Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Premier League: West Ham ta faɗa Championship, Tottenham ta tsallake rijiya da baya

Wannan shafi ne da ke kawo muku wainar da ake toyawa a ranar ƙarshe ta gasar Premier Ingila

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. , West Ham 0-0 Leeds

    West Ham na matsa lamba.

    Kwallon ta je wajen Pablo a cikin yadi na 16 sai dai kan da ya sa ta yi yawa.

  2. GOAL - Burnley 0-1 Wolves, Adam Armstrong

    Ka da ka taɓa yin shakka. Adam Armstrong ya maka kwallon cikin raga ta wuce Max Weiss.

  3. Dalot ya je Brighton don goyon bayan United, Brighton 0-0 Man Utd

    Gabanin wannan wasan an shaidawa Diogo Dalot ba zai buga wannan wasan ba, saboda sauye-sauyen da Michael Carrick yayi.

    Amma ɗan wasan ya bi United zuwa kallon wasan domin nuna goyon bayansa ga United.

    Dalot yana cikin tawagar shugabancin Amorim.

  4. 'Salah ne Sarkinmu', Liverpool 0-0 Brentford

    Wata tuta da aka ɗaga ta nuna cewa 'Daga nasara zuwa ɗukaka. Salah ne Sarkinmu'

  5. , Tottenham 0-0 Everton

    Aikin da ke gaban Tottenham mai sauƙi ne, su yi nasara domin buga Premier mai zuwa.

    Duk wani sakamako bayan wannan zai iya kawo ƙarshen tarihinsu na zama gasar cikin haɗari.

    Mintina 90 da za a buga sun jefa Arewacin london cikin zaman ɗar-ɗar.

  6. Ranar bankwana

  7. Da Kevin Fulham za ta fara wasa, Fulham v Newcastle (16:00 GMT)

  8. Burnley da Wolves duka sun faɗa gasar Championship a bana, Burnley v Wolves (16:00 BST)

  9. Babu Haaland a wasan saboda saye-sauyen da aka yi, Man City v Aston Villa (16:00 BST)

  10. West Ham na buƙatar nasara kan Leeds ko ta halin ƙaƙa, West Ham v Leeds (16:00 BST)

  11. Mo Salah ya yi bayani mai karya zuciya, Liverpool da Brentford (16:00 BST)

    "Na san zuwaciyata za ta karye, zan yi kuka - ko shakka babu," kamar yadda wani magoyin bayan Liverpool Salim ya bayyana lokacin da aka tambaye shi yaya zai ji idan Salah zai yi bankwana.

    A tarihin Liverpool 'yan wasa biyu ne suka ci kwallo sama da Mo Salah da ya ci (257), Ian Rush (346) da Roger Hunt (285).

    Kuma yana cikin manyan 'yan wasan da suka fi yawan cin kwallo a tarihin Premier.

    Shi ko Salah ya ɓata rawarsa da tsalle da rikicinsa da Slot?

    Salim ya ce "sam ko kaɗan, ɗan wasan da ya samu wannan nasara ba zai taɓa ɓata rawarsa da tsalle ba".

  12. Lokacin bankwana, Man City da Aston Villa (16:00 BST)

    Yau Pep Guardiola zai jagoranci Manchester City wasa na 593 - kuma ita ce ranarsa ta ƙarshe a ƙungiyar.

    Rana ta ƙarshe a wani tarihi da kocin ya kafa, na sauya City zuwa ɗaya daga cikin ƙungiyoyin kwallon ƙafa masu ƙarfi a duniya, ya lashe kofina uku a kaka daya, ya kuma sauya matsayin ƙungiyar baki ɗaya.

    Duk abin da zai faru a wasan yau da Villa wani abu ne na tunawa a ranar bankwanan Pep da bajintarsa da tarihin da ya barwa ƙungiyar.

    Ka da ka yi tsammanin za a yi a gama ba tare da zubar da hawaye ba daga magoya baya a fikin wasa na Etihad.

  13. Me zai faru a tseren da ake yi na tikitin Champions League

    Saboda zuwa wasan ƙarshe da Villa ta yi a gasar Europa da yuwuwar ƙungiyoyi shida suje Champions Lig daga Premier a kakar gaba.

    Amma idan har hakan zai faru, akwai buƙatar Villa ta kare Premier a ta biyar.

    A yanzu su ne na huɗu da maki uku tsakaninsu da Liverpool da ke ta biyar. Hakan na nufin Liverpool na buƙatar cinye Brentford domin haye Villa da Emery ke jagoranta.

    Magoya bayan Bournemouth da Brighton na fatan hakan ya faru. Idan kuma ta faru, ɗaya daga cikinsu zai tafi tare da Liverpool zuwa Champions Lig na gaba, ƙungiyoyi shida kenan daga Premier.

    Cherries na buƙatar maki ɗaya ne tal akan Nottenham domin ƙare gasar a mataki na shida.

  14. Wasanni 10 duka za a sa ƙarfe 16:00 BST

    Za a fara wasannin yau ne duka 10 da ƙarfe 4:00 a gogon Najeriya da Nijar da Birtaniya, ƙarfe 3:00 kenan agogon Ghana.

  15. Teburin Premier ta bana

    Yadda teburin Premier yake a yanzu da ya kasance saura wasa guda a kammala gasar.

    Har yanzu akwai sauran runa a kaba.

    Wane ne zai faɗa Champiuonship, wane ne zai samu zuwa Champions Lig, wane zai je Europa da Comference?

  16. Yau ce ranar ƙarshe

    za mu kawo bayanai da sharhi na wasanni 10 da za a fafata a gasar Premier Ingila ta kakar 2025/26.

    Tuni Arsenal ta lashe gasar amma har yanzu ba a samu cikon ƙungiya ɗaya da za ta fada ba, yayin da kocin Man City ke ban kwana da ƙungiyar kazalika Mohamed Sala da Andy Robertson na Liverpool.

    Akwai wasu abubuwa ma da dama.

  17. Wane ne zai tsallake rijiya da baya

    A yau za a kammala gasar Premier Ingila wadda tuni Arsenal suka lasheta, bayan jiran shekara 22.

    An samu ƙungiyoyi biyu da suka faɗa gasar Championship, Burnley da Wolves, yanzu kuma ana neman cikon ƙungiya ɗaya da za ta zama ta uku.

    Tsakanin West Ham United da ke matsayi na 18 da kum Spurs da ke matsayi na 17, maki ɗaya ne ya raba tsakanin ƙungiyoyin biyu.

    Tottenham ko canjaras ta yi za ta tsallake siraɗin, ita kuma West Ham so take a ci Tottenham sannan kuma ta yi nasara ita ma.

  18. Ma su bibiyar mu barka da zuwa ranar ƙarshe ta Premier Ingila.

    Muhammad Buhari Fagge ne zai kasance da ku a wannan rana, domin kawo muku sharhi da bayanan abubuwan da ke faruwa kai tsaye a gasar Premier.

    Ku kasance da mu.