Arsenal za ta je Old Trafford, domin buga wasan makon farko a Premier League ranar Lahadi.
Wannan shi ne karo na tara da United za ta fara wasan farko a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Wannan shi ne kaka ta 100 da Arsenal za ta buga gasar Lik a Ingila, ta kuma yi nasara biyar daga shida baya a wasan makon farko.
Haka kuma Gunners ta yi wasa 14 a jere a waje ba tare da rashin nasara ba tun bayan da Tottenham ta yi nasara a kanta da ci 1-0 a watan Nuwamba a St James Park.
United ta yi nasarar cin karawa 22 a ranar buɗe gasar lik, kuma wannan shi ne karon farko da za a fafata tsakanin United da Arsenal a makon farko, bayan da ƙungiyar Old Trafford ta ci Gunners 4-1 a 1989/90.
Sabon ɗan wasan da Arsenal ta ɗauka bana Viktor Gyokeres ya zama kan gaba a cin ƙwallaye kaka biyu tsakanin manyan gasar Turai 10. ya ci ƙwallo 68 a wasa 66 a Sporting tsakanin 2023/24 da 2024/25.
United ta yi nasara a kan Arsenal sau 99 a karawa 243 a dukkan fafatawa daga ciki ta yi canjaras 55 aka doke ta 89, kenan United na fatan cin Arsenal karo na 100 a tarihi.