Labaran wasannin BBC Hausa na 7 zuwa 11 ga watan Afrilun 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Talata 7, zuwa Asabar 11 ga watan Afrilun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Abdu, Haruna Kakangi

  1. VAR: BABU FENARITI, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Jose Maria Sanchez Martinez

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ibrahim Konate

    Lafari Jose Maria Sanchez Martinez ya soke fenaritin da ya bayar da kuma katin gargaɗi da ya bai wa Ibrahim Konate.

    Ko haka zai bai wa Liverpool ƙwarin gwiwa?

  2. VAR, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Lafari ya je duba bidiyo domin tantance gaskiya

  3. PSG TA SAMU FENARITI, Paris St-Germain 2-0 Liverpool

    Ibrahim Konate ne ya yi sulu ya ɗebe Zaire-Emery ta baya, nan take lafari ya nuna fenariti.

    Da alamu abubuwa na ƙara dagule wa Liverpool.

  4. ƘWALLO A RAGA: Paris St-Germain 2-0 Liverpool, Minti na 65

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Khvicha Kvaratskhelia ya ja ƙwallo ta tsakiyar difendu ya jefa ƙwallo a raga.

    Wannan zai sa PSG ta numfasa!

  5. , Paris St-Germain 1-0 Liverpool

    A cikin minti biyu da suka wuce ana ta gwagwagwa tsakanin waɗannan ƙungiyoyi biyu.

    Ana kai ruwa rana.

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

  6. , Paris St-Germain 1-0 Liverpool

    PSG ta ɓaras da kyawawan damarmaki guda uku zuwa huɗu kuma tabbas za su ɗora wa kansu laifin rashin ƙara yawan ƙwallaye.

  7. Rashford ya ɓaras da dama mai kyau, Barcelona 0-1 Atletico Madrid

    Rashfaord ya samu wata ƙwallo amma sai ya buga ta a gefen raga.

    Da wuya Barcelona ta sake samun wata dama mai kyau kamar wannan.

  8. , Paris St-Germain 1-0 Liverpool

    Duk da cewa ƴan wasan Liverpool sun ɗan fara da kuzari amma ƴan PSG sun sake karɓe fozeshon inda suke shafa ƙwallo a ɓarayin Liverpool.

    Liverpool kan ɗan taɓa ƙwallo lokaci zuwa lokaci amma suna yin kuskure da yawa.

  9. AN DAWO WASA, Barcelona 0-1 Atletico Madrid

    A Camp Nou ma an take wasa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

    Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

  10. AN DAWO WASA, Paris St-Germain 1-0 Liverpool

    An sake take wasa tsakanin PSG da Liverpool bayan dawowa hutun rabin lokaci.

    Steven Gerrard: Ina ganin kamar Liverpool ta yi abin da za ta iya a farkon lokaci amma ya kamata su ƙara ƙokari.

  11. HUTUN RABIN LOKACI: Barcelona 0-1 Atletico Madrid, Barcelona 0-1 Atletico Madrid

    Barcelona ta yi wasa iyakar wasa amma ƙwallo ta ƙi shiga, daɗin-daɗawa kuma aka kori ɗan wasanta Pau Cubarsi, kuma Julian Alvarez ya zura mata ƙwallo,

    Kai, abin ya yi yawa!

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  12. HUTUN RABIN LOKACI: PSG 1-0 Liverpool, Paris St-Germain 1-0 Liverpool

    Liverpool za ta ji babu daɗi an tafi hutun rabin lokaci tana ƙasa, to amma ƙwallo ɗaya ce kawai, akwai sauran lokacin wasa.

  13. AN CI ƘWALLO- Barcelona 0-1 Atletico Madrid, Minti na 45

    Julian Alvarez ne ya ɗauki bugun tazara mai kyau daga nisan yadi 25.

    Ya yi kwance-kwance ya sharɓo wata ƙwallo kai tsaye zuwa ƙusurwar ƙarfen raga ta sama, babu abin da Joan Garci zai iya yi sai kallo.

    An sha mamaki a Camp Nou!

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  14. AN KORI ƊAN WASA, Barcelona 0-0 Atletico Madrid

    Lafari ya sauya katin gargaɗin da ya bai wa ɗan wasan Barcelona Pau Cubarsi zuwa katin kora saboda ya yi ƙeta don kada a ci ƙwallo da gangan.

    Barcelona ce ta yi bake-bake a filin tana gara ƙwallo yadda take so amma ga shi za ta kammala farkon rabin lokaci da mutum 10.

  15. Barcelona na cin karenta babu babbaka

    Kusan za a iya cewa Barcelona ce ke kiɗanta tana rawanta a fili.

    Tun minti na 11 rabon da Atletico Madrid ta kai wani kyakkyawan hari.

  16. PSG na gara ƙwallo son ranta, Paris St-Germain 1-0 Liverpool

    PSG na da kashi 72% na shafa ƙwallo zuwa yanzu da ya rage kimanin minti 10 a je hutun rabi lokaci.

  17. Simeone ya kasa zaune ya kasa tsaye, Barcelona 0-0 Atletico Madrid

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Diego Simeone ji yake kamar ya faɗa cikin fili! Ya dage, za ka ɗauka cewa shi ne ɗan wasan Atletico na 12.

    Mataimakin lafari na nuna masa cewa kada fa ya zaƙe da yawa.

  18. Rashford ya jefa ƙwallo a raga amma an soke, Barcelona 0-0 Atletico Madrid

    Marcus Rashford

    Asalin hoton, Reuters

    Marcus Rashford ya jefa ƙwallo a raga amma mataimakin alƙalin wasa ya ɗaga tuta kan cewa ya yi satan fage.

    Rashford ya jefa ƙwallon ne wadda ta fito daga ƙafar Lamine Yamal, to amma tun farko Lamine ya yi gaggawa da ɗan taƙi kaɗan, wanda hakan ya sa aka ce yana ofsayid.

  19. Paris St-Germain 1-0 Liverpool, Minti na 11

    Desire Doue ya zura ƙwallo a ragar Liverpool.

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

  20. AN FARA WASA: PSG v Liverpool