Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saro-Wiwa: Mutumin da Tinubu ya karrama bayan shekara 30 da rataye shi
- Marubuci, Wedaeli Chibelushi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wa Ken Saro-Wiwa afuwa, shekara 30 bayan rataye shi, lamarin da ya sha tofin Allah tsine daga sassan duniya.
Tare da sauran mutane takwas masu hankoro, kotu ta samu Mista Saro-Wiwa da laifin kisan kai inda ta yanke masa hukuncin kisa, sannan aka zartar da hukuncin ta hanyar rataye shi a shekarar 1995 karkashin gwamnatin mulkin soja ta wancan lokacin.
Sai dai mutane da dama sun yi zargin cewa an masu wannan hukuncin sanadiyyar zanga-zangar da suka jagoranta ta adawa da ayyukan manyan kamfanonin hakar man fetur a yankinsu na Ogoniland, musamman kamfanin Shell. Shell ya musanta hannu a kisan mutanen.
Duk da cewa an yi maraba da afuwar da Tinubu ya yi wa mutanen, wasu masu hankoro da kuma yan’uwan wadanda aka kashe sun ce hakan bai wadatar ba.
Baya ga yi masu afuwa, shugaban na Najeriya Bola Tinubu ya kuma karrama Saro-Wiwa da sauran masu hankoron tara - wadanda ake wa lakabi da ‘Ogoni nine’ - da lambar girmamawa ta kasa.
Mutanen - Mista Saro-Wiwa, Barinem Kiobel, John Kpuinen, Baribor Bera, Felix Nuate, Paul Levula, Saturday Dobee, Nordu Eawo da kuma Daniel Gbokoo - na daga cikin jerin mutanen da shugaban kasar ya karrama a wani bangare na bikin ranar dimokuradiyyar kasar.
Tinubu ya ce karramawar ta kasance yabo ne ga “jaruman” da suka bayar da “muhimmiyar gudumawa” ga dimokuradiyyar kasar.
Lokacin da suka mayar da martani kan afuwar da aka yi wa mutanen tara, kungiyoyin masu hankoro sun ce suna son gwamnatin ta yi kokarin da ya zarce haka.
Kungiyar raya al’ummar Ogoni, wato Movement for the Survival of the Ogoni People (Mosop), wadda marigayi Saro-Wiwa ya jagoranta, ta kira afuwar a matsayin “aikin jarumta”.
Sai dai kungiyar ta ce afuwa na nufin cewa mutum ya yi laifi, amma a zahiri “ba su yi wani laifi ba”.
Matar marigayi Barinem Kiobel ta gode wa Tinubu kan lambar karramawar da ya ba su, sai dai ta bukaci shugaban kasar ya “ayyana mijinta da sauran mutanen a matsayin wadanda ba su da laifi” tun da “babu batun a yi wa wanda bai aikata laifi ba afuwa.”
Ta shaida wa BBC cewa abin da take so shi ne a sake yin shari’ar.
A wani bangaren kuma kungiyar Amnesty International ta ce ”afuwa bai zamanto adalci ga mutanen Ogoni tara da aka kashe ba”.
Ya kamata a dauki wasu karin matakai domin ganin kamfanonin hakar man fetur sun yi adalci game da bata muhalli da suke yi yanzu haka a Najeriya, in ji kungiyar.
Mista Saro-Wiwa na daga cikin mutane na gaba-gaba da suka jagoranci al’ummar Ogoni wurin yin zanga-zangar lumana don nuna adawa da ayyukan Shell da sauran kamfanonin hakar man fetur.
Kungiyar Mosop ta zargi kamfanonin man fetur din da laifin gurbata muhallin da al’umma suka dogara da shi wajen neman na rayuwa.
Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani ta hanyar amfani da karfi kan masu zanga-zangar.
Daga baya kotun soji da ta yi zamanta a cikin sirri ta kama mutanen tara da laifin kisan wasu sarakunan yankin Ogoni hudu.
Kasashen duniya da dama sun yi tir da kisan mutanen. An bayyana lamarin a matsayin kisan gilla kuma batun ya zamo tamkar wani tambarin gwagwarmayar yaki da masu bata muhalli da kuma danniya.
Daga baya an dakatar da Najeriya daga kungiyar kasashe rainon Ingila ta Commonwealth.
Tun daga wancan lokacin kamfanin Shell ya fuskanci shari’o’i da dama kan kwararar mai da lalata muhalli a yankin Neja-Delta da kuma fadin kudancin Najeriya, wanda ya hada da yankin Ogoniland.
A shekarar 2021 wata kotu a Netherlands ta umarci kamfanin Shell ya biya manoma diyyar kwararan danyen man fetur da ya lalata filayen noma da kuma wuraren kamun kifi a Neja-Delta. Kamfanin ya amince ya biya diyyar kudi sama da dala miliyan 100.
A farkon wannan shekarar lauyoyi da ke wakiltar wasu al’ummu biyu da ke Ogoniland suka bukaci kotu a birnin London ta tilasta wa kamfanin Shell daukan alhakin man da ya gurbata muhalli a yankin tsakanin shekarun 1989 zuwa 2020.
Shell ya musanta aikata duk wani laifi tare da cewa masu zagon kasa ga ayyukan kamfanin ne suka haifar da malalar man, da masu satar danyen mai da kuma masu aikin tace danyen man fetur ba bisa ka’ida ba, lamarin da ya ce ba laifinsa ba ne.
Ana sa ran yin cikakkiyar shari’ar a shekarar 2026.
Karin bayani daga Chris Ewokor