Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Premier League: West Ham ta faɗa Championship, Tottenham ta tsallake rijiya da baya

Wannan shafi ne da ke kawo muku wainar da ake toyawa a ranar ƙarshe ta gasar Premier Ingila

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Hutun rabin lokaci, Sunderland 1-0 Chelsea

    Abubuwan Chelsea na ƙara ja baya, ko da yake muna sa ran ganin sabon mai horaswa da zai kama aiki bayan gasar kofin duniya.

  2. Hutun rabin lokaci, Nottingham Forest 1-0 Bournemouth

    Me zai faru idan aka tashi haka, Nottingham Forest na kan gaba?

  3. Hutun rabin lokaci, Man City 1-0 Aston Villa

    Manchester City na kan gaba a wasan da ci 1-0.

  4. Hutun rabin lokaci, Liverpool 0-0 Brentford

    Babu ci a wasan Liverpool da Brentford

  5. 🥅Tottenham 1-0 Everton

    Joao Palhinha (43 mins) ⚽️

    Ya kamata su samu kwallob tun lokacin da aka sa wasan.

    Joao Palhinha ne ya ci kwallon. Idan aka tafi a haka Tottenham ta sha.

  6. 🥅Crystal Palace 0-1 Arsenal

    Gabriel Jesus (42 mins)

  7. 🥅Brighton 0-2 Man Utd

    Bryan Mbeumo ⚽️

    Amad Diallo ne ya bai wa ɗan wasan kwallo ya ci, Manhester da za ta koma Champions a bana ta mamaye wasan.

  8. Mo Salah ya karaɗe ko ina

    Mo Salah ya karaɗe filin wasan yana nan yana can a ranarsa ta ƙarshe a Liverpool.

    Cikin minti 35 da fara wasan:

    • Taɓawa 36
    • fassin 22
    • Hari uku
    • Ɗaya ya yi raga
  9. Wasu ne za su gasar Europa

    A yadda ake a haka Sunderland za su je gasar Europa.

  10. , Nottingham Forest 1-0 Bournemouth

    Morgan Gibbs-White ya ci kwallo sama da 10 a Premier, wani saƙo ga mai horaswa Thomas Tuchel.

  11. 🥅Brighton 0-1 Man Utd

    Patrick Dorgu ⚽️

    Da ka ɗan wasan ya jefata raga bayan kwaso ta da aka yi daga kwana.

    Ko za ka iya cankar wanda ya ba da kwallon aka ci?

    Kyaftin ɗin Manchester United ya kafa tarihin ba da kwallo a ci 21 a kaka ɗaya, yanzu yana gaban tsohon ɗan wasan City Kevin De Bruyneda na Arsenal Thierry Henry

  12. 🥅Nottingham Forest 1-0 Bournemouth

    Morgan Gibbs-White ⚽️

  13. , Brighton 0-0 Man Utd

    Manchester na son amfani da damar kai hari cikin gaggawa, Bruno Fernandes ya bai wa Amad Diallo sai dai bai iya ɗaukar kwallon ba, ana ta samun kuskure daga wajen United.

  14. , Liverpool 0-0 Brentford

    Dominic Szoboszlai ya bugawa Mo Salah kwallo mai kyai a cikin yadi na 18 sai dai bai taɓa ta yadda ya kamata ba don haka bai ci ba.

    'Yan wasan Liverpool sun ƙagu su ga Salah ya ci kwallo a wasansa na ƙarshe.

  15. 🥅 Man City 1-0 Aston Villa

    Antoine Semenyo (23 mins) ⚽️

  16. Sunderland 1-0 Chelsea

    Trai Hume ⚽️

  17. Wasan ya yi zafi da yawa, Tottenham 0-0 Everton

    Ana buga wannan wasa cikin yanayin zafi da yawa, kowa kamar yana buga wasan ƙarshe na wata gasa, har zuwa wane lokaci ne Tottenham za ta ci gaba da buga wasan a haka.

  18. , West Ham 0-0 Leeds

    Ga yanayin da ake ciki a filin wasa na London, inda magoya bayan West Ham ke ta ihu domin ƙarawa 'yan wasan kwarin gwiwar samun nasarar da suke buƙata.

  19. Fulham 1-0 Newcastle

    Issa Diop (20 mins) ⚽️

  20. , Nottingham Forest 0-0 Bournemouth

    Dan wasan Bournemouth na gaba Evanilson na neman matsa lamba ya ga ya samu ya ci kwallo.