Labaran wasannin BBC Hausa na 7 zuwa 11 ga watan Afrilun 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Talata 7, zuwa Asabar 11 ga watan Afrilun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Abdu, Haruna Kakangi

  1. Fifa na kokarin ganin Iran ta buga gasar kofin duniya a bana, Fifa World Cup

    Fifa World Cup

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Iran ta ce ba za ta yanke hukunci kan halartar tawagar ƙasarta a gasar FIFA World Cup ba sai bayan ta samu amsa daga FIFA dangane da bukatar canza wurin wasannin ta.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Iran (FFIRI) na ƙoƙarin a mayar da wasannin rukuni da take ciki daga Amurka zuwa Mexico, saboda dalilan tsaro da suka danganci rikicin siyasa a yankin.

    A watan da ya gabata, FFIRI ta bayyana cewa tana tattaunawa da FIFA kan sauya wurin wasa, yayin da ma’aikatar wasanni ta Iran ta hana tawagar ƙasar da na ƙungiyoyinta zuwa buga wasa a ƙasashen da take kallon abokan gaba.

    Sai dai shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya sanar a makon da ya gabata cewa Iran za ta buga wasanninta kamar yadda aka tsara.

    A halin yanzu, an tsara Iran za ta buga dukkan wasanninta na rukuni a Amurka – inda za ta kara da New Zealand da Belgium a Los Angeles, sannan ta kammala da wasa da Egypt a Seattle.

    A gefe guda, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Iran za ta iya zuwa Amurka domin buga wasa, amma ya nuna damuwa kan tsaron su, duk da cewa daga baya ya bayyana cewa duk wani barazana ba zai fito daga Amurka ba.

  2. An sa sunan Isak cikin ƴan Liverpool da za su kara da PSG, Champions League

    Alexander Isak

    Asalin hoton, Getty Images

    An saka sunan Alexander Isak cikin ƴan wasan Liverpool da za su buga wasan zagayen farko a kwata fainal a Champions League ranar Laraba da Paris Saint-Germain, bayan shafe mako 15 yana jinya.

    Ɗan ƙwallon mai shekaru 26 bai samu damar buga wasanni yadda aka yi tsammani ba tun bayan sayo shi daga Newcastle a ranar karshe ta kasuwar cinikin ƴan wasa kan sama da fam miliyan 125.

    Isak ya buga wasa 16 kacal a Liverpool, saboda yana kokarin komawa kan ganiya da fama da ƙananan raunuka kafin ya samu mummunan rauni a watan Disamba.

    Ɗan wasan tawagar Sweden ya ji rauni ne a yayin da Micky van de Ven ya yi masa ƙeta a wasan da Liverpool ta doke Tottenham 2-1. Wannan rauni ya kai ga yi masa tiyata a ƙafarsa, inda aka gano karyewar ƙashin kafarsa.

    Rashin Isak ya yi tasiri sosai ga Liverpool, kuma dawowarsa cikin ƴan wasan da za su fuskanci PSG a Champions League na iya zama babban ƙarfafawa gwiwa ga kocin Arne Slot da ke fuskantar matsin lamba.

    Matsin lamba na ƙaruwa kan kocin bayan wasu rashin nasara musamman da Manchester City ta doke su 4-0 a FA Cup zagayen kwata fainal.

    Isak ya koma atisaye a Liverpool ranar Alhamis da ta gabata, kuma ya motsa jiki tare da abokan wasansa a safiyar Talata kafin tafiya Faransa.

  3. Ahmad Diallo ya goyi bayan a bai wa Carrick aikin kociyan Man United na dindindin, Manchester United

    Manchester United

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan wasan Manchester United sun yi imanin cewa Michael Carrick shi ne “mutumin da ya dace” ya jagoranci ƙungiyar na dindindin, a cewar Amad Diallo.

    Carrick ya sauya yanayin yadda ƙungiyar ke taka leda tun bayan da aka ba shi aikin rikon ƙwarya zuwa ƙarshen kakar nan a watan Janairu, inda yanzu United take matsayi na uku a gasar Premier League, kuma ya kusan samun gurbin buga Champions League a kakar mai zuwa.

    Bayan korar Ruben Amorim a farkon shekara, United ke ɗari-ɗarin ɗaukar kociyan dindindin shi ya sa ta bai wa tsohon ɗa wasanta aikin rikon kwarya.

    Da yake magana yayin atisayen ƙungiyar a wajen Dublin, Amad ya nuna goyon bayansa ga tsohon kyaftin ɗin United.

    Ya ce: “Ba aikinmu bane mu yanke hukunci kan makomar sa, amma ya yi abin kirki sosai kuma yana taimaka wa ƙungiyar sosai. Yana da kwarewa kuma ya san abin da United ke bukata. Muna ganin shi ne mutumin da ya dace.”

    Amad ya ƙara da cewa Carrick yana da burin cin nasara da kuma kai ƙungiyar Champions League, kuma yana aiki da kowane ɗan wasa yadda ya kamata.

    Shi ma Bryan Mbeumo ya bayyana jin daɗinsa wajen aiki da Carrick, inda ya ce kocin ya san mecece mu’amala da ƴan wasa saboda ya san ƙungiyar sosai.

    Mbeumo, wanda ya koma United daga Brentford a bara, ya ce zuwa United babban ƙalubale ne a gare shi, kuma yana fatan su kammala kakar bana da kwarin gwiwa da samun gurbin shiga Champions League a kaka mai zuwa.

    A ƙarshe, ƴan wasan United sun nuna cewa suna farin ciki da Carrick a matsayin koci, duk da cewa ba su da ikon yanke hukunci kan wanda zai jagoranci ƙungiyar na dindindin.

  4. Watakila ƴan kallo gasar kofin duniya bashi ya hau kansu kan tsadar tikiti da abin hawa, Fifa World Cup 2026

    Infantino

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabannin magoya bayan tawagogin tamaula sun nuna damuwa cewa magoya bayan da za su je marawa kasashensu a baya a gasar FIFA World Cup a bana za su iya shiga cikin bashi saboda tsadar sufuri da kuma tikitin kallon wasa.

    Magoya bayan Ingila da na Scotland sun riga sun koka kan tsarin farashin, wanda ke sa kuɗin tikiti yake riƙa hawa da sauka bisa ga buƙata. Yanzu kuma an tabbatar cewa kuɗin jirgin ƙasa zuwa filin wasa a Boston zai kai dala 80 (kimanin £60) zuwa da komawa.

    Rahotanni sun nuna cewa farashin da aka saba biya daga Boston South Station zuwa Foxboro Station (wanda ke kusa da filin wasa) kusan dala 20 ne, amma yanzu ya ninka sosai.

    Paul Goodwin, daya daga cikin shugabannin magoya bayan Scotland, ya ce wasu magoya baya za su iya shiga bashi ko amfani da katin bashi domin zuwa kallon gasar cin kofin duniya a Amurka da Canada da kuma Mexico, abin da zai jawo damuwa sosai.

    Ya bayyana cewa wannan lamari yana nuna yadda ƙwallon ƙafa ke ƙara nisa da talakawa, yana mai cewa wannan tsadar ba ta dace ba.

    Scotland za ta fara wasanta da Haiti a Boston ranar 14 ga Yuni, sannan ta sake buga wasa da Morocco bayan kwanaki biyar. Ita kuma Ingila za ta kara da Ghana.

    Ana sa ran dubban magoya bayan Scotland za su je Amurka duk da tsadar, amma suna jin kamar ana cutarsu da kuɗade masu yawa.

    Ƙungiyar magoya bayan ƙwallon ƙafa ta Ingila ma ta nuna rashin jin daɗi kan tsadar sufuri da wajen ajiye abin hawa, inda ajiye mota a filin wasa ke farawa daga dala 175.

    Sai dai hukumar sufuri ta Boston (MBTA) ta kare kanta, tana mai cewa jirgin ƙasa zai kasance hanya mafi sauƙi da arha, kuma za su samar da sabis mai yawa don ɗaukar magoya baya.

    A ƙarshe, an ji cewa wasu magoya bayan Scotland na tunanin hayar bas-bas na makaranta domin rage tsadar tafiya.

  5. Corinthians ta naɗa Diniz sabon kociyanta, Brazil

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Corinthians ta naɗa tsohon kocin Brazil, Fernando Diniz, a matsayin sabon wanda zai horar da ita, bayan da ta kori Dorival Junior sakamakon rashin nasara a wasa takwas a jere a dukkan fafatawa.

    An kori Dorival ne bayan shan kashi 1-0 da suka yi a gida a hannun Internacional a gasar Serie A ta Brazil, hakan ya sa Corinthians ke matsayi na 16, maki biyu kacal tsakani da ƴan karshen teburi.

    Tsohon ɗan wasa Diniz, wanda ya taɓa bugawa Corinthians wasa a baya, ya jagoranci Fluminense zuwa lashe Copa Libertadores a shekarar 2023, kafin ya sake ɗaukar Recopa Sudamericana a shekara ta gaba.

    A wannan lokaci kuma, ya yi aiki a matsayin kocin riƙon ƙwarya na tawagar Brazil na tsawon wata shida, kafin a kore shi a watan Janairu 2024 bayan Brazil ta sha kashi a gida a wasan neman tikitin World Cup a hannun Argentina da ci 1-0.

    Nan gaba Corinthians za ta kai ziyara, domin karawa da ƙungiyar Argentina, Platense, a gasar Copa Libertadores a ranar Alhamis.

  6. Ramsey tsohon ɗan wasan Arsenal ya yi ritaya, Arsenal da tawagar Walaes

    Ramsey

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙyaftin ɗin Wales kuma tsohon ɗan wasan Arsenal, Aaron Ramsey, ya sanar da yin ritaya daga buga ƙwallon ƙafa nan take.

    Ɗan wasan mai shekaru 35, wanda bai da ƙungiya tun bayan barin Pumas UNAM ta Mexico a shekarar da ta gabata, ana sa ran zai fara sabon aiki a fannin horar da tamaula.

    Ramsey ya bar wasa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan ƙasar Wales, inda ya ci ƙwallo 21 a wasa 86 da ya buga, sannan ya wakilci ƙasarsa a manyan gasa uku.

    Ya taka muhimmiyar rawa wajen kai Wales zuwa wasan kusa da na ƙarshe a UEFA Euro 2016, inda har ya samu shiga cikin fitattun ƴan wasan gasar.

    Daga baya ya buga wa Wales UEFA Euro 2020 da kuma FIFA World Cup 2022, wanda shi ne karo na farko da Wales ta kai matakin ƙarshe a gasar cin kofin duniya cikin shekaru 64.

    Ramsey ya fara tamaula ne a Cardiff City kafin ya koma Arsenal a 2008, inda ya shafe shekaru 11 yana taka leda, ya lashe kofin FA Cup uku.

    Bayan haka, ya buga wa Juventus da Nice wasanni, sannan ya je aro a Rangers, inda ya taimaka musu kaiwa wasan ƙarshe a Europa League 2022, duk da cewa ya kasa cin ƙwallo a bugun fanareti a bugun daga kai sai mai tsaron gida a fafatawar.

    Ya kuma sake komawa Cardiff City, inda ya yi aiki na ɗan lokaci a matsayin kocin rikon ƙwarya a ƙarshen kakar da ta gabata.

    Ramsey ya koma Pumas ne da fatan ko zai koma kan ganiya domin ya buga wa Wales a World Cup na wannan shekarar idan sun samu tikiti.

    Sai dai bayan ya kasa samun sabuwar yarjejeniya bayan barin Mexico, ya yanke shawarar kawo ƙarshen rayuwarsa ta buga ƙwallon ƙafa nan take.

  7. Real Madrid v Bayern Munich

    Babu wasu ƙungiyoyi biyu da suka fi karawa da juna a gasar zakarun Turai kamar Real Madrid da Bayern Munich.

    Sun kara sau 28 a gasannin UEFA, inda Real ta yi nasara sau 13, Bayern kuma ta yi nasara sau 11 yayin da aka tashi canjaras sau 11.

    Wannan zai zamo karawa ta 41 da Real Madrid ta yi a matakin kwata-fainal na gasar Champions League, yayin da Bayern kuma ke zuwa matakin a karo na 36.

  8. Maguire ya sanya hannu kan sabon kwantaragi a United

    Harry Maguire ya buga wa Ingila wasa sau 65

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Harry Maguire ya buga wa Ingila wasa sau 65

    Harry Maguire ya sanya hannu kan sabon kwantaragin shekara ɗaya a ƙungiyar Manchester United, tare da yiwuwar ƙara tsawaitawa idan kwantaragin ya ƙare.

    Dama kwantaragin mai tsaron bayan na United zai ƙare ne a ƙarshen wannan kaka.

    A shekarar 2019 ne Maguire ya koma Manchester United daga Leicester City kan kuɗi fam miliyan 80, wanda a lokacin ya kasance ɗan wasan baya mafi tsada a tairihi.

    Ya yi wa United wasa sau 266, inda ya lashe kofin League Cup tare da ƙungiyar a kakar wasa ta 2022-23 da kuma kofin ƙalubale a kakar da ta biyo baya.

    Maguire ya ce “wakiltar Manchester United babban karramawa ce. Wannan abu ne da ni, da kuma iyalina ke alfahari da shi a kullum.”

    Bayan fadi-tashin ganin an ci gaba da yi da shi a ƙungiyar da kuma matakin da tsohon kocin ƙungiyar Erik ten Hag ya ɗauka na karɓe matsayin kyaftin daga hannunsa, an yi ta raɗe-raɗin cewa Maguire zai bar United a shekarar 2023.

    Sai dai daga baya ya riƙa samun damar yin wasa a ƙarƙashin tsohon mai horaswa Ruben Amorim, sannan kuma damar tasa ta riƙa ƙaruwa a ƙarƙashin kocin riƙon ƙwarya Michael Carrick, inda Maguire ke cikin ƴan wasan da aka sanya daga farko a wasanni 10 a ƙarƙashin Carrick.

  9. Barka da warhaka!

    Barka da zuwa shafin labaran wasannin kai-tsaye na BBC Hausa na wannan mako, wato 7 zuwa 11 ga watan Afrilun 2026.

    A wannan mako ne ake yin karawar falle na farko na wasannin kwata-fainal a gasar zakarun Turai ta Champions League.

    Ranar Talata:

    • Real Madrid v Bayern Munich
    • Sporting CP v Arsenal

    Ranar Laraba:

    • Barcelona v Atletico Madrid
    • Paris Saint-Germain v Liverpool