Kwamandojin ISWAP biyu sun miƙa wuya ga sojin Najeriya - Su wane ne su?

Asalin hoton, Nigeria Army/X
Wasu manyan kwandojin ƙungiyar ISWAP su biyu sun miƙa wuya ga rundunar sojin Najeriya.
Rundunar sojin ƙasa ta Najeriyar ce ta sanar da cewa mutanen masu suna Ismail Mohammed da Abu Umar da suka miƙa wuya yanzu suna tsare a hannunta kuma suna ci gaba da bayar da bayanai masu muhimmanci, kamar yadda ta sanar.
"Rundunar Operation HADIN KAI sun samu wata gagarumar nasara a yaƙi da take yi da ta'addanci bayan da wasu manyan kwamandojin ƙungiyar ISWAP biyu suka miƙa wuya ga dakarunmu a ranar 8 ga watan Yuni 2026," in ji muƙaddashin jami'in yaɗa labarai na rundunar Haruna Sani.
Ku karanta cikakkun bayani kan kwamandojin a nan.






















