Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/06/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage da Muhammad Annur

  1. 'Za mu yi martani idan Amurka, Faransa da Birtaniya suka taimaka wa Isra'ila'

    Iran ta yi gargaɗi Amurka, da Birtaniya da kuma Faransa kan cewa kada su kuskura su taimako wa Isra'ila kare kanta daga hare-haren da take kai wa, a cewar kafofin yaɗa labaran Iran.

    Iran ta ce muddin haka ya faru za ta mayar da martani mai zafi.

    Rahotanni sun bayyana cewa Tehran za ta afka wa sansanonin soji da jiragen ruwa da faɗin yankunan uku, in har suka taimaka wa Isra'ila.

  2. An kashe mutum 1,296 a watan Mayu a Najeriya - Rahoto

    Wasu sabbin alƙalumma kan matsalar tsaro a Najeriya sun nuna cewa mutum 1,296 aka kashe a watan Mayu a sassan ƙasar.

    Rahoton kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a shiyyar Afirka ta yamma da yankin Sahel ya ce an samu ƙaruwar yawan waɗanda suka mutu a watan Mayu idan aka kwatanta da Afrilu inda aka kashe mutum 1,092.

    Rahoton ya kuma ce mutum 1,086 aka yi garkuwa da su a sassan Najeriya a watan Mayu inda aka samu ragi idan aka kwatanta da watan Afrilu da aka yi garkuwa da mutum 1,178.

    Rahoton Beacon Security and Intelligence Limited ya nuna cewa an samu ragi na kashi kusan shida cikin dari na matsalolin tsaro a Najeriya cikin watan Mayun da ya gabata, idan aka kwatanta da yadda lamarin ya kasance a watan watan Afrilu da ya gabace shi.

  3. Harin Iran ya hallaka mutum uku a Isra'ila

    Tun da farko mun ruwaito cewa harin ramuwar gayya da Iran ta kai Isra'ila ya hallaka mutum biyu.

    Sai dai yanzu kafofin yaɗa labaran Isra'ila da kuma jami'an gwamnati sun ce alkaluman sun kai mutum uku.

    Shugaban jam'iyyar adawa a Isra'ila ya miƙa sakon ta'aziyya ga waɗanda suka rasu.

    "Daren da ya gabata ya kasance mai wahala ga al'ummar Isra'ila," kamar yadda Yair Lapid ya rubuta, inda ya buƙaci jama'a da su bi umarnin jami'ai.

  4. Yadda harin ramuwa da Iran ta kai wa Isra'ila ya lalata gine-gine

    Mun fara samun hotuna bayan harin ramuwar gayya da Iran ta kai wa Isra'ila a daren jiya Juma'a.

    An ɗauki waɗannan hotuna ne da safiyar yau a birnin Rishon LeZion, da ke kudancin Tel Aviv.

  5. Isra'ila ta kaɗa gangar yaƙi - Ayatollah Ali Khamenei

    Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce Isra'ila ta kaɗa gangar yaki, kuma ƙasarsa za ta ci gaba da mayar da mummunan martani kan hare-haren da ake kai ma ta.

    Ya ce "bai kamata su yi tunanin cewa za su kaddamar da hare-hare kuma shikenan ba, su ne suka fara, su ne suka kunna wutar yaƙi kuma ba za mu bari su tafi haka nan ba.

    A wani taron gaggawa na kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, jakadan Iran ya ce hare-haren da Isra'ila ta kai ya yi sanadin mutuwar mutum 78 - akasarinsu fararen hula - tare da jikkata wasu da dama.

    An kaddamar da hare-haren ne kan cibiyoyin nukiliya da na soji, amma sun shafi fararen hula da dama.

    Isra'ila ta ce ta kai farmakin ne domin hana Iran mallakar makamin nukiliya.

  6. Ana zaman ɗar-ɗar a Isra'ila bayan harin ramuwar gayya da Iran ta kai

    Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin da Iran ke ci gaba da mayar da martani kan hare-haren da ake kai mata.

    An ji ƙarar fashewar abubuwa a biranen Isra'ila da suka haɗa da birnin Kudus da kuma Tel Aviv.

    Wani ɗan jarida kuma mazaunin birnin Tel Aviv, Gideon Levy, ya shaida wa BBC an kakkabo wasu makaman linzami wasu kuma sun faɗi ƙasa.

    Akwai aƙalla guda biyu da suka faɗi kai-tsaye kan gine-gine inda suka ruguza wasu ɓangarorinsu.

    Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce mutane uku ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata tun bayan da Iran ta fara kai hare-haren.

  7. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Asabar.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.

    Ahmad Bawage ne zai jagoraci kawo muku labaran.