Najeriya za ta kara da Morocco a daf da karshe a Afcon

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku bayanai kan wasan Aljeriya da Najeriya zagayen kwata fainals a gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 da ake yi a Moroko.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. , Aljeriya 0-0 Najeriya

    Ɗan wasan Aljeriya, Rayan Aït-Nouri ya yi laifi, an kuma busa

  2. , Aljeriya 0-0 Najeriya

    Akor Adams daga Najeriya ya buga ƙwallo da kafar hagu amma ba ta da wani hatsari.

  3. , Aljeriya 0-0 Najeriya

    Riyad Mahrez na Aljeriya ya samu bugun tazara zuwa gidan Najeriya.

  4. , Aljeriya 0-0 Najeriya

    An gama duba lafiyar mai tsaron raga an ci gaba da wasan har yanzu ba ci Aljeriya da Najeriya zagayen kwata fainal.

  5. , Aljeriya 0-0 Najeriya

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana duba lafiyar mai tsaron ragar Aljeriya, Luca Zidane.

  6. , Aljeriya 0-0 Najeriya

    Calvin Bassey na Najeriya ya buga ƙwallo da ƙafar hagu daga gefen hagu daf da shiga da'ira ta 18, amma an tare shi. Ademola Lookman ne ya kawo ƙwallon ta bugun kusurwa.

  7. , Aljeriya 0-0 Najeriya

    An bai wa Mohammed Amoura na Aljeriya katin gargaɗi.

  8. Najeriya ta kai kora, Aljeriya 0-0 Najeriya

    Ademola Lookman (Najeriya) ya buga ƙwallo da ƙafar dama daga gefen hagu, amma mai tsaron raga, Luca Zidane (Aljeriya) ya tsare ta a kusa da kusurwar hagu. Akor Adams ne ya bayar da ƙwallon.

  9. Mun ɗan samu tangarda amma komai ya koma daidai, Afcon Morocco 2025/26

    Jama'a sai a yi mana hakuri sakamakon tangarɗar da muka samu amma komai ya koma daidai za mu ci gaba da kawo muku sharhi da bayanan wasan Aljeriya da Najeriya ba ci har yanzu

  10. Yan Super Eagles da za su fuskanci Aljeriya, Afcon Morocco 2025/26

    Afcon

    Asalin hoton, BBC Sport

  11. Ƴan wasan da za su buga wa Aljeriya wasan Najeriya, Afcon Morocco 2025/26

    Afcon

    Asalin hoton, BBC Sport

  12. Morocco ta kai zagayen daf da karshe a Afcon, Afcon Morocco 2025/26

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu masaukin baki, Morocco ta samu tikitin zuwa wasan daf da ƙarshe a Gasar Kofin Nahiyar Afirka ta 2025, bayan doke Kamaru a Rabat, kamar yadda BBC ta ruwaito. an ci ƙwallon farko kan hutu ta hannun Brahim Diaz, sannan ta biyu a zagaye na biyu ta hannun Ismael Saibari.

    Da wannan nasarar, tawagar da Regragui ke jan ragama ta kai matsayin da ta taɓa kaiwa a baya zuwa wasan kusa da na ƙarshe a gasar kofin duniya a Qatar a 2022 da zuwa daf da karshe.

    Yanzu nasara biyu kacal ta rage mata kafin ta lashe kofin nahiyar na farko tun 1976 rabonta da shi.

    Kawo yanzu Morocco ba ta sha kashi ba a wasa 25 a jere—tun daga lokacin da ta fice a zagayen ƴan 16 a gasar Afcon a 2023—kuma ta kai wasan daf da ƙarshe a AFCON karo na farko tun 2004, lokacin da ta sha kashi a hannun Tunisia a wasan ƙarshe.

    Atlas Lions za ta nuga zagayen daf da karshe ranar Laraba da duk wadda za ta yi nasara a karawa tsakanin Aljeriya da Najeriya ranar Asabar.

  13. Ƴan wasan Najeriya da ke taka rawar gani a Morocco, Afcon Morocco 2025/26

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Tun kan fara Afcon an sa ran Victor Osimhen ne zai taka rawar gani a wasannin bana, sai dai kuma Ademla Lookman ne ke haskawa a tawagar ta Super Eagles.

    Tun kan kammala gasar ana cewa Lookman ne fitatcen ɗan wasa a Afcon a Morocco, wanda ya ci ƙwallo uku kawo yanzu da bayar da huɗu aka zura a raga.

    Haka kuma Lookman na aiki ne a matakin mai baiwa ƴan gaba ƙwallo, sannan ya taimaka wajen tsare gida, hakika Lookman na nuna kansa a wasannin da ake buga wa a bana

    Har yanzu ana ganin Osimhen bai kai kan ganiya ba a gasar nan, domin yadda ya ƙware a zura ƙwallo a raga ya kamata waɗanda ya ci a Morocco su haura ukun da yake da su.

    To sai dai a duk wasa yana sa ƙwazo yana damun masu tsare baya da kazar-kazar da ɓarar da damar maki, kenan Super Eagles ba ta samun matsi da yawa idan yana cikin fili.

    Haka shima ɗan wasan gaba Akor Adam yana nuna kansa, wanda ya ci ƙwallo ya kuma bayar da biyu aka zura a raga, kuma Alex Iwobi yana raba ƙwallo tun daga tsakiya da kuma Wilfred Ndidi da yake da matukar mahimmancin a wasannin Najeriya.

  14. Senegal ta kai daf da karshe a Afcon bayan cin Mali a Morocco, Afcon Morocco 2025/26

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Iliman Ndiaye ne ya ci kwallon da ya bai wa Senegal nasarar doke Mali, wadda ta kare wasan da ƴan ƙwallo 10 da ci 1–0 a ranar Juma’a zagayen kwata fainals

    Lamarin da ya ba su damar shiga wasan daf da ƙarshe a Gasar Kofin Nahiyar Afirka Afcon karo na uku cikin gasa huɗu a baya-bayan nan.

    Ndiaye ya zura ƙwallo bayan minti 27 da fara wasa.

    An rage wa Mali ɗan wasa ɗaya bayan da aka kori ƙyaftin, Yves Bissouma da aka yiwa jan kati, sakamakon katin gargadi na biyu da ya karɓa a daf da tafiya hutun rabin lokaci.

    Tun farko an ba shi katin gargadi ne saboda mummunan ƙetar da ya yi a minti na 25, sannan aka kore shi bayan da ya yi wa Idrissa Gana Gueye keta

    A wasan da ya gabata tsakaninsu da Tunisia a zagaye na biyu, Mali ta kammala karawa da ƴan wasa 10 a ciki filin, inda ta kai zagayen gaba a bugun fenariti da cin 3-2, bayan da suka tashi 1-1 har da karin lokaci.

  15. Kokarin da Super Eagles ke yi a Afcon a Morocco, Super Eagles

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Najeriya ta ja ragamar rukuni na uku da lashe dukkan wasa uku da maki tara.

    Ta fara da nasara a kan Tanzaniya 2-1 da cin Tunisia 3-2 da doke Uganda 3-1, sannan ta yi waje da Mozambique 4-0 a wasan zagaye na biyu.

    Kenan Aljeriya ta kawo matakin kwata fainal da cin ƙwallo takwas, kuma ɗaya ya shiga ragarta, Super Eagles kuwa ta ci 12 sannan aka zura mata huɗu a raga.

    Najeriya tana da Afcon uku da ta lashe a 1980 da 1994 da kuma 2013.

  16. Fitattun ƴan wasan Aljeriya a Afcon a Morocco, Afcon Morocco 2025/26

    Afcon

    Asalin hoton, ge

    Ƙyaftin ɗin tawagar Aljeriya, Riyad Mahrez yana taka rawar gani a Afcon a Morocco, duk da cewar shekaru sun ja, amma yana da gogewa da kwarewa, wanda yake da ƙwallo uku a raga kawo yanzu.

    Haka kuma Ibrahim Maza ya ci ƙwallo biyu da Anis Moussa shima mai biyu a raga a Morocco, dukkansu masu zafi ne da zarar sun samu dama ba wasa.

    Yana da mahimmaci Super Eagles ta sa ido a kan Mohamed Amoura, wanda shi ne kan gaba a yawan zura ƙwallaye a raga a wasannin neman shiga gasar kofin duniya ta 2026 da za a yi a bana a Amurka da Canada da kuma Mexico.

    Haka kuma mai tsaron ragar Aljeriya, Luca Zidane ɗan gidan Zinedine Zidane ƙwallo ɗaya ne ya shiga ragarsa daga wasa huɗu kawo yanzu a Morocco, kenan yana kokarin ganin tawagarsa ta ɗauki wannan kofin a karo na uku jimilla.

  17. Me kuke son sani kan wasan Aljeriya da Najeriya a Afcon, Afcon Morocco 2025/26

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Najeriya ta fara da ɗaukar Afcon a karon farko a tarihi a matakin mai masaukin baki a 1980 da doke Aljeriya 3-0 a Legas.

    Itama Aljeriya ta fara da lashe Afcon na farko a 1990 kan Najeriya da cin 5-1 a wasan farko daga baya ta ci Super Eagles 1-0 a zagayen karshe a lokacin da Clemens Westerhof ke jan ragamar Najeriya.

    Sai kuma a 2019 da Aljeriya ta yi nasara a kan Najeriya a zagayen daf da karshe, inda Riyad Mahrez ya ci ƙwallon a bugun tazara daga baya Aljeriya ta doke Senegal ta kuma lashe kofin.

    Wasan karshe da suka fuskanci juna shi ne a sada zumunta a cikin Satumbar 2022 a Oran, inda Aljeriya ta yi nasarar cin 2-1.

  18. Za a yi karon batta tsakanin Aljeriya da Najeriya a Afcon, Afcon Morocco 2025/26

    Afcon

    Asalin hoton, Getty Images

    Aljeriya da Najeriya za su buga zagayen ƙwata fainals ranar Asabar a Marrakech a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Morocco.

    Aljeriya mai Afcon biyu da ta ɗauka a 1990 da kuma 2019, ta kai zagaye na biyu a wasannin da Morocco ke gudanarwa da lashe dukkan karawar rukuni na biyar da haɗa maki tara.

    Ta fara wasan farko da cin Sudan 3-0 da doke Burkina Faso 1-0 da yin nasara 3-1 a kan Equatorial Guinea.

    Daga nan ta fitar da Jamhuriyar Congo da cin 1-0 a zagaye na biyu a minti na 119 ta hannun Boulbina daf da za a tashi a karin lokaci.

  19. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.