Ƙyaftin Bowen ya kalubalanci ƴan kallon West Ham, Wolves 3-2 West Ham
Asalin hoton, Reuters
Ƙyaftin Jarrod Bowen ya kalubalanci magoya bayan West Ham United, bayan da Wolverhampton ta fitar ita daga Carabao Cup a Molinuex.
To sai dai ya shiga kafarsa ta sada zumunta, inda ya nemi afuwa kan abinda ya aikata ranar Talata, sakamakon rashin nasara da suka yi.
Swiantek ta kai zagaye na biyu a US Open
Wadda take ta biyu a jerin masu buga kwallon tenis a
duniya, Igwa Swiatek ta fara US Open da kafar dama, bayan da ta kai zagaye na
biyu cikin ruwan sanyi, bayan caskara Emiliana Arango.
Swiantek wadda ta lashe Wimbledon Open a watan jiya da
ake sa ran za ta dauke gasar da ake a Flushing Meadows ta yi nasarar cin 6-1
da kuma 6-2.
Kenan za ta fuskanci Suzan Lamens a fafatawar zagaye na
biyu.
An yi wa Miliams alfarmar shiga US Open ta ƴan wasa bibiyu
Asalin hoton, Getty Images
Venus Williams za ta buga gasar US Open ta ƴan wasa bibiyu bayan da aka yi mata alfarmar shiga wasannin tare da takwararta Leylah Fernandez.
Mai shekara 45 ta koma buga Grand Slam a bana karo na 25 a makon nan.
Koda yake Karolina Muchova ta yi waje da ita ranar Litinin, amma za ta kara a wasannin da ake yi a Flushing Meadows tare da Fernandez.
Za kuma su fuskanci Lyundmyla Kichennok da Ellen Perez a zagayen farko.
Williams ta lashe US Open a gasar ƴan wasa bibiyu a 1999 da kuma 2009 tare da ƴar uwarta, Serena.
Asalin hoton, Getty Images
Porto na gab da cimma yarjejeniya zaman aro da ɗan wasan Arsenal mai shekara 25 daga Poland, Jakub Kiwior. (Sky Sports, external)
Crystal Palace na shirin shiga tattaunawa da ɗan wasan Liverpool Harvey Elliott mai shekara 22, yayin da suke kokarin neman wanda zai maye gurbin, Eberechi Eze mai shekara 27, da ya koma Arsenal. (Football Insider, external)
Bayer Leverkusen da Galatasaray na kalubalantar Crystal Palace a cinikin ɗan wasan Manchester City da Switzerland, Manuel Akanji. (Independent)
Brentford na son ɗauko ɗan wasan Borussia Dortmund mai shekara 22 daga Jamus, Max Beier, yayin da ita kuma ƙungiyar ta Bundesliga ke harin ɗan wasan Portugal, Fabio Silva mai shekara 23 daga Wolves. (Sky Sports, external)
Roma ta tattauna da Chelsea da wakilan Tyrique George kan saye ɗan wasan Ingila mai shekara 19. (Gianluca di Marzio - in Italian, external)
Bottas da Perez za su tuka motar Cadillac a Formula 1 a baɗi
Asalin hoton, Getty Images
Valtteri Bottas da Sergio Perez will za su tuka motar Cadillac a tseren motocin Formula 1 a baɗi.
Rabon da suyi tseren motocin Formula 1 tun 2024.
Bottas, wanda zai cika shekara 36 da haihuwa ranar Alhmis, ya tuka motar Marsandi tare da Lewis Hamilton daga 2017 zuwa 2021.
Shi kuwa Perez mai shekara 35 ya lashe Grand Prix shida, biyar a Red Bull da ɗaya a Racing Point da ake kira Aston Martin.
Palace za ta ɗauki Pino daga Villareal kan fam miliyan 26
Asalin hoton, Getty Images
Crystal Palace ta amince za ta biya fam miliyan 26, domin sayen ɗan wasan Villareal, Yeremy Pino.
Mai shekara 22 da haihuwa yana sa ran komawa Selhurst Park da taka leda, wanda daga nan za a auna koshin lafiyarsa.
Pino yana da ƙunshin yarjejeniyar fam miliyan 69 a ƙungiyar Sifaniya, amma da yake saura kwantiragin kaka biyu ya rage masa, shi ya sa Villareal ta amince da tayin Palace.
Palace ta yi zawarcin Pino, bayan da ɗan wasan tawagar Ingila, Eberechi Eze ya koma Arsenal da taka leda kan fam miliyan 60 ranar Asabar.
Ƴan wasa biyu Palace ta ɗauka a bana da ya haɗa da mai tsaron raga, Walter Benitez daga PSV Eindhoven da mai tsaron baya, Borna Sosa daga Ajax kan fam miliyan uku.
Pino ya fara taka leda a matakin matashi a Las Palmas daga nan ya koma Villareal a 2017.
Wolves ta kusan kallama sayen Krejci daga Girona
Asalin hoton, Getty Images
Wolves ta kusan kammala sayen ɗan wasan Girona mai tsaron baya, Ladislav Krejci kan fam miliyan 26.
Mai shekara 26 ana sa ran zai je Molineux a makon nan, domin a auna koshin lafiyarsa, zai zama na biyar da Vitor Perieira ya ɗauka a bana.
Krejci ɗan ƙwallon tawagar Jamhuriyar Czech, ya koma Girona kan fara kakar da ta wuce, ya kuma yi mata karawa 35 a dukkan fafatawa da ta kare a mataki na 16 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Ya koma Girona daga Sparta Prague, wanda ya yi wa kaka biyar a ƙungiyar da lashe kofi biyu a babbar gasar kasar.
Tuni dai Wolves ta ɗauki ackson Tchatchoua da David Moller Wolfe da Fer Lopez da kuma Jhon Arias.
Wolves ta ƙi sallama tayin fam miliyan 50 da Newcastle ta taya Larsen
Wolverhampton ta ƙi sallama tayin fam miliyan 50 da
Newcastle United ta yi wa Jorgen Strand Larrsen.
Watakila kungiyar da Eddie Howe ke jan ragama ta kara
tayi a karo na biyu, tun a baya BBC ta sanar cewar Wolves ba ta da niyyar
sayar da dan wasan tawagar Norway.
Tuni
Newcastle ta shiga kasuwa, domin maye gurbin Callum Wilson, wanda ya bar St
James Park a watan jiya.
Haka kuma
Newcastle ta yi kokarin sayen gurbin mai cin kwallaye, amma sai
Ekitike ya zabi Liverpool, Benjamin Sesco ya koma Manchester United, sannan
Joao Pedro ya bar Brighton ya koma Chelsea daga cikin wadanda ta yi zawarci.
Everton na son sayen Soucek daga West Ham
Asalin hoton, Getty Images
Everton,tana fatan sayen Tomas SDoucek daga West Ham kamar yadda Times ta sanar.
Soucek ya taka leda a karkashin David Moyes lokacin da ya ja ragamar West Ham United.
Strasbourg ta ƙi sallama tayin da Forest ta yi wa Bakwa
Asalin hoton, Getty Images
Strasbourg ta ƙi sallama tayin fam miliyan 30.2 da Nottingham Forest ta yi wa Dilane Bakwa.
Mai shekara 22 yana sha'awar komawa City Ground, kuma yana fatan za a kammala komai kafin a rufe kasuwar cikikayyar ƴan ƙwallo ranar 1 ga watan Satumba.
Bakwa ya ci ƙwallo 11 da bayar da 20 aka zura a raga a wasa 69 a Strasbourg tun bayan da ya koma ƙungiyar daga Bordeaux a 2023.
Itama wadda ta koma buga Premier League a bana Leeds United da Sunderland, suna son sayen matashin tawagar Faransa ta ƴan kasa da shekara 21.
Forest ta taya ɗan wasan ne a lokacin da ake tantama kan makomae kociya, Nuno Espirito Santo a ƙungiyar.
Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta amince da yarjejeniyar ba da aron ɗan wasanta na Senegal, mai shekara 24, Nicolas Jackson ga Bayern Munich. (Bild - in German)
Ɗan wasan tsakiya a Ingila, Kobbie Mainoo mai shekara 20, na nazarin barin Manchester United nan gaba kaɗan. (Talksport)
Crystal Palace ta gabatar da tayin fam miliyan 15 kan ɗan wasan Manchester City Manuel Akanji, mai shekara 30. (Sun)
Ɗan wasan gaba a Manchester United da Denmark Rasmus Hojlund mai shekara 22, zai samu karin albashi idan ya amince ya koma Napoli. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Matasan da suka ci ƙwallo a Premier mafiya karancin shekaru, Newcastle 2-3 Liverpool
Asalin hoton, BBC Sport
Matashi Rio NGumoha na ya ci wa Liverpool ƙwallo na uku da ta doke Newcastle 3-2 a mako na biyu a Premier League ranar Litinin.
Wayne Rooney yana daga cikin matashin ɗan wasa da ya zura ƙwallo a karawarsa ta farko a Premier League a Everton da ya ci Arsenal.
Crystal Palace ta tuntuɓi City kan a sayar mata da Akanji
Asalin hoton, Getty Images
Crystal Palace ta tuntuɓi Manchester City kan a sayar mata da mai tsaron baya, Manuel Akanji
Har yanzu ba a taya ɗan ƙwallon ba, amma wata majiya ta sanar da BBC cewar Palace tana son jin ko za a iya sayar mata da ɗan wasan tawagar Switzerland.
Watakila City ta sayar da shi kan fam miliyan 15, wanda bai yi mata wasa biyu ba da fara Premier League ta bana.
Haka kuma ƙungiyar Turkiya, Galatasaray tana son yin zawarcin mai tsaron bayan mai shekara 30.
Akanji ya koma Etihad daga Borussia Dortmund a 2022, yana daga cikin ƴan wasan da suka lashe mata kofi uku rigis a 2023 da buga mata karawar karshe a Champions League da ta yi nasara a kan Inter Milan.
A farkon watan nan kociya, Pep Guardiola ya sanar zai mayar da hankali kan ƴan wasan da za su sayar, saboda sun kashe kuɗi da yawa a bana wajen sayen ƴan kwallo shida kan fam miliyan 150.
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Everton da Scotland Nathan Patterson ya ɗau hankalin Sevilla da ke son ɗaukansa aro. (Liverpool Echo)
West Ham ta yi watsi da tayin Everton kan ɗan wasanta na tsakiya mai shekara 30 daga Czech, Tomas Soucek. (Times - subscription required)
Mai buga tsakiya a Brazil Andreas Pereira mai shekara 29, na da damar barin Fulham a wannan kakar. (Teamtalk)
Daraktan Roma zai tattauna da Liverpool kan ɗan wasan Girka, Kostas Tsimikas mai shekara 29, wanda Marseille ke nuna kwaɗayinta. (Football Italia)
Crystal Palace ta shiga farautar ɗan wasan Toulouse da Faransa, Jaydee Canvot mai shekara 19. (Fabrizio Romano)
Ɗan wasan tsakiya a Bournemouth Philip Billing mai shekara 29, zai koma Denmark domin ci gaba da taka leda a Midtjylland kan yarjejeniyar fam miliyan 5. (Times - subscription required)
Arsenal tana son sayen Piero Hincapie daga Leverkusen
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta ci gaba da cefane kan a rufe kasuwar
cinikayyar yan kwallo ranar 1 ga watan gobe, harma tana son sayen dan wasan Bayer
Leverkusen mai tsaron baya, Piero Hincapie.
Arsenal ta daɗe tana neman mai tsaron baya daga gefen
hagu, yanzu tana fatan sayen ɗan kwallon tawagar Ecuador.
Hincapie wanda yake da kunshin yarjejeniyar fam miliyan
52 ga duk mai son sayensa, daidai da sama da naira biliyan 315, yana kumas son barin
kungiyar Jamus a bana, .
Ya buga wasa 166 a dukkan karawa a Leverkusen tun bayan
da ya koma kungiyar a 2021 – yana kuma cikin yan wasan da suka lashe Bundesliga
a 2023/24.
Kawo yanzu Arsenal ta kashe sama da fam miliyan 200 wajen
sayen sabbin yan wasa a bana, kwatankwacin sama da naira biliyan 412 kenan
Gunners tana fatan sayar da Fabio Vieira da Reiss Nelson da
Oleksandr Zinchenko da sauransu kafin kasuwar cinikin yan kwallo ta ci ta watse.
Haka kuma Gunners tana son zawarcin Jakub Kiwior, wanda
Porto ke son saya da sauran manyan kungiyoyin Turai.
Ƙungiya biyar ce ta haɗa maki shida a La Liga a wasa biyu
Ranar Litinin aka kammala wasannin mako na biyu a La liga, inda
Athletic Club ta ci Rayo Vallecano 1-0 da wanda Getafe ta je ta yi nasarar zura
kwallo 2-1 a ragar Sevilla.
Kawo yanzu kungiyoyin da suka haɗa maki shida daga wasa
bibiyu sun hada da Real Madrid da Villareal da Getafe da Athletic Club da kuma
Barcelona mai rike da kofin bara.
Newcastle 2-3 Liverpool, Newcastle 2-3 Liverpool
Asalin hoton, Getty Images
An bai wa ɗan wasan Newcastle, Anthony Gordon jan kati ranar Litinin a wasan da Liverpool ta yi nasara 3-2 a Premier League a St James Park.
Kenan jan kati 17 aka yi a karawa tsakanin Newcastle United a Premier League a tarihi - Wasan da aka yi ruwan jan kati shi ne tsakanin Everton da Liverpool da aka yi 25 sai kuma wasan Manchester United da aka yi 18.
Asalin hoton, Getty Images
Wolves za ta gabatar da sabon kwantiragi kan Jorgen Strand Larsen bayan watsi da tayin fam miliyan 50 daga Newcastle, amma har yanzu akwai kwaɗayin cefanar da shi idan har za a ba ta fam miliyan 75. (Telegraph - subscription required)
Strand Larsen na matukar son zuwa Newcastle amma ba a masa kallon wanda zai maye gurbin Alexander Isak mai shekara 25, da Liverpool ke farauta. (The I - subscription required)
Jami'ai a Newcastle har da ɗaya daga cikin masu ƙungiyar, Jamie Reuben, sun tuntubi Isak a kokarin shawo kansa duk da farautar Liverpool. (Daily Mail)
Kocin Wolves Vitor Pereira na son ɗauko ɗan wasan Girona, Ladislav Krejci mai shekara 26. (Guardian)
Borussia Dortmund na gab da cimma yarjejeniya da ɗan wasan Wolves mai shekara 23, Fabio Silva. (, externalAthletic - subscription required)
Newcastle ta yi wasa na 18 ba tare da Nasara ba da Liverpool
Asalin hoton, Getty Images
Newcastle ta yi wasa na 18 ba tare da nasara ba a kan
Liverpool a Premier League daga ciki aka doke ta 13.
Liverpool ta ci Newcastle 3-2 a St James Park a
karashen wasan mako na biyu a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Litinin.
Newcastle ta karasa karawar da yan kwallo 10 a cikin
fili, bayan da aka bai wa Anthony Gordon jan kati.
A kakar da
ta wuce Newcastle ta lashe Carabao Cup a kan Liverpool a Wembley.
Newcastle ta fara da tashi 0-0 a gidan Aston Villa, ita kuwa Liverpool ta doke Bournemouth 4-2 a Anfield.
, Dortmund ta mallaki Chukuemeka daga Chelsea
Asalin hoton, Getty Images
Borussia Dortmund ta mallaki ɗan wasan tawagar Ingila ta matasa, Carney Chukwuemeka daga Chelsea.
Chukwuemeka, mai shekara 21, ya koma Dortmund kan kuɗin da ake cewar zai kai fam miliyan 24, bayan da ya buga mata wasannin aro a kakar da ta weuce.
Ɗan ƙwallon ya buga wasa 32 a Chelsea tun bayan da ya koma Stamford Bridge daga Aston Villa kan fam miliyan 20 a 2022.
Haka shima Aaron Anselmino ya amince zai buga wasannin aro a Dortumun daga Chelsea, harma ya je Jamus domin a auna koshin lafiyarsa.
Siyar da Chukwuemeka da Chelsea ta yi ya sa ta samu fam miliyan 270, kuɗin sayar da ƴan ƙwallo a bana, yayin da ta kashe fam miliyan 277, wajen sayen sabbin ƴan wasa.