Za a fara gwajin riga-kafin cutar sanyin goloriya a Birtaniya

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Ingila za ta zama ƙasa ta farko a duniya da za ta fara yin gwajin riga-kafin cutar goloriya, wata cuta mai yaduwa ta hanyar saɗuwa
Ba kowa ne za a yi wa riga-kafin ba. Za a mayar da hankali ne musamman kan maza masu luwaɗi da kuma waɗanda suka taba kamuwa da wata cuta ta jima’i.
Riga-kafin yana da tasiri tsakanin kashi 30 zuwa 40 cikin 100, amma Hukumar Lafiya ta NHS England na fatan hakan zai taimaka wajen rage yawan sabbin kamuwa da cutar, wanda ke ƙaruwa cikin sauri.
A shekarar 2023, an samu fiye da mutum 85,000 da suka kamu da goloriya– adadin mafi yawa tun da aka fara adana bayanai a shekarar 1918.
Goloriya ba lallai ne ta nuna alamomi ba, amma daga cikin su akwai jin zafi yayin fitsari da kumburi da kuma iya haifar da rashin haihuwa.
Ba a sani ba ko mutane da yawa za su amince a yi musu allurar riga-kafin ba.
Asali, wannan rigakafin ba don cutar goloriya kaɗai aka kirkireshi ba harda riga-kafin cutar sankarau da ake yi wa jarirai a halin yanzu saboda kwayoyin cutar sanƙarau da na goloriya suna da alaƙa sosai.





