Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/09/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/09/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Habiba Adamu

  1. Ana neman kawo mana rikici saboda batun shugabancin jam'iyya — ADC

    Jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya ta yi zargin cewa wasu na neman kara jefa ta cikin rikici bayan amincewa da shugabancinta da hukumar Zaben kasar ta INEC ta yi.

    Jam'iyyar ta musanta bullar wasu rahotannin da ke cewa hukumar INEC ta amince da shugabancin jam'iyyar na jihohi in da ta ce ana yunƙurin haifar da hautsini a tsakani ƴa'ƴanta.

    Jam'iyyar ta ce ita ke da hakkin mika sunayen shugabanninta na jihohi ga hukumar INEC, kuma yanzu haka bata kammala aikin tattara sunayen shugabancin jihohin ba ballantana ace an amince da su.

  2. Shugabannin Larabawa za su gudanar da taron gaggawa a Qatar kan harin Isra’ila

    A yau Litinin ne shugabannin kasashen Larabawa ke gudanar da wani taron gaggawa a Qatar a matsayin martani ga harin da Isra'ila ta kai kan Hamas a Doha a makon daya gabata.

    Daga cikin abubuwan da za a tattauna a taron wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato akwai harin da Isra'ila ta kai Qatar da abubuwan da ta ke aikatawa da suka shafi kisan kiyashi da azabtar da mutane da yunwa, wanda dukkansu barazana ce ga zaman lafiya da kuma ci gaban ƙasashen Larabawa.

    Za a yi a taron ne a Doha domin nuna wa Qatar goyon baya inda Qatar din ta yi alawadai da harin da aka kai mata.

    Shugaban Amurka Trump ya ce Qatar babbar abokiyar Amurka ce a don haka ya kamata Isra'ila ta rinƙa yin taka tsantsan kafin ta kai duk wani hari.

  3. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Litinin.

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.