Saka zai yi jinyar mako huɗu

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan Arsenal, Bukayo Saka ya ji raunin da ake sa ran zai yi jinyar mako huɗu, inda ake tunanin ba zai samu buga wasan Arsenal da Liverpool na ranar Lahadi ba, da kuma wasannin neman gurbin shiga kofin duniya da Ingila za ta fafata da Andorra da Serbia a watan gobe.
An cire ɗanwasan mai shekara 23 ne ana tsaka da wasan Arsenal da Leed United a ranar Asabar da ta gabata.
Kyaftin ɗin Arsenal Martin Odegaard shi ma ya ji rauni a wasan na Leeds, ina aka cire shi kafin a kammala wasan wanda ƙungiyar ta lallasa Leeds da ci biyar da nema.
Har yanzu ba a fayyace yanayin raunin Odegard ba, amma ana sa ran zai buga wasan ƙungiyar da Liverpool.
Da farko magoya bayan Arsenal sun shiga fargaba ne ganin ɗanwasan ya yi kusan wata uku yana jinya a kakar bara.
Sai dai ana ganin ƙungiyar na da zaratan ƴanƙwallo, kasancewar a kakar bana ta ɗauko manyan ƴanwasa irin su Viktor Gyokeres da Noni Madueke da Eberechi Eze.







