Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aston Villa na son Jackson, Chelsea ta matsa ƙaimi kan Garnacho
Aston Villa na duba yiwuwar sayan ɗan wasan Senegal da ke taka leda a Chelsea, Nicolas Jackson mai shekara 24, amma da wuya su iya biyan abin da ake nema wato fam miliyan 60. (Telegraph - subscription required)
Bayern Munich ta fuskanci tsaiko a farautar ɗan wasan gaba na Faransa Christopher Nkunku mai shekara 27, lamarin da ya haifar wa Chelsea cikas a yunkurinta na sayan ɗan wasan RB Leipzig mai shekara 22, Xavi Simons. (Guardian)
Chelsea na son zage damtse wajen sayo ɗan wasan gaba na Argentina, Alejandro Garnacho daga Manchester United - amma da wuya ɗan wasan mai shekara 21 ya bar Old Trafford a arha. (Evening Standard)
Newcastle ta shirya biyan sama da fam miliyan 40 kan ɗan wasan Brentford, Yoane Wissa amma dole sai dai su biya fam miliyan 60 da ƙungiyarsa ta nema kan ɗan wasan na DR Congo. (Northern Echo)
Ɗan wasan Wolves Jorgen Strand Larsen na son zuwa Newcastle -duk da cewa a yanzu yana nazari da shakun raba gari da ƙungiyarsa. (The Athletic - subscription required)
Tottenham ta shiga zawarcin ɗan wasan Monaco da aka yiwa kuɗi fam miliyan 47.5, Maghnes Akliouche mai shekara 23, maimakon ɗan wasan Brazil Savinho da Manchester City ke son a biya ta fam miliyan 70. (Independent)
Crystal Palace na farautar ɗan wasan nan mai shekara 19 daga Southampton, Tyler Dibling domin maye gurbin, Eberechi Eze mai shekara 27, da ke gab da komawaTottenham. (Talksport)
Ɗan wasan tsakiya na Brazil, Douglas Luiz mai shekara 27, na son komawa Nottingham Forest daga Juventus. (Tuttosport - in Italian)
Leeds na dab da sayan ɗan wasan Switzerland, Noah Okafor mai shekara 25 daga AC Milan kan fam miliyan 18.4. (Sky Sports Italy - in Italian)
Wolves da West Ham na zawarcin Marc Casado na Sifaniya, sai dai da wuya su iya shawo kansa ya bar Barcelona. (Marca - in Spanish)
West Ham na dab da ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya na Mexico mai shekara 27, Edson Alvarez. (Talksport), external
Espanyol na tattaunawa da Burnley kan ɗan wasan nan mai shekara 21, Luca Koleosho. (Sky Sports)
Rodrigo Muniz na Brazil na fuskantar kalubale kan yunkurinsa na son komawa Atalanta daga Fulham. (Fabrizio Romano)