Mece ce ƙungiyar Nato kuma waɗanne ƙasashe ne mambobinta?

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban rundunar kawancen soja, Jens Stoltenberg, ya yi allawadai da shawarar Donald Trump na cewa zai "karfafa wa" Rasha gwiwa ta kai hari kan mambobin kungiyar NATO da suka kasa biyan kudaden da suka dace kan tsaro.
Stoltenberg ya bayyana cewa kalaman Trump na kara saka sojojin Turai da na Amurka cikin hatsari.
Kungiyar tsaro ta NATO da ta hada da kasashen Turai da Arewacin Amurka na kara fadada mambobinta tare da karfafa matakan tsaro a matsayin martani ga mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Mece ce Nato kuma yaushe aka kafa ta?
Nato - Ƙungiya ce da aka kafa ta a shekarar 1949 da kasashe 12, ciki har da Amurka da Birtaniya da Kanada da Faransa.
Manufarta ita ce ta toshe faɗaɗa da Tarayyar Soviet ke yi a lokacin - ƙungiyar ƙasashe waɗanda suka haɗa da Rasha.
Mambobin sun yarda cewa idan aka kai hari kan daya daga cikinsu, to duk sauran kasashe za su taimaka mata - wanda zai iya hadawa da amfani da makami.
Nato ba ta da dakaru na kanta, amma kasashe mambobi na iya ɗaukar matakin soji na hadin gwiwa don magance rikice-rikice. Suna kuma haɗa tsare-tsare na soja tare da gudanar da atisayen soji na hadin gwiwa.
Bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine a watan Fabrairun 2022, Nato ta ce ta kasance "mafi girman barazana kuma kai tsaye ga tsaron kawayenta".
Waɗanne ƙasashe ne mambobin Nato?
Nato tana da mambobi 31 a fadin Turai da Arewacin Amurka.
Bayan rugujewar Tarayyar Soviet a shekarar 1991, ƙasashen Gabashin Turai da dama sun shiga ƙungiyar.
Kasashen sun haɗa da Albania da Bulgaria da Hungary da Poland da Czech Republic da Slovakia da Romania da Lithuania da Latvia da kuma Estonia.
Sweden da Finland sun nemi shiga a watan Mayun 2022, bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine. Ƙasashen biyu dai na fargabar tsaronsu.
Finland, wadda ke da iyakar kasa mai nisan kilomita 1,340 (mil 832) da Rasha - ta zama wakiliya ta Nato a cikin watan Afrilun 2023.
Yanzu Sweden na buƙatar majalisar dokokin Hungary kawai don amincewa da zama mamba.
Bosnia da Herzegovina da Jojiya su ma suna son shiga Nato.
Nawa mambobin Nato ke kashewa kan tsaro?
Nato ta bukaci kasashe mambobin kungiyar da su kashe akalla kashi 2 cikin 100 na kudaden shigar da suke samu a kasar kan tsaro.
Amurka tana kashe kusan sama da kashi 3 cikin 100 kuma kasashen da ke kan iyaka da Rasha - kamar Poland da Jamhuriyar Baltic - suna kashe sama da kashi 2 cikin 100 kan sojojinsu.
Burtaniya tana kashe sama da 2 cikin 100 ne kawai.
Ko yaya ƙasashe kamar Faransa da Jamus da Italiya da Spain suke kashe kudi wanda ya dace da daidai samu daidai kashewa a 2023.
- Poland - 3.9%
- Amurka - 3.49
- Estonia - 2.7%
- Lithuania - 2.54%
- Burtaniya - 2.07
- Faransa - 1.9%
- Jamus - 1.57%
- Italy - 1.46%
- Spain - 1.26%
- Luxembourg - 0.72%
Yaushe Ukraine za ta shiga ƙungiyar Nato?
Nato ta ce Ukraine na iya zama mamba, amma ba ta tabbatar da lokacin da hakan zai faru ba.
Ƙungiyar ta ƙi amincewa da buƙatar Shugaban Ukraine Zelensky na zama mamba cikin "sauri" a watan Satumba na 2022.

Asalin hoton, Getty Images
Rasha dai na adawa da ra'ayin Ukraine na shiga kungiyar tsaro ta Nato, saboda fargabar kada sojojin kawancen su kusanci yankinta.
Kyiv ta amince cewa ba za ta iya shiga kungiyar Nato ba yayin da take yaƙi da Rasha, amma tana son shiga da wuri bayan an kawo karshen fadan.
Tun daga watan Yulin 2023, Majalisar Nato-Ukraine ta hada kai don taimaka wa Ukraine ta kare kanta daga Rasha.
Wadanne makamai ƙasashen Nato ke bai wa Ukraine?
A matsayin kungiya, Nato ba ta aike da makamai zuwa Ukraine ba, amma kasashe da dama sun yi hakan.
Kasashen Amurka da Birtaniya da Jamus da kuma Turkiyya sun samar da makaman yaƙi da tankokin yaƙi da na'urorin kariya na makamai masu linzami da manyan bindigogi da jiragen yaƙi marasa matuka.
Amurka da Birtaniya sun kuma samar musu da makamai masu linzami

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta bar ƙasashen Nato su ba wa Ukraine jiragen yakinta, irin su F-16, tare da bai wa matukan jirgi horo kan yadda ake tuka su.
Netherlands ta ce nan ba da jimawa ba za ta iya jigilar jiragen F-16 18.
Sai dai ƙasashen Nato ba sa tura dakaru zuwa Ukraine, ko kuma amfani da sojojin sama wajen kakabawa yankin hana zirga-zirgar jiragen sama, domin hakan na iya haifar da rikici kai tsaye da Rasha.
Me NATO ke yi kan Rasha?
A cikin 2023, kwamandojin Nato sun amince da cikakken tsare-tsare don tunkarar yiwuwar hare-haren Rasha a yankin Arctic da arewacin Atlantic, tsakiyar Turai, ko yankin Bahar Rum.
A watan Fabrairun 2024, Nato za ta gudanar da ɗaya daga cikin atisayen soji mafi girma tun bayan kawo karshen yaƙin cacar baka.
Atisayen da za a yi a Gabashin Turai zai ƙunshi jami’ai 90,000 daga dukkan ƙasashen Nato 31 da Sweden. Birtaniya za ta aika ma'aikata 20,000.
A baya dai kungiyar tsaro ta Nato ta sanar da shirin kara yawan dakarunta a nahiyar Turai daga 40,000 zuwa sama da 300,000.
Har ila yau, ta ƙarfafa matakan kariya daga gabacinta, mai iyaka da kasar Rasha.
A halin yanzu akwai ƙungiyoyi takwas masu yaki da suka hada da Bulgaria da Hungary da Romania da Slovakia da kuma Jamhuriyar Baltic. Kafin yaƙin Ukraine, akwai ƙasashe hudu ne kawai.











