Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni dangane da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 11/05/2025

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage da Isiyaku Muhammed

  1. Zubimendi na daf da komawa Arsenal

    Martin Zubimendi

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Real Sociedad, Martin Zubimendi, mai shekara 26, ya amince zai koma Arsenal - kuma ɗan wasan tawagar Sifaniyar zai je Gunners da zarar ta biya ƙunshin kwantiraginsa (£50.75m).

    Sai dai wasu rahotanni daga Sifaniya na cewa Xabi Alonso, kociyan Bayer Leverkusen ya saka sunan Zubimendi cikin ƴan wasan da zai je da su Real Madrid da zarar ya maye gurbin Carlo Ancelotti.

    A ɗaya gefen, ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ba ta cire rai kan ɗan wasan tawagar Portugal, Bruno Fernandes ba - inda take son sayo shi daga Manchester United.

    Sai dai kocin United, Ruben Amorim na fatan ɗan ƙwallon zai ci gaba da taka leda a Old Trafford.

  2. Putin ya yi tayin tattaunawa da Ukraine

    Putin

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Putin ya yi tayin tattaunawar kai-tsaye da Ukraine a birnin Santambul na ƙasar Turkiyya ranar Alhamis.

    A taron manema labarai da tsakar daren, Mista Putin ya ce Rasha na son tattaunawa kan abin da ya haddasa rikicin.

    Wakilin BBC ya ce ga Rasha ainahin abin da ya haddasa rikicin shi ne kasancewar Ukraine a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, kuma indai haka ne to babu abin da ya ke so face Ukraine ta miƙa wuya.

    Sa'o'i bayan haka - magajin birnin Kyiv Vitaliy Klitschko, ya yi gargaɗin cewa Rasha za ta iya kai hari ta sama kan Kyiv.

  3. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barka da hantsin Lahadi.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin samun labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Ahmad Bawage ne zai jagoranci kawo muku labaran a wannan safiya!