Rufewa
Masu bibiyarmu nan za mu rufe shafin namu a yau.
Kuna iya dubawa ƙasa domin karanta rahotonnin da muka kawo muku a wunin na yau.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/09/2025
Daga Aisha Babangida da Habiba Adamu
Masu bibiyarmu nan za mu rufe shafin namu a yau.
Kuna iya dubawa ƙasa domin karanta rahotonnin da muka kawo muku a wunin na yau.
Mu kwana lafiya.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai koma ƙasar a ranar Talata bayan kammala hutunsa a ƙasashen Birtaniya da Faransa.
Cikin wata sanarwa da kakakinsa, Bayo Onanuga ya fitar ya ce Tinubu zai koma domin ci gaba da ayyukansa daga ranar 16 gwatan Satumba.
A makon da ya gabata ne Tinubu ya halarci liyafar cin abincin dare tare da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, a fadar Élysée da ke birnin Paris.
Sanarwar ta ce shugabannin biyu sun tattauna batutuwan ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Faransa domin ci gaban ƙasashen biyu.
A ranar 4 ga watan Satumba ne Tinubu ya fara hutun na kwanakin aiki 10, a wani ɓangare na hutunsa na shekara da doka ta tanadar masa.
Wasu ƴanbindga ɗauke da makamai sun auka wa garin Dogon Daji da ke yankin ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, tare da yi wa hakimin garin yankan rago.
Shugaban ƙaramar hukumar Tsafe Hon. Garba Shehu Tsafe ya tabbatar wa BBC cewa lamarin ya faru ne a yau Litinin da maraice.
''Yanzu-yanzu muka samun rahoton cewa ƴanbindiga sun shiga garin Dogon Daji na Nasarawar Keta, sun kuma yanka hakimin garin'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa a wunin yau ƴanbindigar sun tare wasu hanyoyi a yankin da ke kai wa zuwa Gusau.
Shugaban ƙaramar hukumar ya alaƙanta ƙaruwar hare-haren yankin da sluhun da ake yi a jihar Katsina mai makwabtaka.
Dama dai masana tsaro sun jima suna gargaɗin cewa yin sulhu da ƴanbindigar ba mafita ba ce, saboda za su iya barin wurin da aka yi sulhu da su domin kai hari wasu yankunan, sannan su dawo wurin da aka yi sulhun domin samun mafaka.
Majalisar dinkin duniya ta ce nasarar da ake samu a kokarin samar da dai daito tsakanin jinsu na tafiyar hawainiya, inda a yanzu aƙalla kashi 10 na matan da ke faɗin duniya ke rayuwa cikin tsananin tlauci.
Rahoton da majalisar ke fitarwa duk shekara ya yi hasashen cewa fiye da mata miliyan 350 za su ci gaba da kasancewa cikin talauci nan da shekara biyar masu zuwa.
Rahoton ya ce duk da dai an samu raguwar mutuwar mata masu juna biyu da kusan kashi 40 a cikin wannan ƙarnin, har yanzu dai mata sun fi fama da rashin samun kulawar lafiya fiye da maza.
Sabbin alƙaluman da hukumar ƙididdigar Najeriya ta fitar sun nuna cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi.
NBS ta nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin.
Rahoton na hukumar NBS na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya bayar da umarnin karya farashin kayan abinci ƙasar.
A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.
A baya dai dai an yi ta kiraye-kirayen gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan rage hauhawarar farashi domin magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.
Ƙasashen yankin Gulf sun yi kira ga Amurka ta yi amfani da tasirin da ta ke da shi kan Isra'ila domin tabbatar da cewa ba a sake maimaita irin harin da aka kai kan shugabannin Hamas a Qatar a makon da ya gabata ba.
Yayin wani taron gaggawa a birnin Doha, shugaban Majalisar Hadin Kan Ƙasashen, Jasem Mohammed Al Budaiwi ya ce wajibi ne Amurka ta dakatar da abin da isra'ila ke yi.
Tun da farko Sarkin Qatar ya zargi Isra'ila da ƙoƙarin mayar da hannun agogo baya kan ƙoƙarin cimma zaman lafiya, tare da ƙoƙarin mayar da ƙasashen Larabawa ƙarƙashin ikon ta.
Ya kuma yi gargaɗin cewa burin Isra'ila shi ne tabbatar da cewa yankin Gaza, ya zama yankin da ba za a iya ci gaba da rayuwa cikin sa ba.
Wani sabon rahoton bankin duniya da asusun tallafa wa ƙananan yara na Unicef ya nuna cewa a yankin Afirka, kudu da hamadar sahar ƙangin talauci tsakanin ƙananan na ci gaba da ƙaruwa.
Rahoton ya ce fiye da rabin ƙananan yaran Afirka na rayuwa cikin ƙangin talauci, inda ya ce yaro guda cikin kowane biyar na rayuwa cikin ƙangin talauci a duniya.
To sai dai rahoton - wanda aka fitar a cikin wannan wata na Satumba - ya nuna cewa adadin yaran da ke rayuwa cikin ƙangin talauci ya ragu daga miliyan 507 zuwa 412 tsakanin 2014 zuwa 2024, yayin da Indiya ke kan gaba a samun ci gaban.
Rahoton ya ce ƙasashen Kudancin Asiya sun samu nasarar rage yawan yaran da ke rayuwa cikin ƙangin talaucin da kusan fiye da rabi.
''Ƙasashen Afirka, kudu da hadamar Sahara ne ya ƙunshi kusan kashi 23 na ƙananan yara a duniya, kuma yankin ne ya ƙunshi kashi uku cikin huɗu - fiye da miliyan 312 - na yawan duka yaran da ke fama da ƙangin talauci a duniya,'' kamar yadda rahoton ya nuna.
Rahoton ya nuna cewa tun 2014 kashi 52 cikin 100 na yaran yankin na rayuwa cikin ƙangin talauci.
Sabon rahoton ya ƙayyade cewa duk gidan da ke rayuwa a ƙasa da dala uku, yaran gidan na rayuwa cikin ƙangin talauci.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ba zai kawar da yiwuwar sake kai hare-hare kan shugabannin Hamas ba a duk inda su ke, duk da irin sukar da ya ke sha bayan ƙaddamar da wani hari a Qatar a makon da ya gabata.
Netanyahu ya faɗi hakan ne bayan wata ganawar da ya yi da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, wanda duk da a baya ya nuna damuwarsa kan harin da Isra'ila ta kai kan wata kasa ƙawar Amurka.
Rubio dai ya ƙi cewa uffan kan harin Qatar a yayin da ya ke tare da Netanyahu.
Duk da dai rahotanni sun bayyana cewa Donald Trump ya gargaɗi Netanyahu kan harin ta waya, Netanyahu ya sake nananta cewa Isra'ila na da damar bibiyar abokan adawarta a duk inda su ke, musamman Hamas.
Gwamnatin Koriya ta Kudu ta ce duk wani kamfani da mutane aƙalla uku su ka mutu sakamakon hatsarin wurin aiki cikin shekara ɗaya, za a ci shi tarar aƙalla kashi biyar na ribarsa.
Ma'aikatar ƙwadago ta ce ƙarƙashin sabuwar ƙudurin dokar kariyar, za a kuma ƙwace lasisin kamfanin da aka yawaita samun irin waɗannan haɗurrukan da ke kai wa ga mutuwa.
Gwamnatin ƙasar na ɓullo da sabbin matakan ne domin ganin ta rage adadin mutanen da ke mutuwa a wurin yin aiki.
Alkaluma sun nuna cewa 589 ne suka mutu a hadurran da su ka shafi wurin aiki a bara.
Gwamnatin ƙasar za ta ƙara ma'aikatan sa ido kan tsaron lafiya a kamfanoni su aƙalla dubu uku nan da shekarar 2028.
Wata ƙungiyar Cigaban Kanam (KADA) ta fitar da sanarwar alhini da fushi kan kisan gillar da aka yi wa shugaban unguwar Shuwaka, Malam Hudu Hassan Barau, wanda aka fi sani da Sarkin Shuwaka daga yankin Kyaram, al’ummar Garga a Karamar Hukumar Kanam ta Jihar Filato.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a yau Litinin
Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi garkuwa da shi kusan kwanaki shida da suka wuce, inda daga bisani aka kashe shi, kuma aka gano gawarsa a Dajin Wanka a safiyar Litinin 15 ga Satumba, 2025.
A cikin sanarwar, ƙungiyar ta ce wannan ɗanyen aiki ya sake tunasar da matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar yankin.
Ƙungiyar ta zargi gwamnati a matakai daban-daban da gazawa wajen ɗaukar matakan da suka dace don shawo kan hare-haren ‘yan bindiga da suka jefa al’ummar Garga da kewaye cikin tsoro da fargaba.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, da ya ayyana dokar ta-ɓaci a yankin Garga tare da tura jami’an tsaro da za su iya tunkarar matsalar.
"Haka kuma muna roƙon Sanata mai wakiltar Filato ta Tsakiya, Sanata Diket Plang, da ya yi amfani da kujerarsa wajen kawo ɗauki daga gwamnatin tarayya tare da kai gaggawar tallafi ga ɗaruruwan mutanen da abin ya shafa." in ji ƙungiyar
Sanarwar ta kuma caccaki ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Pankshin da Kanke da Kanam, Yusuf Adamu Gagdi, bisa abin da ta kira shiru da rashin ɗaukar mataki kan kashe-kashe a Kanam.
"Muna kira ga ɗan majalisar jiha daga mazabar Kantana, Hon. Samila Bala Nomada da ya haɗa kai da gwamnati wajen ganin an ba da kuɗade da tallafi domin tsaron mazaɓarsa." in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta ce ba za ta sake jurewa da shiru da halin ko-in-kula na shugabanni ba, inda ta buƙaci a kawo adalci da tsaro ga al’ummar Garga da Kanam baki ɗaya.
Aƙalla mutum 40 ne ake zargin ƴanbindiga suka sace daga wani masallaci da ke ƙauyen Gidan Turbe, ƙaramar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, da safiyar Litinin lokacin sallar asuba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Majiyoyi sun ce an yi awon gaba da masallatan ne zuwa dazukan Gohori da ke yankin Tsafe.
A wani ɓangare kuma, rundunar Operation Hadarin Daji ta ce dakarunta sun gudanar da samame a jihohin arewa maso yamma, inda suka tarwatsa harin ƴan bindiga a Katsina, da kuma daƙile wani harin da aka kai wa jami’an NSCDC a kusa da dajin Danmusa.
Firaministan Sifaniya ya buƙaci a haramta wa isra'ila shiga dukkanin gasar wasanni na duniya har sai ta daina abin da ya kira muguwar aika aikar da ta ke tafkawa.
Pedro Sanchez ya alaƙanta ta'asar da isra'ila ke yi a Gaza da wanda Rasha ke yi a Ukraine, inda ya ce ba abu bane da ya dace ba a bar ƙasashen biyu su riƙa shiga gasar wasanni.
Buƙatar haramta wa isra'ila shiga gasar wasanni, shi ne mataki na baya-bayan nan da gwamnatin Sifaniya ta bijiro da shi domin jan hankali kan abin da ta kira kisan ƙare dangin da ake yi a Gaza.
Tuni dai aka haramtawa Rasha shiga gasar wasannin duniya da dama.
Tun da farko ministan al'adu na Spaniya ya ce ƙasar sa za ta ƙauracewa gasar waƙa ta Eurovision ta 2026 idan har za a amince wa Isra'ila shiga gasar.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, ta ce ta kama wani ɗan kasar Indiya da wasu mutum uku bisa zarginsu da hannu wajen shigar da ƙwayoyin Tramadol na fiye da naira bilyan uku zuwa cikin kasar.
Hukumar ta NDLEA ta bayyana cewa wannan kamen kwaya shine mafi girma a cikin wannan shekarar da hukumar ta yi, lamarin da ke nuna ƙaruwar safarar muggan ƙwayoyi da ta’ammali da su a Najeriya.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta NDLEA ta fitar ta ce jami’anta sun yi nasarar kama mutunan ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, sakamakon bin kwakkwafi da bayanan sirri da jami’ansu suka samu.
Hukumar ta ce jami'anta sun gano ƙwayoyin tramol din wadanda aka shigo da su a matsayin magani na multivitamins a cikin wasu walaye, ana ƙoƙari fita da su cikin wasu manyan motoci daga filin girjin.
Rahotanni sun nuna cewa likitoci kan bayar da ƙwayar Tramadol ne don rage radadin ciwo, amma a yanzu tana neman zama wata annoba a tsakanin matasa inda ta ke haddasa mummunan maye.
Bayanai na cewa yawan masu amfani da wannan magani a kasashen Afirka da dama na ƙaruwa duk da illar da take yi lamarin da ke tayar da hankali.
Hukumomin jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo sun fara yi wa ma’aikatan lafiya da ke yaƙi da cutar Ebola da kuma waɗanda suka yi mu’amala da masu cutar allurar rigakafi a Bulape da ke arewa maso tsakiyar jihar Kasai, inda aka ayyana ɓarkewar cutar a ranar 4 ga Satumba.
Wannan ya biyo bayan an kai adadin allurai 360 a ranar 13 ga Satumba zuwa yankin, kamar yadda gidan rediyo mai zaman kansa, Radio Top Congo, ya ruwaito.
An tabbatar da aƙalla mutum 36 ne suka kamu da cutar inda mutum 16 daga ciki sun mutu, da kuma fiye da 50 da ake zargin sun kamu da cutar a Bulape.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an amince da ƙarin alluran rigakafi 45,000 da za a kai wa Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.
Ɓarkewar cutar Ebola na baya-bayan nan shi ne na 16 a DR Kongo tun bayan gano cutar a shekarar 1976.
Cutar ta kashe sama da mutum 2,000 a ƙasar tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.
Ana sa ran tura sabon rukunin sojojin tsaron Rwanda (RDF) zuwa jihar Cabo Delgado a arewacin Mozambique domin maye gurbin waɗanda suka shafe shekara guda suna hidima a ƙasar ta kudancin Afirka, kamar yadda gidan jaridar New Times mai zaman kansa ya ruwaito.
Shugaban ma’aikatar sojin Rwanda, Janar Vincent Nyakarundi, da mataimakin babban jami’in ‘yan sanda mai kula da ayyuka, Vincent Sano, sun yi wa sabon rukunin sojojin bayanin aiki a ranar 13 ga Satumba a makarantar Soja ta Rwanda dake Gako.
Rahoton bai bayyana adadin sojojin da Janar Vincent zai jagoranta ba, haka kuma bai faɗi ranar da za a sauya rundunar ba.
Sauya rundunar ta zo ne bayan Mozambique da Rwanda sun rattaɓa hannu kan sabon Yarjejeniyar matsayin sojoji domin ci gaba da hadin gwiwar soja wajen yaƙar ‘yan ta’adda a Cabo Delgado.
Rwanda ta fara tura sojoji 1,000 na RDF da ‘yan sanda zuwa Mozambique a watan Yulin 2021 domin yaƙar ‘yan bindiga waɗanda suka tilasta rufe wani babban aikin iskar gas na kamfanin Faransa, TotalEnergies.
Ɗan takarar jam'iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Obi ya kuma ziyarci wanda aka naɗa a matsayin Olubadan, Rashidi Ladoja, a Jihar Oyo.
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Obi ya ce burinsa na ziyartar Ladoja shine don girmama shi saboda muhimmancin Ibadan a siyasa da zamantakewa da tattalin arzikin Najeriya.
Obi ya bayyana cewa Ladoja zai kawo ƙwarewarsa a matsayin tsohon sanata da gwamna da attajiri wajen jagorantar Ibadan zuwa matsayi mai daraja.
Obi ya ƙara da cewa, “Ziyarar duka mutanen biyu nan na da nasaba da ci gaban Najeriya da shugabanci na gaskiya da shugabanci da ke da niyyar sauya al’umma"
Amurka da China sun shiga rana ta biyu ta tattaunawar kasuwanci a Spain yayin da wa’adin da ke tilasta wa kamfanin TikTok neman mai siya ko kuma a haramta ta a Amurka ke gabatowa.
Ministan Kuɗin Amurka Scott Bessent da Mataimakin Firaministan China He Lifeng ne ke jagorantar tattaunawar inda ake sa ran tattaunawar zai kawo ƙarshen yaƙin kasuwanci tsakanin ƙasasehn biyu masu manyan tattalin arzikin duniya.
Ana sa ran wa’adin dakatar da TikTok a Amurka wanda zai kare ranar Laraba, zai sake samun ƙarin lokaci,
Trump wanda a baya ya nemi a hana TikTok, yanzu ya sauya matsayinsa kan batun bayan shahararsa ta ƙaru a TikTok a lokacin zaɓen 2024, inda ma fadar White House ta kaddamar da shafin TikTok na hukuma a watan Agusta.
Haka kuma ana sa ran tattaunawar za ta tanadi haɗuwa tsakanin Trump da Xi Jinping a watan Oktoba a Koriya ta Kudu.
Yayin da matsalar daba da ƙwacen waya ke neman zama ruwan dare a jihar Kano, ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun jama'a suna ci gaba da fito da dabaru da hanyoyin da za a magance matsalar.
Cibiyar bincike akan tattalin arziki da zamantakewa da nazari kan al'umma ta Jami'ar Bayero Kano da haɗin gwiwar gidauniyar A A Zaura sun gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki da masana ilimi a jihar Kano.
A taron, za a tattauna dabarun magance matsalolin daba da shaye-shaye.
Masana sun gabatar da kasidu daban-daban ciki har da wadda Dr. Auwalu Halilu ya gabatar mai taken samar da ilimin kasuwanci da cibiyoyin koyon sana'o'in dogaro da Kai.
Gangamin yaƙi da matsalar daba da shaye-shaye sun bayyana cewa sun gudanar da bincike mai zurfi inda aka taskace hanyoyin magance matsalar da kuma bayyana matasa a matakin unguwanni inda ake fatan mika kunshin rahoton ga gwamnati da masu ruwa da tsaki don daukar matakan da suka dace.
Gwamnan Jihar Utah, Spencer Cox, ya bayyana cewa matashin da ake zargi da kashe Charlie Kirk, Tyler Robinson “ba ya bai wa hukumomi haɗin kai har yanzu bai furta cewa shi ne ya harbe Kirk ba."
An kama matashin da ake zargin ne kimanin sa’o’i 33 bayan harbin Kirk wanda yake ɗaya daga cikin fitattun magoya bayan Trump a birnin Orem a ranar Laraba.
Gwamnan ya ce ana ci gaba da bincike kan dalilin harbin.
An kama Robinson ne a daren Alhamis bayan ya mika kansa ga ‘yan sanda.
Takardar sheda daga jihar Utah ta tabbatar da cewa ana zargin shi da laifuka uku da suka haɗa da kisan kai, harbi da bindiga da ƙoƙarin daƙile tabbatar da adalci
Gwamna Umar Bago na Jihar Neja ya bayyana cewa wajibi ne a kan masu wa’azi su riƙa miƙa takardun huɗubarsu domin samun amincewar gwamnati kafin su yi wa’azi a jihar.
Gwanan ya faɗi hakan ne a cikin wani shiri na gidan talabijin TVC inda ya fayyace wasu abubuwa na dokar da ke kokarin tsara yadda ake wa’azi a jihar.
Gwamnan ya ce, “Ban haramta wa’azi ba, Duk wanda zai yi huɗuba a ranar Juma’a, ya kamata ya kawo takardar da zai yi amfani da shi domin a duba abun da ke ciki, ko a Saudiya ma ana yin hakan."
"Ba za mu ce saboda an ba ka dama ka zama malami, za ka fita ka yi wa’azi wanda zai saɓawa mutane ko gwamnati ba.” gwamnan ya ƙara da cewa.
"Saboda haka ne muke son mu ga abin da takardar wa’azin ya ƙunsa, abin da za a faɗi kuma muna aiki tare da hukumomin tsaro na DSS da ƴan sanda da NSCDC da sojoji.” in ji gwamnan.
Wannan mataki da aka fara bayyanata ga bainar jama'a a farkon watan nan ya janyo ce-ce-ku-ce.