, Aljeriya 0-2 Najeriya
Haka kuma Najeriya ta kara yin wani canjin, inda Moses Simon ya maye gurbin Frank Onyeka.
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku bayanai kan wasan Aljeriya da Najeriya zagayen kwata fainals a gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 da ake yi a Moroko.
Mohammed Abdu
Haka kuma Najeriya ta kara yin wani canjin, inda Moses Simon ya maye gurbin Frank Onyeka.
Najeriya ta saka Raphael Onyedika ya canji Wilfred Ndidi saboda raunin da ya ji.
An tsayar da wasan sakamakon raunin da Wilfred Ndidi na Najeriya ya ji.
An bai wa Rayan Aït-Nouri na Aljeriya katin gargaɗi

Asalin hoton, Getty Images
Adil Boulbina ya canji Ibrahim Maza.
Anis Hadj Moussa ya canji Riyad Mahrez.
Baghdad Bounedjah ya canji Ramiz Zerrouki.
Ana duba lafiyar ɗan wasan Najeriya, Calvin Bassey.
Akor Adams na Najeriya ne ya buga ƙwallo da hagu ta kuma faɗa raga, kuma ya samu ƙwallon daga wajen Victor Osimhen.
Victor Osimhen na Najeriya ya saka kai daf da raga, amma mai tsaron raga, Luca Zidane ya tare - Bruno Onyemaechi ya buga masa ƙwallon.
Ademola Lookman na Najeriya ya yi laifi.
Aljeriya ta samu bugun kwana ta hannun Rafik Belghali.

Asalin hoton, Getty Images
Victor Osimhen Na Najeriya ne ya ci ƙwallon da kai, kuma Bruno Onyemaechi ya buga masa.
Wilfred Ndidi na Najeriya ya yi laifi
Ibrahim Maza na Aljeriya ya samu bugun tazara.

Asalin hoton, BBC Sport
Bruno Onyemaechi daga Najeriya ya buga ƙwallo da ƙafar hagu daga nesa ta gefen dama, amma mai tsaron raga, Luca Zidane na Aljeriya ya tsare ta a kusa da kusurwar dama.
Bright Osayi-Samuel na Najeriya ya samu bugun tazara daga gefen hagu.
An yi karin minti uku daga nan za a je hutun rabin lokaci.
Ɗan wasan Najeriya, Bright Osayi-Samuel ya samu bugun tazara daga tsakiyar fili.