Fubara ya kutsa hukumar zaɓen jihar Rivers yayin da 'yansanda ke 'yunƙurin ƙwace iko' da shi

Asalin hoton, Similanayi Fubara/X
Gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya ce ya daƙile yunƙurin ƴansandan jihar ƙarƙashin jagorancin mataimakin kwamishinan ƴansandan jihar na ƙwace iko da ofishin hukumar zaɓen jihar da tsakar dare.
Cikin wani bidiyo da Gidan Talbijin na Channels ta wallafa, gwamnan ya ce ya je ofishin ne bayan da ya yi zargin cewa wasu jami'an ƴansanda sun yi yunƙurin shiga cikin harabar hukumar zaɓen tare da zargin su da watsa wasu muhimman takardun zaɓen da aka shirya gudanarwa ranar Asabar.
Rahotonni sun ce jami'an tsaron da ke gadin hukumar ne suka sanar da jami'an hukumar da wasu hukumomin gwamnati yunƙurin 'yansanda, waɗanda su kuma nan take suka sanar da gwamnan, wanda shi kuma bai yi wata-wata ba ya garzaya shalkwatar hukumar da tsakar daren.
'Yansandan dai sun ce suna biyayya ga umarnin kotun tarayya da ke Abuja da ta hana gudanar da zaɓen, yayin da shi kuma Gwamnan Fubara ya kafe cewa sai an gudanar da zaɓen.






