Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/01/2025.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Isiyaku Muhammed, Usman Minjibir, da Umar Mikail

  1. Za a ƙara kuɗin kiran waya a Najeriya - Gwamnatin Najeriya

    Waya

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da shirin ƙara kuɗin kiran waya da na data, nan ba da jimawa ba.

    Ministan sadarwar ƙasar, Bosun Tijani ne ya bayyana haka a lokacin ganawa da masu ruwa da tsaki a Abuja.

    Ya ce hukumar sadarwa ta ƙasar, NCC ce za ta tsara yadda ƙarin zai kasance.

    Tijani ya ƙara da cewa, “Kafin mu zo da wannan shawara, sai da muka yi la'akari da abubuwa masu yawa na yadda hakan zai taimaka wajen gina ƙasarmu''.

    “Wasu daga cikin abubuwan sun haɗa da tabbatar da inganta hanyoyin sadarwarmu da inganta kamfanoninmu na cikin gida da tabbatar da ɗorewar kamfanonin kansu''.

    ''Haka ma kamar yadda muke ganin hauhawar farashin kayayyaki a duniya, su ma kamfannonin sadarwar na fuskantar wannan matsala, don haka ba za mu bari su durƙushe ba, dole mu yi wani abu don tabbatar da ɗorewarsu'', in ji ministan.

  2. Amurka ta zargi sojojin Sudan da dakarun RSF da tauye haƙƙin 'yan ƙasar

    sojoji

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban wakilin Amurka a Sudan, Tom Periello, ya soki sojojin gwamnati da na 'yan tawayen RSF da ke yaƙi juna, da tauye hakkin 'yan ƙasar na fatan na kafuwar dimukradiyya.

    Mista Periello ya shaida wa BBC cewa Amurka na kira ga dukkan ɓangarorin biyu su amince da yarjejeniyar zaman lafiya, da kafa gwamnatin farar hula kamar yadda 'yan Sudan suka buƙata tun kafin ɓarkewar yaƙin basasa a ƙasar.

    Jami'in na Amurka ya ce za a hukunta waɗanda suka aikata muggan laifuka da kashe-kashen farar hula, hatta masu kamfanonin da ke saida mu su makamai ba za su tsira ba, domin sun ƙara ta'azzara tashin hankalin da Sudan ke ciki.

  3. Isra'ila ta fitar da sabbin dokokin hira da sojojin da ke fagen daga

    sojojin Isra'ila

    Asalin hoton, IDF

    Sojojin Isra'ila sun fitar da sabbin dokokin tattaunawa da sojojin da ke bakin daga ga 'yan jarida, kan fargabar za a iya ɗaukar matakin shari'a a kansu a wata ƙasa kan zargin aikata laifukan yaƙi a Gaza.

    A yanzu za a daina faɗar cikakken sunansu na yanka, a kuma rufe fuskokinsu idan an ɗauki bidiyo.

    Mai magana da yawun sojin Isra'ila ya ce hakan zai kare su daga 'yan gwagwarmaya da ke adawa da Isra'ila.

    A makon da ya wuce wani sojan Isra'ila ya sha da kyar, lokacin ya tafi hutu Brazil inda wani alƙali ya ba da umarnin bincikensa kan laifukan yaƙi bayan wani mai goyon bayan Falasdinawa ya shigar da ƙara kotu.

    Ya bayyana cewa suna da sahihan shaidu da suka haɗa da hotuna har da bidiyo da ke nuna sojan cikin waɗanda suka rusa gidajen Falasdinawa farar hula.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tseye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Barkanmu da sake haɗuwa a wannan shafi domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.