden tafiyar da ita.

    An yi bushe-bushe da kade-kade a lokacin da shugabannin kawancen suka isa zauren taron, kuma shugaba Biden ya ce kawancen shi ne mafi girma a tarihi.

    Shugaban Ukraine Vlodimire Zalensky na cikin mahalarta taron da batun mamayar da Rasha ta yi wa kasarsa ke cikin batutuwan da za a tattauna a taron.

  4. Barka da zuwa

    Barka da zuwa shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa.