Labari mara daɗi
Tuni labari ya ishi Tottenham da magoya bayanta kan farkewar da West Ham ta yi.
A ko wanne wasa matsin lamba na ƙaruwa.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku wainar da ake toyawa a ranar ƙarshe ta gasar Premier Ingila
Muhammad Buhari Fagge
Tuni labari ya ishi Tottenham da magoya bayanta kan farkewar da West Ham ta yi.
A ko wanne wasa matsin lamba na ƙaruwa.
Taty Castellanos (67 mins)⚽️
A halin da ake ciki West Ham na da kwarin gwiwa.
A ƙarshe dai West Ham ta samu ta ci kwallo ɗaya a bugun kwanar da Jarrod Bowen ya yi shi kuma Taty Castellanos ya jefa ta.
Kallo ya koma kan Everton.........
An kori Wesley Fofana bayan katin gargaɗi na biyu da aka ba shi.
Ya taka ɗan wasan Sunderlamd ne Wilson Isidor abin da ya sa aka kore shi kenan.
Kevin Schade (64 mins)⚽️
An mayar da hannun agogo baya.
Wato kusan duk kwallo a wasannin da ake bugawa tana da tasiri, tana sauya teburi kuma.
Ollie Watkins (63 mins)⚽️
Wannan nasara za ta rikita abubuwa a damar da ƙungiyoyin Premier ke da ita na zuwa Champions Lig su shiga.
Sauyi uku daga Brighton da ke karɓar baƙuncin wasa. Carlos Baleba, Solly March da kuma Charalampos Kostoulas suka maye gurbin James Milner, Diego Gomez da Danny Welbeck.
A gefe guda kuma United ta cire Dorgu ta maye gurbinsa da matashin ɗan wasa Shea Lacey.
Muna ganin ruwan kwallaye tun da aka dawo hutun rabin lokaci.
Ko kwallo nawa za a ci gabanin a ƙare wasannin, a ranar ƙarshe ta Premier.
Curtis Jones (58 mins)⚽️ wannan labari zai yi wa Brighton daɗi ita da ke neman gurbin Europa
Zian Flemming⚽️
Cole Palmer (56 mins)⚽️
Malo Gusto own goal (50 min ⚽️
An dawo hutun rabin lokaci.
Ko Burnley za ta iya farke kwallonta?
Wannan dai wani wasa ne da ake sa ran gani a nan gaba amma a gasar Championship ba Premier ba.
Marcus Tavernier ⚽️
Noni Madueke (48 mins)⚽️
Masu kofi sun ƙara ta biyu. Ko ina Arsenal take a London gida ne saboda ta mamaye birnin.
London ta zama jajawur.
Bruno Fernandes ⚽️
Bruno ya jefa ta uku a wasan a wani hari da suka kai da Dorgu.
Ollie Watkins (47 mins) ⚽️
Aston Villa ba ta yi ƙoƙari ba a minti 45 na farko amma yanzu ta dawo da ƙarfinta.
Yara masu lokaci masu Premier, Arsenal na kan gaba da ci 0-1 a wasan hamayyar Landan.
United da ba ta da matsin komai na kan gaba a wasan.
Abin da kamar wuya, nan da minti 45 idan aka tashi a haka Tottenham za ta buga gasar Premier mai zuwa.