Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana neman kawo mana rikici saboda batun shugabancin jam'iyya — ADC
Jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya ta yi zargin cewa wasu na neman kara jefa ta cikin rikici bayan amincewa da shugabancinta da hukumar Zaben kasar ta INEC ta yi.
Jam'iyyar ta musanta bullar wasu rahotannin da ke cewa hukumar INEC ta amince da shugabancin jam'iyyar na jihohi in da ta ce ana yunƙurin haifar da hautsini a tsakani ƴa'ƴanta.
Jam'iyyar ta ce ita ke da hakkin mika sunayen shugabanninta na jihohi ga hukumar INEC, kuma yanzu haka bata kammala aikin tattara sunayen shugabancin jihohin ba ballantana ace an amince da su.
Faisar Kabir, daya ne daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ta ADC, ya shaida wa BBC cewa, wadannan sunaye bad aga hukumar zaben suke ba.
Ya ce," Wasu mutane ne suka kirkiri wannan sunaye domin su kawo mana hargitsi a cikin jam'iyya, amma wannan sunaye ba daga hukumar INEC yake ba."
Faisal Kabir, ya ce," Tun ranar da muka karbi jam'iyya da kwana biyar bayan an yi taron kwamitin amintattun a jam'iyya mun tara shugabannin jam'iyyar su 37 da muka tarar inda aka tabbatar musu da cewa za su ci gaba da rike kujerunsu har zuwa lokacin da jam'iyya zata yanke hukunci akan matakin da ya kamata ta dauka."
Ya ce," A don haka shugabannin na baya na nan akan kujerunsu babu wanda ya rushesu."
Mai Magana da yawun jam'iyyar ta ADC, ya ce" A yanzu abin da muke son yi shi ne kokarin hada kan 'ya'yan jam'iyyar musamman wadanda ke son a hada kan ba wadanda ke son raba kan jam'iyya ba."
Ya ce," Ya kamata mutane su sani a dokance jam'iyya ce ke hada sunayen shugabanninta sannan ta aikewa da hukumar zabe, kuma mu har yanzu ba mu dauki wani suna mun kai wa INEC ba."
Hukumar zaben INEC dai ta tabbatar wa da BBC cewa ta amince da shugabancin jam'iyyar ta ADC karkashin tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya David Mark, amma bata tabbatar da shugabancin jihohi ba.
Tun bayan sanar da sabuwar haɗakar ADC ta ƴan hamayya a Najeriya, jam'iyyar ke fama da tarin matsaloli na cikin gida da kuma adawa daga sauran jam'iyyu.
Haɗakar jam'iyyar ta ADC cike take da hamshaƙan ƴansiyasa masu burin tsayawa takarar shugabancin Najeriya.
Zaɓen 2027 dai zai kasance ɗaya daga cikin mafiya ɗaukar hankali a siyasar Najeriya, kasancewar yadda haɗakar ADC ta fito, ƙunshe da jiga-jigan siyasar ƙasar.
Masana na ganin cewa dole ne jam'iyyar ta yi duk mai yiwuwa domin magance waɗannan matsaloli da take fuskanta, idan har tana son ɗorewa.