Me ya sa abin da ke cikin hanjinmu ke da alaƙa da ƙwaƙwalwarmu?

Wata mace tana cin abinci

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Andre Biernath
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Hanjinmu na ɗauke da ƙwayoyin halitta fiye da miliyan 100 kuma shi ne ke samar da kashi 95 cikin 100 na ƙwayar halittar neurotransmitter da ke kula da ɓangaren ɗabi'unmu.

A kwanan nan, sabuwar shaida ta nuna cewa akwai tasiri mai yawa dangane da alaƙar hanji da lafiyar jikin ɗan'adam saboda dubban miliyoyin ƙwayoyin cuta da ke zaune a wurin.

Hakan ya nuna irin alaƙar da hanjinmu ke da ita da kuma ƙwaƙwalwarmu.

Amma ta yaya aka samu irin wannan alaƙar? Kuma ko zai yiwu a inganta ta domin samun lafiyar jiki da kuma walwala?

Alaƙar aiki tsakanin hanji da ƙwaƙwalwa

Waɗannan gaɓoɓin biyu na da alaƙa da juna ta hanyoyi uku, a cewar Dr Saliha Mahmood Ahmed, wata likitar hanji kuma jakadiya cibiyar Bowle Reaserach a Birtaniya.

Na farko shi ne lakar vagus, wata laka mai muhimmanci a jikin ɗan'adam da ta haɗa ƙwaƙwalwa kai-tsaye da sauran gaɓobi da yawa kamar zuciya da hanji.

NA biyu, ƙwaƙwalwa da hanji kan sadu da juna ta hanyar taimakon sinadarai. Waɗannan abubuwa, kamar ghrelin da GLP-1, ana samar da su ne bisa taimakon masana'antar sinadarai a jikin mutum (gland) kuma su aika saƙo zuwa sassan jiki gaba ɗaya.

Na ukun shi ne garkuwar jiki.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Mutane da dama na tunanin waɗannan ƙwayoyin halittar na garkuwa na cikin jini ne, amma kuma akasarinsu na aiki ne a hanji kuma a matsayin masu shiga tsakanin ƙwaƙwalwa da duka sauran halittun jiki," in ji Dr Ahmed.

Dr Pankaj J Pasricha, wani ƙwararre a asibitin Mayo da ke Amurka ya bayyana cewa dalilin wannan haɗaka ita ce ƙwaƙwalwa na buƙatar kuzari mai yawa kafin ta iya aikinta kuma hanjinmu shi ne kamar injinta.

Ya ce ƙwaƙwalwa ce ke da kashi 2 cikin 100 na duka nauyin jikinmu amma kuma tana shanye kashi 20 cikin 100 na duka kuzarin jikinmu - kuma aikin hanji shi ne daddatsa abinci zuwa dunƙule-dunƙule domin samar da "makamashi" na aikin.

A wani fannin kuma, ƙwaƙwalwa ce ke jujjuya hanji, amma dai kuma shi ma yana juya ta.

Misali a nan shi ne, duk lokacin da muke shirin aikata wani muhimmin abu, hanjinmu ne yake fara kaɗawa. Mukan ji amai, ko ma gudawa.

Haka nan, idan cikin mutum ya cushe kuma ya kasa yin bahaya tsawon lokaci hakan ka iya haifar masa da rashin natsuwa.

Wasu ababen sha

Asalin hoton, Getty Images

Duniya guda a cikin cikinmu

Hanjinmu na ɗauke da ƙwayoyin cutar bacteria da virus tsakanin 10 zuwa tiriliyan 100.

Wannan adadi ya fi na ƙwayar halitta (cells) da ke jikin ɗan'adam gaba ɗaya.

Ƙwararru sun ce wadannan abubuwa na da alaƙa mai ƙarfi da mu. Suna samun abinci ne daga abincin da muke ci da kuma taimaka mana wajen narkar da abincin, amma sukan taimaka mana wajen niƙa su domin samar da sinadaran da ba za mu iya yin da kanmu ba.

Dr Saliha ta ce sabbin kayan aiki da ake samu ne suka taimaka wajen gano ƙwayoyin cuta masu rai da ke zaune a hanji da kuma fahimtar yadda yin tasiri ga rayuwar wasu ƙwayoyin cuta.

Ƙwararru kan ce nau'ukan abincin da ke ɗauke a ƙwayar cutar bacteria na da amfani wajen narkar da abinci a jikin mutum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙwararru kan ce nau'ukan abincin da ke ɗauke a ƙwayar cutar bacteria na da amfani wajen narkar da abinci a jikin mutum

Hanyar magance matsala

Ganin irin iliman da aka samu a baya-bayan nan da kuma alaƙar hanji da ƙwaƙwalwa, ko zai yiwu a zauna lafiya tsakanin cutukan da ke hanjinmu da sauran halittu?

Dr Saliha ta yi bayanin cewa abu ne mai wuya saboda kowane mutum na da irin tsarin yadda ƙwayoyin bacteria da virus suke a jikinsa.

Amma ƙwararru na cewa akwai abubuwan da ake ganin za su iya yi wa kowa da kowa aiki wajen zaman lafiyar cikinmu. Daga ciki akwai cin daidaitaccen abinci kuma mai lafiya.

Abinci masu ɗauke da wasu ƙwayoyin cutar bacteria da ke taimakawa wajen narkar da abinci - kamar sarrafaffen nonon shanu (yoghurt) - waɗanda kuma suke da harza - kamar 'ya'yan itace - ana bayar da shawarar cin su sosai.

"Zan iya cewa gambiza a abincin da muke ci na da amfani, musamman abincin da suka samo asali daga ganyayyaki," in ji Dr Saliha.

Likitar ta hanji ta bayar da shawarar kowane mutum ya mayar da hankali kan yawan cin kayan marmari, da hatsi, da nau'in ɓawo a kowane abinci.

Likitar ta ce bincike ya nuna cewa jikin ɗan'adam na ƙara lafiya idan yana cin na'ukan ganyayyaki.

Ƙwararru na cewa yin gambiza a abincin da muke ci na da muhimmanci, musamman 'ya'yan itatuwa da kayan miya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙwararru na cewa yin gambiza a abincin da muke ci na da muhimmanci, musamman 'ya'yan itatuwa da kayan miya