Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta taya Gyokeres, Tottenham na zawarcin Mbuemo
Arsenal ta gabatar da tayin farko na fam miliyan 46.8, tare da yiwuwar ƙarin fam miliyan 8.5, ga Sporting kan ɗanwasan gaban Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 27. (Record)
Sabon kocin Tottenham Thomas Frank na shirin ɗauko ɗanwasan gaban Kamaru Bryan Mbeumo mai shekaru 25 da ɗan wasan Jamhuriyar Dimokraɗiyar Congo Yoane Wissa, mai shekara 28, daga tsohuwar ƙungiyarsa Brentford. (Guardian)
Newcastle ta kara ƙaimi a zawarcin da ta ke yi wa ɗan wasan gaban Brighton da Brazil Joao Pedro bayan ta fahimci cewa ɗan wasan mai shekaru 23 zai yi sha'awar komawa ƙungiyar da Eddie Howe ke horaswa. (Telegraph)
Bayer Leverkusen na shirin gabatar da tayin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Manchester City James McAtee, mai shekara 22 (Sky Sports)
Napoli na gogayya da ƙungiyoyin gasar Saudiyya wurin ɗaukar ɗan wasan gaban Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 25, daga Liverpool. (Fabrizio Romano)
Fenerbahce na sha'awar ɗaukar ɗan wasan baya na ƙasar Ingila Kyle Walker, mai shekara 35, daga Manchester City bayan da ya kasa samun tagomashi a zaman aron da ya yi a AC Milan. (Times)
Bayan ta ɗauki Leroy Sane a kyauta, Galatasaray ta gana da wakilan ɗan wasan tsakiyar Manchester City Ilkay Gundogan, mai shekara 34, domin kawo tsohon ɗan wasan na Jamus zuwa Turkiyya. (Fanatik)
Lazio na sha'awar sayen Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 29, daga AC Milan - inda ta ke buƙatar sake haɗa ɗan wasan da tsohon kocinsa na Chelsea Maurizio Sarri. (Daily Mail)
Aston Villa ta miƙa tayin yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan gefe ɗan ƙasar Sifaniya Jesus Rodriguez mai shekara 19 daga Real Betis. (The Athletic)
Everton na zawarcin tsohon ɗan wasan tsakiya na Manchester United Fred, mai shekara 32, wanda a halin yanzu yake taka leda a Fenerbahce. (Sozcu)
Rangers na shirin sallamar Cyriel Dessers mai shekaru 30 ya koma AEK Athens, bayan ɗan wasan na Najeriya ya amince da yarjejeniyar albashin fam 30,000 a duk mako da ƙungiyar ta ƙasar Girka. (Daily Record)
Roma ta fara tattaunawa da Brighton kan ɗan wasan tsakiya na Denmark Matt O'Riley, mai shekara 24. (Gazzetta)
Wolves ta bayyana sha'awar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Celta Vigo ɗan ƙasar Sifaniya Fer Lopez, mai shekara 21. (Sky Sports)