Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya 07/04/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Umar Mikail da Isiyaku Muhammed

  1. Ƴanbindiga sun kashe ƴan sa-kai 13 a jihar Kebbi

    Bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya na cewa kimanin mutum 20 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da wasu ƴan bindiga suka kai a wasu garuruwa biyu a jiya Lahadi.

    Lamarin ya faru ne a yankin karamar Hukumar Augie - ɗaya daga cikin yankunan da ake cewa mayaƙan Lakurawa na da sansani.

    Kodayake kawo yanzu ba a tabbatar ko su wa ne maharan ba.

    Ga dai karin bayanin da Jameel Gulma wani ɗan jarida a yankin da ya bibiyi labarin, inda ya ce maharan sun kashe mutum shida ne, suka kwashe shanu, sai ƴan sa-kai suka bi su.

    "A nan suka yi wa ƴan sa-kan kwantan ɓauna, suka buɗe musu wuta, inda suka kashe guda 13 daga cikinsu."

  2. Rashin tallafin Amurka zai ta'azzara mutuwar mata wajen haihuwa - MDD

    MDD

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa rage kuɗaɗen tallafi na iya kawo cikas ga ci gaban da aka samu na rage mace-macen mata a wajen haihuwa.

    Wani rahoto da hukumar lafiya ta duniya ta fitar ya ce mace-macen masu juna biyu da kuma wurin haihuwa ya ragu da kashi 40 cikin ɗari sai dai masana sun ce ci gaban ya ragu kuma ana fargabar adadin zai sake ƙaruwa saboda dakatar da tallafin da Amurka ke bayarwa.

    A shekarar 2023 mata masu juna biyu ɗubu ɗari biyu da sittin aka bayar da rahoton sun mutu, wato kwatankwacin a ce mace ɗaya na mutuwa duk bayan minti biyu.

    Kuma ƙasashen Afrika ne matsalar ta fi ƙamari a ƙasashen Chadi da Najeirya da Somalia

  3. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da safiyar ranar Litinin daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu cigaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.