Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarin wasanni daga 16 zuwa 22 ga watan Agustan 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 16 zuwa 22 ga watan Agustan 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Umar Mikail

  1. Kano Pillars ta sayi ƙarin 'yanwasa biyu

    Ƙungiyar ƙwallon ƙfa ta Kano Pillars ta ɗauki ƙarin 'yanwasa biyu domin ƙarfafa tawagar ta mai horarwa Ogenyi Evans kafin fara kakar wasa ta 2025-26.

    A ranar Laraba ta sanar da sayen ɗanwasan tsakiya Olakunle Alaka daga ƙungiyar Akwa United kan yarjejeniyar shekara biyu.

    A ranar dai ta sake sanar da ɗaukar ɗanwasan gaba Aliyu Umar daga Niger Tornadoes kan kwantaragin shekara biyu shi ma.

    Sanarwar na zuwa ne bayan nasarar lashe kofin Gusau/Ahlan da aka fafata a jihar Nasarawa ranar Juma'ar da ta gabata, inda ta doke Plateau United a bugun finareti.

    A ranar Lahadi kuma Pillars za ta fara buga gasar NPFL ta bana a gidan Abia Warriors da ke garin Umuahia na jihar Abiya.

  2. Ba ni da niyyar barin Man United a yanzu - Maguire

    Manchester United ta toshe duk wata kafa da za ta iya bai wa ɗanwasan bayanta Harry Maguire damar barin kulob ɗin a bazarar nan, yayin da shi ma ɗanwasan ya ce da ma ba shi da niyyar barin Old Trafford.

    United ta zaɓi aiki da zaɓin da ke cikin kwantaragin Maguire na watan Janairu, wanda zai sa ya tsawaita zamansa da shekara ɗaya, a daidai lokacin da koci Ruben Amorim ke cewa tawagar tasa "na rasa shugabanni".

    Maguire ya ce akwai ƙungiyoyin da ke sha'awarsa a yanzu, amma mamallaka United sun faɗa masa cewa zai ci gaba da zama daram.

    "A shekarar da ta gabata, ikon na hannunsu," a cewarsa. "Ba ni da wani zaɓi a lokacin. Babu wata magana. Kawai sun yanke shawarar tsawaita yarjejeniyar ne.

    "Ina da tabbacin cewa kulob ɗin yana nufin ba shi son na tafi ne kwatakwata. Wasu 'yan ƙungiyoyi sun tuntuɓa a kaina kuma ina tunanin an ce musu a'a."

    Hakan na nufin kwantaragin Magiure mai shekara 32 zai ƙare a bazara mai zuwa, inda zai samu damar karɓar tayi daga sauran ƙungiyoyi.

  3. Bournemouth ta ɗauki Amine Adli daga Bayer Leverkusen

    Bournemouth ta ɗauki ɗanwasan gefe Amine Adli daga Bayer Leverkusen kan kuɗin da za su kai fan miliyan 25.2.

    Ɗanwasan mai shekara 25 shi ne nja bakwai da ƙungiyar ta ɗauka a wannan bazarar kuma ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar.

    Ɗanwasan na Morocco na buga wasa ne daga gefen hagu, ko daga tsakiya a matsayin lamba 10, ko kuma a gefen dama.

    Adli ya buga wa Leverkusen wasa 143 tare da cin ƙwallo 10 da kuma bayarwa a ci wasu 12 cikin wasa 42 a kakar wasa ta 2023-24.

    Yanzu Bournemouth ta kashe kusan fan miliyan 350 wajen cefanen 'yanwasa, yayin da ta sayar da 'yanwasa uku ga Real Madrid da Liverpool da PSG.

  4. Tottenham na fatan kammala cinikin Eze daga Palace

    Har yanzu Tottenham tana tattaunawa da Crystal Palace, domin a sayar mata da Eberechi Eze.

    Eze ya buga wa Palace wasan Premier League da Chelsea ranar Lahadi, har ma ya ci ƙwallo daga bugun tazara daga baya aka soke.

    Ɗan wasan tawagar Ingila yana da ƙunshin yarjejeniyar fam miliyan 60 da karin fam miliyan takwas na tsarabe-tsarabe ga duk wadda za ta saye shi yarjejeniyarsa ba ta kare ba a Selhurst Park.

    Haka kuma Palace tana tattaunawa kan sayar da Marc Guehi ga Liverpool.

    Da zarar ta cefar da ƴan wasan biyu, zai sa ta kara karfin ƙungiyar, wadda ke fatan sayen Bilal El Khannouss daga Leicester City.

  5. Marseille ta saka Rabiot da Rowe a kasuwa

    Marseille ta saka Adrien Rabiot da Jonathan Rowe a kasuwa, sakamakon halin rashin da'a lokacin da Rennes ta yi nasara a Lique 1 a makon jiya.

    An bayar da rahoton cewa Rabiot ɗan wasan tawagar Faransa da na Norway, Rowe sun tada yamutsi a tsakaninsu bayan tashi daga karawar.

    Marseille ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Rennes wadda ta karasa wasan da ƴan ƙwallo 10 a cikin fili tun a minti na 26.

    An canza Rowa, mai shekara 22 a karawar, yayin da Rabiot mai shekara 30 aka kammala wasan da shi a fili, sun kuma yi hatsaniya ne bayan kammala fafatawar.

  6. Aston Villa na duba yiwuwar sayan ɗan wasan Senegal da ke taka leda a Chelsea, Nicolas Jackson mai shekara 24, amma da wuya su iya biyan abin da ake nema wato fam miliyan 60. (Telegraph - subscription required)

    Bayern Munich ta fuskanci tsaiko a farautar ɗan wasan gaba na Faransa Christopher Nkunku mai shekara 27, lamarin da ya haifar wa Chelsea cikas a yunkurinta na sayan ɗan wasan RB Leipzig mai shekara 22, Xavi Simons. (Guardian)

    Chelsea na son zage damtse wajen sayo ɗan wasan gaba na Argentina, Alejandro Garnacho daga Manchester United - amma da wuya ɗan wasan mai shekara 21 ya bar Old Trafford a arha. (Evening Standard)

    Newcastle ta shirya biyan sama da fam miliyan 40 kan ɗan wasan Brentford, Yoane Wissa amma dole sai dai su biya fam miliyan 60 da ƙungiyarsa ta nema kan ɗan wasan na DR Congo. (Northern Echo)

  7. Salah ne gwarzon ɗan wasan ƙungiyar ƙwararrun ƴan ƙwallo na bana

    Dan wasan Liverpool, Mohamed Salah shi ne ya lashe ƙyautar gwarzon Premier League ta bara da ƙungiyar ƙwararrun ƴan ƙwallo ta karrama.

    Ɗan wasan tawagar Masar, mai shekara 33, shi ne na farko da ya lashe ƙautar karo uku, sakamakon rawar da ya taka a Liverpool da ta kai ta lashe babban kofin tamaula na Ingila a kakar da ta wuce.

    Salah shi ne ya lashe takalmin zinare, bayan zama kan gaba a cin ƙwallaye a Premier League da cin ƙwallo 29 da bayar da 18 aka zura a raga.

    Cikin waɗanda aka bayyana ƴan takara har da Alexander Isak, wanda bai halarci bikin ba, sakamakon takaddama dake tsakaninsa da Newcastle United.

    Ɗan wasan Aston Villa, Morgan Rogers shi ne ya lashe ƙyautar matashin da yafi yin fice a kakar ta ta wuce.

  8. Newcastle United ta kara taya Wissa a karo na biyu

    Newcastle ta kara farashin da ta yi wa ɗan wasan Brentford, Yoane Wissa kan fam miliyan 40.

    Har yanzu ƙungiyoyin na kan ciniki, bayan da Newcastle ta ce za ta biya fam miliyan 35 da karin fam miliyan biyar na tsarabe-tsarabe.

    Tun farko Newcastle ta taya mai shekara 28 kan fam miliyan 30, inda Brentford ba ta sallamar ba.

    A farkon makon nan Wissa ya goge kafar sada zumuntarsa da ta shafi Brentford, wanda ya ƙwallafa rai sai ya koma Newcastle da taka leda a bana.

    Ɗan wasan tawagar Jamhuriyar Congo ya ci ƙwallo 19 a Premier League kakar 2024/25.

  9. Har yanzu Isak ɗan wasan Newcastle ne

    Newcastle ta fitar da jawabi kan kalaman da Isak ya yi a kafarsa ta sada zumunta.

    Mun yi takaici da aka ankarar damu kan wani jawabi a kafar sada zumunta da Alexander Isak ya yi.

    Mun fayyace cewar har yanzu Isak ɗan wasan mune, kuma bamu cimma matsaya da wata ƙungiya ba kan barin Newcastle United a bana.

    Muna fatan ci gaba da buga kakar nan da fitattun ƴan ƙwallon mu, sai dai muna la'akari da burin da ɗan wasa yake da shi muna kuma saurararsu.

  10. Tottenham ta shiga zawarcin ɗan wasan Monaco da aka yiwa kuɗi fam miliyan 47.5, Maghnes Akliouche mai shekara 23, maimakon ɗan wasan Brazil Savinho da Manchester City ke son a biya ta fam miliyan 70. (Independent)

    Crystal Palace na farautar ɗan wasan nan mai shekara 19 daga Southampton, Tyler Dibling domin maye gurbin, Eberechi Eze mai shekara 27, da ke gab da komawaTottenham. (Talksport)

    Ɗan wasan tsakiya na Brazil, Douglas Luiz mai shekara 27, na son komawa Nottingham Forest daga Juventus. (Tuttosport - in Italian)

    Leeds na dab da sayan ɗan wasan Switzerland, Noah Okafor mai shekara 25 daga AC Milan kan fam miliyan 18.4. (Sky Sports Italy - in Italian)

  11. Ba za mu ci gaba da alaka ba - Isak

    Alexander Isak ya fitar da jawabi a kafarsa ta sada zumunta, bayan da aka bayyana shi cikin fitattun ƴan wasan Premier League a kakar 2024/25.

    Dan wasan ya ce ya yi farinciki da ya shiga jerin gwarzayen Premier a a kakar da ta wuce - ya kara da cewar yana son komawa Liverpool da taka leda, amma Newcastle ta kasa cika alkawari kan kwantiragin dake tsakaninsu.

  12. Wolves da West Ham na zawarcin Marc Casado na Sifaniya, sai dai da wuya su iya shawo kansa ya bar Barcelona. (Marca - in Spanish)

    West Ham na dab da ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya na Mexico mai shekara 27, Edson Alvarez. (Talksport), external

    Espanyol na tattaunawa da Burnley kan ɗan wasan nan mai shekara 21, Luca Koleosho. (Sky Sports)

    Rodrigo Muniz na Brazil na fuskantar kalubale kan yunkurinsa na son komawa Atalanta daga Fulham. (Fabrizio Romano)

  13. Ana auna girman raunin Kai Havertz

    Arsenal na jiran ta ji ko Kai Havertz zai yi jinya mai tsawo, sakamakon raunin da ya ji.

    Mai shekara 26 bai yi atisaye ba a Emirates ranar Laraba, yayin da likitocin Arsenal ke auna girman raunin da ya ji.

  14. Inter Milan na bibbiyar yadda lamaru ke kasancewa mai tsaron raga ɗan Kamaru, Andre Onana mai shekara 29, yayinda ake jita-jitar Manchester United za ta raba gari da shi. (Sun)

    Chelsea ta shirya bada aron ɗan wasanta na Ingila, Raheem Sterling mai shekara 30, kuma tana son sayar da wasu 'yanwasa takwas kafin karshen kakar cinikin 'yanwasa.(Telegraph - subscription required)

    Chelsea ta yi watsi da tayin da aka gabatar ma ta daga Bayern Munich kan ɗan wasan gaba a Faransa, Christopher Nkunku mai shekara 27. (Times - subscription required)

    Newcastle za ta gabatar da tayin fam miliyan 35 kan ɗan wasan gaba a DR Congo, Yoane Wissa amma da alama Brentford ba za ta sayar da ɗan wasan mai shekara 28 ba, sai idan har ta samu mai maye gurbinsa. (Sun)

  15. Bayer Leverkusen ta ɗauki aron Echeverri daga Man City

    Bayer Leverkusen ta amince za ta ɗauki aron ɗan wasa, Claudio Echeverri daga Manchester City.

    Ɗan ƙwallon tawagar Argentina ta matasa ƴan kasa da shekara 19 ya buga wa City karawa ukui a kakar da wuce - daga ciki har da FA Cup, wanda Crystal Palace ta yi nasarar doke City.

    Ya ci ƙwallon farko a ƙungiyar a wasan da City ta caskara Al-Ain 6-0 a Fifa Club World Cup a Amurka.

    City ta sayi Echeverri daga River Plate kan fam miliyan 12.5 a Janairun 2024, yanzu zai taka leda a gasar Bundesliga karkashin Erik ten Hag.

  16. Tsohon ɗan wasan Liverpool da Arsenal, Alex Oxlade-Chamberlain ya kasance wanda Birmingham City ke hari daga Besiktas. (Mirror)

    Leeds na gab da cimma yarjejeniya da AC Milan kan ɗan wasan gaba a Switzerland, Noah Okafor mai shekara 25, kan £17.2m (20m euros). (Florian Plettenberg)

    Jamie Vardy mai shekara 38 na son zuwa Celtic kasancewa a yanzu ba shi da ƙungiya tun barowarsa Leicester a karshen kaka. (Sun), external

    Haka zalika ɗan wasan na Ingila Vardy ya kasance wanda ƙungiyar Seria A Napoli ke farauta. (Mail)

  17. Shin wanene Jackson Tchatchoua?

    Sabon ɗan wasan Wolves, Jackson Tchatchoua, ya fara taka leda a Charleroi ta Belgium, wadda ya buga wa karawar farko a cikin shekarar 2021.

    A kakar 2023/24 ya koma buga wasannin aro a Hellas Verona da cewar za ta iya mallakarsa idan ya taka rawar gani.

    Mai shekara 23 ya buga karawa 64 a Hellas da cin ƙwallo biyu da bayar da biyar aka zura a raga.

    A watan Yunin 2024, Tchatchoua ya fara buga wa tawagar Kamaru a wasan da ta doke Cape Verde, wanda kawo yanzu ya yi mata fafatawa 10.

  18. Wissa ya goge kafar sada zumuntarsa da ya shafi Brentford

    Yoane Wissa ya goge kafar sada zumuntarsa ta Instagram da ta shafi Brentford, bayan da ake tantama kan makomarsa a ƙungiyar.

    Ɗan ƙwallon tawagar Congo, wanda bai buga wasan da Nottingham Forest da doke Brentford 3-1 a Premier League ba, yana son komawa Newcastle United da taka leda.

    Ana sa ran Brentford za ta amince ta sayar da Wissa ga Newcastle cikin makon nan, bayan da ta sayi Dango Ouattara daga Bournemouth.

    Sai dai Bournmouth ta yi wa ɗan wasan farashin fam miliyan 60.

  19. Ɗan wasan Aston Villa da Jamaica, Leon Bailey mai shekara 28, na gab da tafiya Roma a matsayin aro. (Corriere dello Sport - in Italian)

    Crystal Palace ta tuntuɓi Leicester kan cinikin ɗan wasan tsakiya a Moroko mai shekara 21, Bilal El Khannouss. (Athletic - subscription required)

    Palace na duba yiwuwar saye ɗan wasan Wolves da Koriya ta Kudu, Hwang Hee-chan mai shekara 29. (Sun)

    Napoli ta shirya shiga fafatawa a cikin ɗan wasan Manchester United da Denmark, Rasmus Hojlund mai shekara 22, wanda ke tattaunawa da AC Milan. (Sport Italia - in Italian),

    Ɗan wasan tsakiya a Brazil, Douglas Luiz mai shekara 27, ya cimma yarjejeniya da Nottingham Forest amma yana jiran Juventus. (Corriere dello Sport - in Italian)

  20. Wolves ta ɗauki Jackson Tchatchoua daga Hellas Verona

    Wolves ta sanar da sayen Jackson Tchatchoua kan fam miliyan 12.5 daga Hellas Verona.

    Tuni mai shekara 23 ya saka hannu kan kunshin yarjejeniyar kaka biyar a Molineux.

    Ɗan wasan tawagar Kamaru, shi ne kan gaba mafi gudu a gasar Serie A a kakar da ta wuce.