Mu kwana lafiya
Nan muke rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye na ranar Juma'a, wanda ya kawo rahotonni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Muna nan tafe da wani sabon shafin gobe da safe.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/10/2024
Usman Minjibir, Abdullahi Bello da Isiyaku Muhammed
Nan muke rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye na ranar Juma'a, wanda ya kawo rahotonni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Muna nan tafe da wani sabon shafin gobe da safe.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.

Asalin hoton, NASS
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sauya lambar girman da ya bai wa kakakin majalisar wakilan ƙasar zuwa GCON bayan 'yanmajalisar sun nuna rashin jin daɗinsu.
Yayin jawabinsa na Ranar 'Yanci a ranar Talata, Tinubu ya sanar da karrama wasu manyan ƙasar ciki har da Kakakin Majalisa Tajedeen Abbas da lambar girma ta CFR, yayin da aka bai wa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ta GCON.
GCON ce lamba ta biyu mafi girma a Najeriya bayan GCFR.
Sai dai hakan ya jawo muhawara a majalisar wakilan a ranar Laraba, inda wakilan suka nemi shugaban ya sauya wa jagoran nasu da lamba mafi girma.
"A madadin haka, [shugaban] ya amine ya sauya wa kakakin lambar da GCON maimakon CFR kamar yadda aka saba," a cewar wata sanarwa a yau Juma'a da mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar.
Sanarwar ta ce 'yanmajalisar sun jawo hankalin shugaban ƙasar kuma ya yanke shawarar gyara "kuskuren da aka yi na saɓa wa daɗaɗɗiyar al'ada".

Asalin hoton, EPA
Kamfanin dillancin labarai na Lebanon ya ce asibiti huɗu sun daina aiki a kudancin ƙasar sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa kan Hezbollah.
Wani asibiti a Beirut ya dakata da aiki sakamakon ɓarnar da hari ta sama da Isra'ila ta kai a kusa da asibitin ya yi.
Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce sansanin da aka tanada da ke iya daukar mutum900 a Lebanon ya cika sakamakon umarnin da Isra'ilar ta ba al'ummar kudancin ƙasar na barin yankin.
Isra'ila ta ce ta yi amannnar cewa ta kashe ƴan Hezbollah 250, yayin da ta tabbatar da kashe sojojinta t0 a fafatawa da Hiezbollah gaba da gaba.

Asalin hoton, EPA
Jiragen yaƙin Amurka sun kai wa sansanonin mayaƙan ƙungiyar Houthi hari a Yemen.
Lamarin na zuwa ne bayan sun yi iƙirarin harbo wani jirgin Amurkar maras matuƙi da ke yawo a sararin samaniyar Yemen a farkon makon nan.
Wata kafar yaɗa labarai mai alaƙa da Houthi ta ce an kai ɗaya daga cikin hare-haren a birnin Sanaa.
Babban birin na Yemen ya ɗan sarara daga hare-hare ta sama cikin shekara biyu da suka wuce bayan yaƙi tsakanin ɓangarori masu yaƙi da juna ya ɗan lafa.
Mayaƙan da ke samun goyon bayan Iran sun sha kai hare-hare kan jiragen dakon kaya a Tekun Maliya tun bayan fara yaƙin Gaza, abin da ya sa Amurka ke jagorantar ƙawancen ƙasashe masu kai musu hare-hare.

Asalin hoton, EPA
An rage hukuncin dakatarwar da aka yanke wa ɗanwasan tsakiyar Faransa Paul Pogba zuwa wata 18 bayan ya samu nasara a ƙarar da ya ɗaukaka a kotun wasanni.
Wasu majiyoyi na kusa da ɗanwasan na Juventus sun shaida wa BBC Sport cewa zai iya komawa atasaye a watan Janairun 2025 kuma zai samu damar komawa taka leda a watan Maris.
Hukumar yaƙi da shan ƙwayoyi masu ƙara kuzari ta Italiya ce ta dakatar da Pogba a watan Fabrairu bayan gwaji ya nuna cewa ƙwayoyin halitta na kuzarin namiji sun yi yawa a cikin jininsa.
Shugaban kotun ta Cas, Matthieu Reeb, ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters cewa an rage dakatarwar zuwa wata 18 tun daga ranar 11 ga watan Satumba.
Tsohon ɗanwasan na Manchester United ya kai ƙarar ga Cas da kansa kuma ya gabatar da hujjoji yayin wani zama a farkon kakar bana.
Tun a baya ya sha faɗa cewa ba zai taɓa shan ƙwayar kuzari "da gangan ba" kuma hukuncin "ba daidai ba ne".
Da a ce ba a rage dakatarwar ba, ba zai sake taka leda ba har sai a 2027, lokacin yana shekara 34 da haihuwa.

Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Najeriya ta fara shirin kwaso 'yan ƙasar daga Lebanon sakamakon da ake yi tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah.
Wata sanarwa da hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa National Emergency Management Agency (Nema) ta fitar a yau Juma'a ta ce ana yunƙurin mayar da waɗanda ke da niyyar komawa gida ne kawai.
Nema ce ke jagorantar shirin wanda ta fara da tantancewa. 'Kuma nan take za a fara cika sharuɗɗan dawo da su," in ji sanarwar.
"Shugaban 'yan Najeriya mazauna ƙasar ya bayyana yadda ofishin jakadancin Najeriya ke taimaka musu musamman game da zirga-zirga, ya kuma ce babu ɗan Najeriyar da ya rasa ransa zuwa yanzu."
Sanarwar ta ƙarƙare da cewa duk ɗan Najeriyan da yake son komawa gida ya kai kansa ofishin jakadancin ƙasar a Lebanon.

Asalin hoton, Reuters
Yayin da ɓaraguzai suka cika babbar hanyar da ta raba ƙasar Lebanon da Syria, 'yan Lebanon ɗin na ci gaba da tsallaka iyakar a ƙafa.
Isra'ila ta ce ta kai harin da ya lalata hanyar ne saboda lalata maɓoyar Hezbollah. Sai dai ma'aikatan lafiya sun ce harin ya sa shigar da kayayyakin da ake buƙata ya yi wahala sosai.
Kafin a katse hanyar, ita ce babbar hanyar shige da fice tsakanin Syria da Lebanon.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Reuters
Kasashen Tarayyar Turai sun amince da karin haraji kan motocin da aka ƙera a China,masu amfani da wutar lantarki.
Matakin ya sha suka sosai, musamman daga Jamus, wacce ke fargabar cewa motocinta da take ƙerawa da ake fitarwa zuwa China na iya fuskantar barazanar ƙarin haraji.
Hukumar Tarayyar Turai ta ce amfani da tallafin da China ke bada wa wajen samar da motoci bai dace ba, kuma yana durƙusar da masana'antun ƙera motoci na Turai.
Mai magana da yawun hukumar Tarayyar Turai, Olof Gill ya ce za su ci gaba da tattaunawa da China wajen ganin an samar da mafita.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce Iran da ƙawayenta ba su jin tsoron yin fito na fito da Isra'ila, duk da kashe shugabannin Hamas da Hizbollah da Isra'ilar ta yi.
Ayatollah Khamenei ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da hudubar Juma'a a babban massalacin Tehran, inda ya ce harin da Iran din ta kai wa Isra'ila halastacce ne kuma ɗan ƙaramin hukunci ne na laifukan da Isra'ilar take aikatawa.
Ya ce, "me ya kamata mu yi ? daga ɓangaren ƴan siyasa da dakarun soji da kuma sauran hukumomi, duk za mu hadu mu dauki matakin da ya dace, a lokacin da ya dace kamar dai yadda muka saba yi a baya."
Shugaban addinin ya kuma yi wa shugaban Hizbollah da aka kashe Hassan Nasrullah addu'a tare da jinjina masa.
Ministan harakokin wajen Abbas Araghchi ya isa Lebanon domin ganawa da shugaban siyasar ƙasar.
Wannan ne karon farko da jagoran addunin na Iran ya yi huɗubar Juma'a, tun bayan kisan da Amurka ta yi wa kwamandan dakarun juyin juya hali Qassem Soleimani a Janairun 2020.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Ecowas ta ce tana shirin kafa runduna ta dakaru 5,000 domin yakar ta'addanci a yankinta na yammacin Afrika.
Shugaban hukumar Ecowas Omar Touray wanda ya bayyana haka a wani taron tsaro da aka gudanar a Abuja ya ce an kai hare-hare 1,605 tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2024 a yammacin Afirka, kuma an samu hasarar rayuka 6,956.
Ya ce, "bisa umarnin shugabannin ƙasashen Ecowas, akwai yunƙuri da ake na samar da runduna ta dakaru 5,000 domin yaƙi da ta'addanci."
Mali da Burkina Faso da Niger da Nigeria ne ƙasashen da matsalar tsaro ta fi addaba a yankin.
Mista Touray, ya ce a Burkina Faso an kai hare-hare 611 attacks inda aka kashe mutum 3,810. A Mali na kai hare-hare 546 inda aka kashe mutum 1424.
A Najeriya kuma an kai hare-hare 238 yayin da kuma aka kashe mutum 905, sai Nijar inda aka kai hare-hare153 tare da samun hasarar rayuka 676.
An kuma kai hare-hare 44 a Benin da hasarar rayuka 66. Sai Togo inda aka kai hare-hare 13 da hasarar rayuka 75.

Asalin hoton, Twitter/@govborno
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya bayyana takaicinsa a kan yadda mutane suke gina gidaje a magudanar ruwa a jihar.
Zulum ya bayyana haka ne a ranar Alhamis bayan ya kai ziyarar duba ɓarnar da ambaliyar - wadda ta ɗaiɗaita jihar - ta yi ga hanyoyin mota da gadoji da asibitoci da sauransu.
A cewarsa, "Ɓarnar ta yi yawa. Mun ziyarci wurare da dama mun gani. Akwai ban takaici yadda mutane suke gina gidaje a magudanar ruwa. Ba don a tare masa hanya ba, da ruwan zai riƙa bin hanyarsa yana wucewa ne.
"Duk da gargaɗin da ake yi, amma har yanzu mutane suna cigaba da gini a magudanar ruwa, wanda irin waɗannan matsalolin ne suka jawo ambaliyar. Ba za mu watsar da kula da rayuwar mutanen Maiduguri ba saboda wasu ɗaiɗaikun mutane," in jij shi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A ƙarshe ya yi kira ga ma'aikatar aikace-aikace da jami'an tsaro su tabbatar babu wanda ya sake yin gini a magudanar ruwa a jihar.

Asalin hoton, FACEBOOK/Abba Kabir Yusuf
A jihar Kano, ana ci gaba da zaman makoki da alhinin rasuwar mutum bakwai waɗanda suka rasu a sakamakon cutar kwalara da suka kamu da ita bayan sun sha ruwan wata rijiya a wani ƙauye.
Bayanai na cewa lamarin ya auku ne sanadiyyar gurɓacewar ruwa sakamakon ambaliyar ruwa daga wani kudiddifi da ke kusa da rijiyar kuma kawo yanzu mutum fiye da 10 ne suke kwance a asibiti suna karɓar magani.
Bayanan daga ƙauyen Kanye da ke ƙaramar hukumar Kabo a jihar Kano na cewa mutanen garin sun fara ganin waɗanda suka harbu da cutar ta kwalara ne a unguwar da rijiyar take bayan da wasu magidanta suka yi amfani da ruwan rijiyar kuma suka kwanta rashin lafiya.
Kwamishinan lafiya na jihar ta Kano, Dokta Abubakar Labaran Yusuf ya ce ba shi da cikakken bayani tukuna, amma zai tura jami’ai don ƙara kai ɗauki da kuma bincike.
Sai dai bayanai na cewa a baya-bayan nan an samu mutuwar ɗimbin mutane a sassan jihar Kano sakamakon ɓullar cutar kwalara, inda hukumomi suka tabbatar da cewa cikin fiye da mutum 600 da ake fargabar sun kamu da cutar fiye da 30 ne suka mutu.
Ma'aikatar lafiya ta bayyana cewa ana kyautata zaton cewa ambaliyar ruwan da aka samu zuwa cikin wasu rijiyoyi ne ta haddasa kwalarar da ta yi sanadin mutuwar mutanen amma sun ce sun saka magani a wuraren.

Asalin hoton, EPA
An fara kai kayayyakin agaji zuwa babban birnin Beirut na Lebanon, kamar yadda rundunar sojin Lebanon ta wallafa a shafinta na X.
BBC ta ga wasu hotuna, waɗanda wasu ke ɗauke da tambarin Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO.
A jiya Alhamis ne darakta-janar na WHO ya yi kira a samu haɗin ƙarfi da ƙarfi wajen kai kayayyakin agajin da ake buƙata zuwa Lebanon.
Wannan tallafin na farko ya iso ne daga Romania.

Asalin hoton, EPA

Asalin hoton, Reuters
Rundunar Tsaron Isra'ila wato IDF ta ce ta kashe mambobin Hezbollah guda 250 a cikin kwana huɗun da suka gabata.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da IDF ɗin ta fitar, inda ta ce, "a kwana huɗu da suka gabata, IDF ta kashe ƴan Hezbollah 250, daga cikin su guda 21 kwamandoji ne," kamar yadda sanarwar ta nuna.
Sanarwar ta ƙara da cewa sun kai hare-hare a wuraren mayaƙan ƙungiyar sama da 2,000, inda ta ce sun yi mayar da hankalinsu a kan kudancin Lebanon.

Asalin hoton, AP
Aƙalla mutum 20 ne suka rasu, ciki har da ƙananan yara bayan ƴandaba sun kai wani hari a ƙauyen Pont-Sonde da ke yankin Artibonite a ƙasar Haiti, sannan wasu kusan 50 suka jikkata.
Wani faifan bidiyo da aka fitar ya nuna yadda mutane suke ta gujde-guje, sannan babban mai gabatar da ƙara na gwamnatin ƙasar ya bayyana harin a matsayin "kisan kiyashi" kamar yadda Associated Press suka ruwaito.
Ƴandaban dai suna neman mamaye yankuna da dama na Haiti, wanda hakan ya sa dakarun Kenya, da ke samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya suka isa ƙasar domin fatattakarsu.
Har yanzu ba a tantance adadin waɗanda suka mutu ba, amma wasu kafofin sadarwa na cikin ƙasar sun ruwaito cewa an kashe sama da mutum 50, amma gamayyar ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam na ƙasar sun ce waɗanda suka rasu ba su wuce 20 ba, kamar yadda AP ta ruwaito.
Ƙungiyar Grant Grif na cikin miyagun ƙungiyoyin ta'addanci a Haiti. A shekarar 2023 an zarge su da kai hari ofishin ƴansanda, inda suka kase ƴansanda shida, sannan an zarge su tursasa rufe wani asibiti da ke ɗauke da majinyata 700,000.
Mambobin ƙungiyar, waɗanda ba su wuce 100 ba, an zarge su da kashe-kashe da fyaɗe da garkuwa da mutane, kamar yadda ahoton Majalisar Ɗinkin Duniya da AP ta kalato ya nuna.

Asalin hoton, Rivers State Government Press
Rikicin siyasa da ya ƙi, ya ƙi cinyewa a tsakanin gwamnan jihar Rivers Sim Fubara da tsohon ubangidansa, ministan Abuja Nyesom Wike ya ɗauki sabon salo a sanadiyar zaɓen ƙananan hukumomin jihar, wanda za a yi gobe Asabar.
Tun a shekarar 2023 ce shugabannin biyu suke takun-saƙa a kan jan ragamar jihar, lamarin da ya sa siyasar jihar ta ɗauki zafi, har ta zama abar kallo da magana a faɗin ƙasar.
Tuni ɓangaren Wike suka ce ba za a yi zaɓen ba, su kuma ɓangaren gwamna Fubara suka ce babu gudu, ba ja da baya sai an yi.
Tun a farko-farkon mulkin Fubara aka fara rikici a game da shugabannin ƙananan hukumomi, inda bayan wa’adin waɗanda Fubara ya gada daga Wike ya ƙare, ya buƙaci su tafi, su kuma suka ce allambaran suna da sauran lokaci, ana cikin wannan ne ya sanar da naɗa shugabannin riƙon ƙwarya domin su maye gurbin waɗancan, lamarin da ya tayar da tashin hankali a jihar.
Tun a lokacin da aka gudanar da zaɓen shugabannin PDP na jihar Rivers ne aka fara hango wannan rikicin na zaɓen ƙananan hukumomi.
A zaɓen, tsagin Wike na PDP ya samu a nasara a kan tsagin Fubara, lamarin da ya haifar da saɓani mai girma tsakanin Wike da ƙungiyar gwamnoni, har Wiken ya yi barazanar kunna wutar siyasa a duk jihar da ta sa baki a jiharsa.

Asalin hoton, Tinubu/X
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce za a cigaba da luguden wuta a kan ƴanbindiga da ɓarayin daji da masu satar man fetur da sauran ɓata-garin da suke addabar Najeriya matuƙar ba su daina ta'addancin da suke yi ba.
Tinubu ya bayyana haka ne a jiya Alhamis a cibiyar samun horo na sojoji ta Army Resource Center da ke Abuja a wajen taron tattaunawa a kan matsalolin tsaro a Najeriya da hanyoyin magance su wanda kamfanin dillanci na Najeriya NAN ya shirya a ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulsalami.
Tinubu wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce, "shekara 15 ke nan muna fama da rashin tsaro a Najeriya. Mugayen mutane suna yadda suke so. Amma yanzu lokaci ya zo da dole su dakata haka.
"A cikin shekara ɗaya, an kashe sama da kwamandojin Boko Haram 300, sannan an samu sauƙin garkuwa da mutane domin kuɗin fansa. Don haka wannan gargaɗi ne gare su, sun dai ga yadda aka yi da kwamandojinu, don haka idan suka ƙi miƙa wuya, za su fuskanci abun da ya faru da jagororinsu.
"Ƙofarmu a buɗe take ga duk wanda yake so ya miƙa wuya, idan ba haka ba kuma, sun san abin da zai biyo baya," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar lafiya ta jihar Borno ta ayyana ɓarkewar annobar kwalara a faɗin jihar, inda aka fargabar fiye da mutum 450 sun kamu amma an tabbatar da kamuwar mutum 17 kawo yanzu.
Kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Baba Gana ne ya bayyana hakan lokacin da yake ayyana ɓarkewar annobar, inda ya ce daga cikin gwaji fiye da 200 da aka yi, 17 sun kamu da cutar.
Kwamishinan ya ƙara da cewa ɓarkewar cutar dai ya faru ne sakamakon annobar ambaliyar ruwa da ta ɗaiɗaita ɗaruruwan ƴan jihar.
Farfesa Baba Gana ya ce an samu ɓarkewar cutar a ƙananan hukumomin Jere da Mafa da Konduga da Dikwa da Ƙaramar Hukumar birnin da kewaye.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da wani sabon gwajin gaggawa na cutar kyandar biri, wanda ake fatan zai taimaka wajen daƙile yaduwar cutar.
Gwajin dai yana ba da damar gano kwayar cutar daga fatar jikin danadam. Hukumar ta ce ƙarancin kayan gwaje-gwaje ya taimaka wajen yaduwar cutar a Afirka.
A halin yanzu dai an saki alluran rigakafi guda miliyan shida don yaƙar barkewar cutar wadda ta fi ƙamari Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, inda aka kaddamar da aikin rigakafi a wannan makon.
Dakarun Isra'ila sun ce sun kashe kwamandan Hezbollah na sadarwa, Muhammad Rashid Skafi a wani luguden bama-bamai da suka kai Beirut a jiya.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce Skafi ya kwashe shekaru 24 a ƙungiyar kuma makusanci ne ga manyan jagororin Hezbollah.
Ƙungiyar ta Hezbollah dai ba ta uffan ba tukunna.