Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarin wasanni daga 16 zuwa 22 ga watan Agustan 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 16 zuwa 22 ga watan Agustan 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Umar Mikail

  1. Boro ta ɗauki ɗan wasan Man City Nypan

    Wani ɗan wasan Manchester City, Sverre Nypan ba zai buga gasar Premier League ba a bana, saboda Middlesbrough ta ɗauki aronsa zuwa karshen kakar bana.

    Mai shekara 18 mai buga wa tawagar Norway ta matasa ƴan kasa da shekara 21 ya koma Etihad daga Roseborg kan fam miliyan 12.5 a watan Yuni.

  2. Tottenham ta tuntuɓi Palace kan ko za ta sayar mata da Eze, kan kuɗin da ya kai fam miliyan 55. (Independent)

    Ita kuma Palace na kokarin ganin ko za ta iya saye ɗan wasan Faransa mai shekara 20, Jeremy Jacquet domin ya maye gurbin Guehi. (Independent)

    Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

    Latsa nan domin shiga

    Karshen Whatsapp

    Aston Villa ta sa ɗan wasan gaba a Chelsea da Senegal, Nicolas Jackson mai shekara 24, cikin waɗanda take farauta amma za ta iya fuskantar kalubale daga Bayern Munich. (Florian Plettenberg)

    Ɗan wasan Manchester United da Ingila, Jadon Sancho mai shekara 25, ya yi watsi da batun zuwa Roma, da ta shirya biyansa fam miliyan 20.(Talksport)

    Kocin Arsenal Mikel Arteta na son sayen ɗan wasan gefe amma dole sai ya sayar da 'yanwasan sa kafin ya iya shiga wani ciniki. (Mirror)

  3. Cinikayyar da aka yi a Premier League kawo yanzu

    Arsenal

    • Kepa Arrizabalaga - from Chelsea - £5m
    • Martin Zubimendi - from Real Sociedad - £60m
    • Christian Norgaard - from Brentford - £10m (£15m)
    • Noni Madueke - from Chelsea - £48.5m
    • Cristhian Mosquera - from Valencia - £13m
    • Viktor Gyokeres - from Sporting - £55m (£64m)

    Aston Villa

    • Yasin Ozcan - from Kasimpasa - £5.9m (£6.7m)
    • Zepiqueno Redmond - from Feyenoord - Free
    • Marco Bizot - from Brest - Undisclosed
    • Evann Guessand - from Nice - £26m (£30.3m)

    Bournemouth

    • Adrien Truffert - from Rennes - £11.4m (£14.4m)
    • Djordje Petrovic - from Chelsea - £25m
    • Bafode Diakite - from Lille - £30.3m (£34.6m)
    • Ben Gannon Doak - from Liverpool - £20m (£25m)

    Brentford

    • Michael Kayode - from Fiorentina - £14.8m
    • Caoimhin Kelleher - from Liverpool - £12.5m (£18m)
    • Romelle Donovan - from Birmingham City - £3m
    • Antoni Milambo - from Feyenoord - Undisclosed
    • Jordan Henderson - from Ajax - Free
    • Dango Ouattara - from Bournemouth - £42.5m

    Brighton

    • Charalampos Kostoulas - from Olympiakos - £29.8m (£31.5m)
    • Diego Coppola - from Hellas Verona - £8.5m
    • Olivier Boscagli - from PSV Eindhoven - Free
    • Maxim de Cuyper - from Club Brugge - Undisclosed

    Burnley

    • Bashir Humphreys - from Chelsea - £12m (£14.7m)
    • Marcus Edwards - from Sporting - £8.5m
    • Jaidon Anthony - from Bournemouth - £7.5m
    • Zian Flemming - from Millwall - £7m
    • Max Weiss - from Karlsruher - £4.3m
    • Quilindschy Hartman - from Feyenoord - Undisclosed
    • Axel Tuanzebe - from Ipswich - Free
    • Loum Tchaouna - from Lazio - Undisclosed
    • Kyle Walker - from Manchester City - £5m
    • Jacob Bruun Larsen - from Stuttgart - Undisclosed
    • Lesley Ugochukwu - from Chelsea - Undisclosed
    • Martin Dubravka - from Newcastle - Undisclosed
    • Armando Broja - from Chelsea - Reported £20m

    Chelsea

    • Liam Delap - from Ipswich - £30m
    • Estevao Willian - from Palmeiras - £29m (£48.5m)
    • Dario Essugo - from Sporting - £18.5
    • Mamadou Sarr - from Strasbourg - £12m
    • Kendry Paez - from Independiente del Valle - £8.3m (£16.6m)
    • Joao Pedro - from Brighton - £60m
    • Jamie Gittens - from Borussia Dortmund - £48.5m
    • Jorrel Hato - from Ajax - £37m

    Crystal Palace

    • Walter Benitez - from PSV Eindhoven - Free
    • Borna Sosa - from Ajax - Undisclosed

    Everton

    • Charly Alcaraz - from Flamengo - £12.6m (£15.2m)
    • Thierno Barry - from Villarreal - £27m
    • Mark Travers - from Bournemouth - Undisclosed
    • Adam Aznou - from Bayern Munich - Undisclosed
    • Kiernan Dewsbury-Hall - from Chelsea - £24m (£28m)
    • Jack Grealish - from Manchester City - Loan
    • Tom King - Wolves - Undisclosed

    Fulham

    • Benjamin Lecomte - from Montpellier - reported £500k

    Leeds

    • Jaka Bijol - from Udinese - £15m
    • Lukas Nmecha - from Wolfsburg - Free
    • Sebastiaan Bornauw - from Wolfsburg - £5.1m
    • Gabriel Gudmundsson - from Lille - £10m
    • Sean Longstaff - from Newcastle - £12m
    • Anton Stach - from Hoffenheim - £17m
    • Lucas Perri - from Lyon - reported £15.6m
    • Dominic Calvert-Lewin - Free agent

    Liverpool

    • Florian Wirtz - from Bayer Leverkusen - £100m (£116m)
    • Jeremie Frimpong - from Bayer Leverkusen - £29.5m
    • Armin Pecsi - from Puskas Akademia - £1.5m
    • Milos Kerkez - from Bournemouth - £40m
    • Hugo Ekitike -from Eintracht Frankfurt £69m (£79m)
    • Giovanni Leoni - from Parma - £26m

    Manchester City

    • Tijjani Reijnders - from AC Milan - £46.3m (£60m)
    • Rayan Ait-Nouri - from Wolves - £31m (£36.3m)
    • Rayan Cherki - from Lyon - £30.5m (£35.6m)
    • Marcus Bettinelli - from Chelsea - Nominal
    • Sverre Nypan - from Rosenborg - £12.5m
    • James Trafford - from Burnley - £27m/£31m*

    *City sources say deal worth £27m, Burnley say £31m

    Manchester United

    • Matheus Cunha - from Wolves - £62.5m
    • Diego Leon - from Cerro Porteno - Undisclosed
    • Bryan Mbeumo - from Brentford - £65m (£71m)
    • Banjamin Sesko - from RB Leipzig - £66.3m (£73.7m)

    Newcastle

    • Antonio Cordero - from Malaga - Free
    • Anthony Elanga - from Nottingham Forest - £55m
    • Park Seung-soo - from Suwon Bluewings - Undisclosed
    • Aaron Ramsdale - from Southampton - Loan
    • Malick Thiaw - from AC Milan - Reported £34.6m
    • Jacob Ramsey - from Aston Villa - £40m

    Nottingham Forest

    • Igor Jesus - from Botafogo - £10m
    • Jair Cunha - from Botafago - Undisclosed
    • Dan Ndoye - from Bologna - Undisclosed
    • Angus Gunn - from Norwich - Free
    • Omari Hutchinson - from Ipswich Town - £37.5m
    • James McAtee - from Manchester City - £30m
    • Arnaud Kalimuendo - from Rennes - Reported £26m

    Sunderland

    • Enzo le Fee - from Roma - £19.3m
    • Habib Diarra - from Strasbourg - £30m
    • Noah Sadiki - from Royale Union Saint-Gilloise - Reported £15m
    • Reinildo Mandava - from Atletico Madrid - Free
    • Chemsdine Talbi - from Club Brugge - Reported £18m (£20.5m)
    • Simon Adingra - from Brighton - £18m (£20.5m)
    • Granit Xhaka - from Bayer Leverkusen - £13m (£17m)
    • Robin Roefs - from NEC Nijmegen - Undisclosed
    • Marc Guiu - from Chelsea - Loan
    • Arthur Masuaku - from Besiktas - Free
    • Nordi Mukiele - from Paris Saint-Germain - (£12m)

    Tottenham

    • Kevin Danso - Lens - £20.9m
    • Mathys Tel - from Bayern Munich - £29.8m (£34.1m)
    • Kota Takai - from Kawasaki Frontale - £5m
    • Mohammed Kudus - from West Ham - £55m
    • Joao Palhinha - from Bayern Munich - Loan

    West Ham

    • Jean-Clair Todibo - from Nice - £36.3m
    • El Hadji Malick Diouf - from Slavia Prague - £19m
    • Kyle Walker-Peters - from Southampton - Free
    • Callum Wilson - from Newcastle - Free
    • Mads Hermansen - from Leicester - £20m

    Wolves

    • Fer Lopez - from Celta Vigo - £19.6m (£21.3m)
    • Jorgen Strand Larsen - from Celta Vigo - £23m
    • Jhon Arias - from Fluminense - £15m
    • David Moller Wolfe - from AZ Alkmaar - £10m
    • Jackson Tchatchoua - from Hellas Verona - £12.4m
  4. Real Madrid za ta kara da Osasuna a makon farko a La Liga

    Bayan kwana 41 tsakani da Real Madrid ta buga wasan karshe a Fifa Club World Cup, za ta fafata da Osasuna a makon farko a La Liga ranar Talata a Santiago Bernabeu.

    Wannan ɗaya ne daga wasa ukun da za ta yi a cikin watan Agusta da ya haɗa da zuwa gidan Oviedo ranar Lahadi da wasa da Mallorca duk a cikin watan nan.

    Sabon koci, Xabi Alonso ya bayyana sabbin ƴan wasa huɗu da Real Madrid ta ɗauka a bana daga cikin waɗanda zai fuskanci karawar da Osasuna.

    Sun haɗa da Huijsen da Trent da Carreras da kuma Mastantuono. Rüdiger ba zai yi wasan ba, sakamakon dakatarwa, yayin da Bellingham da Camavinga da Mendy da Endrick ke jinya.

    OsasunaTa buga wasan sada zumunta shida kan fara kakar nan karkashin sabon koci, Alessio Lisci.

    Haka kuma ta sayi karin ƴan ƙwallo har da matashi daga Real Madrid Víctor Muñoz ta kuma sayi Ander Yoldi da kuma Iker Benito.

  5. Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta buga wasanni a filin wasa na Sani Abacha

    Gwamnatin Kano ta amince ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta riƙa buga wasanninta na gida a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata a gasar firimiyar Najeriya ta bana.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan watsa labarai na ƙungiyar, Ahmad Hamisu Gwale ya fitar, inda ya ce an samu amincewar ce bayan tattaunawa tsakanin hukumar wasanni ta Kano da wakilan ƙungiyar.

    Asali dai ƙungiyar Barau FC tana wasa ne a filin wasa na Dambatta da ke arewacin Kano, wanda a yanzu ƙungiyar ta ce ana gyare-gyare.

    Da yake jawabi kan lamarin, shugaban ƙungiyar, Ibrahim Shitu Chanji ya yi godiya ga Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, "bisa amincewa mu riƙa buga wasanninmu na gida a filin wasa na Sani Abach. Haka kuma hukumar wasanni ta taka rawar gani wajen amincewa da buƙatarmu, sannan muna godiya ga kwamishinan wasanni na Kano, Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso.

    Barau za ta fara wasanta na farko ne da ƙungiyar Enyimba a ranar 24 ga watan Agustan 2025 a filin wasa na Sani Abacha.

  6. Milan tana sha'awar ɗaukar Hojlund daga Man United

    Daraktan wasannin AC Milan, Igli Tare ya tabbatar cewar suna sha'awar ɗaukar ɗan wasan Manchester United, Rasmus Hojlund.

    Ɗan kasar Denmark bai yi wa United wasan da Arsenal ta yi nasara 1-0 ba ranar Lahadi a Premier League.

    Tun can baya ɗan wasan ya sanar cewar yana son ci gaba da taka leda a Old Trafford, sai dai kuma da United ta sayo Benjamin Sesco daga RB Leipzig daga nan aka fara tantama kan makomar ɗan wasan.

    Haka kuma Hojlund ya yi zaman benci a wasan sada zumunta da Fiorentina a Amurka, inda aka yi amfani da Mason Mount a gurbinsa.

    Hojlund ya koma United kan fam miliyan 72 kaka biyu baya, zuwa yanzu ya ci ƙwallo 10 a wasa 52.

    Haka kuma Milan na son sayen ɗan wasan Juventus, Dusan Vlahovic.

  7. Nottingham Forest ta kammala sayen ɗan ƙwallon Rennes, Arnaud Kalimuendo kan kwantiragin kaka biyar kan fam miliyan 26.

    Ɗan kasar Faransa mai shekara 23 ya ci ƙwallo 18 a wasa 34 a bara da Rennes ta kare a mataki na 12 a Ligue 1.

    Tuni dai Forest ta kashe kusan fam miliyan 114 wajen sayen ƴan wasa shida, kafin ɗaukar Kalimuendo.

    A karshen mako ta sayi Omari Hutchinson daga Ipswich Town kan fam miliyan 37.5 da kuma ɗan wasan Manchester City, James McAtee kusan fam miliyan 30.

    A ranar Lahadi Forest ta doke Brentford da cin 3-1 a City Ground a Premier League.

  8. Raducanu da Draper za su fuskanci juna a karawar bibiyu ta na miji da mace, US Open 2025

    Ƴar Burtaniya, Emma Raducanu za ta fuskanci takwaranta, Jack Draper a US Open ta ƴan bibiyu ta mace da na namiji a birnin New York.

    Raducanu mai shekara 22 tana gida ɗaya da Carlos Alcaraz, shi kuwa Draper mai shekara 23 yana tare da ƴar Amurka Jessica Pegula, bayan da Tommy Paul da Paula Badosa suka hakura da wasannin.

    Tun farko an caccaki masu shirya gasar, bayan da suka sanar cewar wasan yan bibiyu na mace da na namiji shi kaɗai za a fara yi daga 19 zuwa 20, sannan a fara babbar gasar daga 24 ga watan Agusta,

    Za a yi taklarar lashe dalar Amurka miliyan ɗaya tsakanin ƙungiya 16.

  9. Watakila Guehi ya koma Liverpool kafin 1 ga watan Satumba, Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Liverpool tana tattaunawa da Crystal Palace, domin a sayar mata da Marc Guehi kan fam miliyan 35, saboda ya koma taka leda a Anfield.

    Har yanzu ba su kai ga cimma yarjejeniya ba, amma ana cewar Liverpool za ta ɗauki Guehi kafin ranar rufe kasuwar cinikin ƴan ƙwallo wato 1 ga watan Satumba.

  10. Za a sa sunan Piastri a wajen zaman ƴan kallo a Australian Grand Prix

    Za a saka sunan Oscar Piastri a wajen zaman ƴan kallo a baɗi a gasar tseren motocin Formula 1 a Australian Grand Prix.

    Mai shekara 24 shi ne kan gaba a tseren bana da tazarar maki tara tatsakaninsa da takwaransa direban McLaren, Lando Norris kuma saura tsere 10 a kammala kakar bana.

    Za a fara kakar shekara mai zuwa a filin Albert Park a birnin Melbourne daga 6 zuwa ga watan Maris ɗin 2026.

  11. , Chelsea 0-0 Crystal Palace

    Tottenham da Crystal Palace na tattaunawa kan cinikin Eberechi Eze, sai dai kawo yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba.

    Wasu na ganin cewar Palace ba za ta saki Eze ba idan har ba ta samu madadinsa ba.

    A ranar Lahadi Palace ta tashi 0-0 da Chelsea a Stamford Bridge a Premier League.

  12. Manchester United na nazari kan miƙa tayinta kan ɗan wasan tsakiya a Crystal Palace da Ingila, Adam Wharton mai shekara 21. (Talksport)

    Inter Milan tayi watsi da tayin yuro miliyan 50 daga Chelsea kan ɗan wasanta na Italiya, Alessandro Bastoni mai shekara 26. (La Gazzetta dello Sport)

    Ɗan wasan tsakiya a RB Leipzig da Netherlands, Xavi Simons mai shekara 22, ya faɗawa ƙungiyarsa yana son zuwa Chelsea, duk da tayin da yake samu daga Bayern Munich da Manchester City. (ESPN)

    AC Milan ta matsa ƙaimi kan saye ɗan wasan Denmark da Manchester United, Rasmus Hojlund mai shekara 22 kan yuro miliyan 35, sai dai kuma tana nazari kan ɗan wasan gaba a Juventus da Serbia, Dusan Vlahovic mai shekara 25. (La Gazzetta dello Sport)

  13. Liverpool ta sayar da ƴan wasa kusan kan fam miliyan 200

    Bournemouth ta amince za ta biya kuɗin ɗan wasan Liverpool, Ben Doak kan kuɗi fam miliyan 25 har da karin tsarabe-tsarabe.

    Ɗan wasan bai buga karawar da Liverpool ta doke Bournemouth 4-2 ba ranar Juma'a, bayan da ƙungiyoyin ke cinikin ɗan wasan.

    Doak ya buga wa Liverpool karawa 10 tun bayan da ya koma Anfield daga Celtic a 2022.

    Kenan Liverpool ta sayar da ƴan wasa kusan fam miliyan 200, bayan da ta kashe sama da fam miliyan 270 wajen ɗaukar sabbi a bana ta kuma tanadi fam miliyan 110, domin biyan kuɗin Alexander Isak, wanda Newcastle ta ƙi sallamarwa.

    Cikin waɗanda Liverpool ta sayar sun hada da Luis Diaz ga Bayern Munich kan fam miliyan 65.5 da Darwin Nunez tga Al-Hilal kan fam miliyan 46.3 da Jarrell Quansah ga Bayer Leverkusen kan fam miliyan 35.

    Sauran da Liverpool ta sayar sun hada da Caoimhin Kelleher da Tyler Morton da Nat Phillips da kuma Trent Alexander-Arnold ga Real Madrid kan fam miliyan .8.4 koda yake Real ta ce kuɗin bai kai haka ba.

    Ita kanta Bournemouth ta ɗauki Dango Quattara daga Brentford kan fam miliyan 42.5.

    Ta kuma sayar da masu tsare bayanta da ya haɗa da Illia Zabarnyi da Dean Huijsen da kuma Milos Kerkez.

  14. Neymar ya sha kuka bayan da aka ci Santos 6-0 a gasar lik ta Brazil

    Ɗan wasan tawagar Brazil, Neymar ya fice daga cikin fili yana sharɓar kuka bayan da Santos tasha kashi da ci 6-0 a gida a hannunVasco da Gama.

    Karon farko da Neymar aka ci su ƙwallaye da yawa a tarihi yana cikin fili, kuma a karon farko da zura ƙwallaye da yawa a ragar Santos kuma a gida a babbar gasar tamaula ta Brazil.

    Tuni ka kori kociya Cleber Xavier, bayan tashi daga wasan na ranar Lahadi, sai dai Santos mai rike da kofin gasar Brazil karo takwas tana da maki biyu tsakaninta da ƴan karshen teburi.

    Xavier, mai shekara 61, ya karɓi aikin a watan Afirilu, bayan da ya yi mataimaki a ƙungiyoyin dake buga gasar lik ta Brazil da kuma a tawagar ƙwallon kafar kasar.

    Santos, wadda ta koma buga babbar gasar tamaula ta Brazil a watan Nuwamba, bayan zama a Serie B ta yi nasara biyar daga karawa 15.

    Ranar 24 ga watan Agusta, Santos za ta buga wasan gaba da Bahia.

  15. Za a buga wasan karshe tsakanin Sinner da Alcaraz a Cincinati Open, Cincinati Open wasan karshe

    A yau Litinin za a buga wasan karshe tsakanin Jannik Sinner da Carlos Alcaraz a Cincinati Open kuma karo na hudu da za su yi tata burza a tsakaninsu a bana.

    Sinner mai rike da kofin, mai shekara 24, wanda ke bikin cikar ranar haihuwarsa ya kai wannan matakin, bayan caskara Terence Atmane da ci 7-6 da 6-2.

    Shi kuwa Alcaraz ya kai bante ne sakamakon doke Alexander Zverez da cin 6-4 6-3.

    Daga wasa ukun da suka fuskanci juna, Alcaraz dan kasar Sifaniya ya yi nasara a Rum da a Roland Garrosd, yayin da Sinner dan kasar Italiya ya lashe Wimbledon Open a cikin watan Yuli.

  16. Mai tsaron raga a Kamaru Andre Onana mai shekara 29, ya sha zaman benci a fafatawar Manchester United a soma Firimiyar Ingila da ta haska da Arsenal, yanayin da ke tabbatar da yunƙurin ƙungiyar na neman dawo da David de Gea mai shekara 34 daga Fiorentina. (Sun)

    Sai dai, United a yanzu ta sa kuɗaɗenta a neman mai tsaron raga na Aston Villa da Argentina, Emiliano Martinez mai shekara 32, da kuma ɗan wasan Paris St-Germain da Italiya, Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26. (Telegraph - subscription required)

    Albashin Jadon Sancho ya kasance abin da ya ke nazari a tafiyarsa Roma daga Manchester United. Ɗan wasan mai shekara 25 daga Ingila na son ganin ko akwai ƙungiyoyin da za su iya bashi abin da ya ke samu duk mako wato £250,000. (Teamtalk)

    Roma ita ma ta tuntuɓi Manchester United kan yarjejeniya da ɗan wasan Netherlands mai shekara 26, Tyrell Malacia, wanda Besiktas ke zawarci. (Fabrizio Romano)

  17. Arteta ya ci United wasa takwas daga karawa 12, Manchester United 0-1 Arsenal

    Bayan da Arsenal ta yi nasara a kan Manchester United da cin 1-0 a Old Trafford ranar Lahadi.

    Kenan Mikel Arteta ya yi nasara a kan Wolverhampton sau tara, sannan ya ci United sau takwas da canjaras biyu aka doke shi karawa biyu daga ƙungiyoyin da ya ci da yawa a Premier League.

  18. Gyokeres ya fara wasan farko a Premier da kalubale

    Viktor Gyokeres ya buga wasan Arsenal a karon farko a Premier League da kai hari sau ɗaya a tarihi tun bayan fafatawar lik 69 da ya yi.

    Wannan rashin kokarin da ya yi sai ka koma watan Afirilun 2023, lokacin da yake taka leda a Coventry City a karawa da Blackburn a wasan da bai kai hari koda ɗaya ba.

  19. Arsenal ta ci gaba da cin ƙwallaye daga kwana

    Tun da aka fara kakar 2023-24, Arsenal ta zura ƙwallo a raga daga kwana sau 31 a Premier League - kenan ta bayara da tazarar 11 da duk wata ƙungiya mai wannan ƙwazon.

    Haka ita kuwa United an zura mata ƙwallo daga kwana guda 23.

    .

  20. Sabbin ƴan wasan United sun yi abin kirki a wasan Arsenal, Manchester United 0-1 Arsenal

    Sabbin ƴan ƙwallon da aka saya sun nuna kansa a Manchester United a wasan farko da suka fuskanci Arsenal kamar Bryan Mbeumo da Matheus Cunha.

    Sai dai wanda Arsenal ta saya fam miliyan 64 daga Sporting, Viktor Gyokeres bai nuna kansa ba, bai kuma yi abin azo a gani ba a fafatawar.