Labarin wasanni daga 23 zuwa 29 ga watan Agustan 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 23 zuwa 29 ga watan Agustan 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Umar Mikail

  1. Crystal Palace ta sayi Yeremy Pino daga Villarreal

    Yeremy Pino

    Asalin hoton, Getty Images

    Crystal Palace ta ɗauki Yeremy Pino daga Villarreal kan kuɗi fan miliyan 26.

    Ɗan ƙasar Sifaniyan mai shekara 23 ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara biyar, kuma zai samu damar buga wasan Premier League da Aston Villa ranar Lahadi.

    "Labari ne mai daɗi cewa Yeremy - ɗanwasa mai hazaƙa da ke da irin wannan tarihi a Turai da ƙasarsa - ya zaɓi ya taka mana leda," a cewar shugaban ƙungiyar ta Palace Steve Parish.

    "Yayin da muke shirin buga gasanni da dama a kakar nan, ɗanwasa ne da magoya bayan Palace za su ji daɗin ƙwarewarsa."

  2. Kocin Najeriya ya fitar da tawagar 'yanwasan neman zuwa gasar Kofin Duniya

    Tawagar Super Eagles ta Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan tawagar Super Eagles ta Najeriya Eric Chelle ya fitar da tawagar 'yanwasa 23 da za su buga wa ƙasar wasannin neman zuwa Kofin Duniya ta 2026.

    A ranar 6 da 9 ga watan Satumba Najeriya za ta buga wasa da Rwanda a gida, da kuma karawa da Afirka ta Kudu a waje.

    Kocin bai kira 'yanwasan gaba ba irinsu Victor Boniface, da Sadiq Umar, da Nathan Tella. Sai kuma ɗanwasan tsakiya Yusuf Alhassan da shi ma ba zai buga wasannin ba.

    Tawagar 'yanwasan ta ƙunshi:

    Masu tsaron raga: Stanley Nwabali (Chippa United, South Africa); Amas Obasogie (Singida Blackstars, Tanzania); Adeleye Adebayo (Volos FC, Greece)

    'Yanwasan baya: William Ekong (Al-Kholood, Saudi Arabia); Calvin Bassey (Fulham FC, England); Olaoluwa Aina (Nottingham Forest, England); Bright Osayi-Samuel (Birmingham City, England); Bruno Onyemaechi (Olympiakos, Greece); Chidozie Awaziem (Nantes FC, France); Felix Agu (Werder Bremen, Germany); Benjamin Fredericks (Dender FC, Belgium)

    'Yanwasan tsakiya: Alex Iwobi (Fulham FC, England); Frank Onyeka (Brentford FC, England); Wilfred Ndidi (Besiktas FC, Turkey); Fisayo Dele-Bashiru (SS Lazio, Italy); Raphael Onyedika (Club Brugge, Belgium); Christantus Uche (Getafe CF, Spain)

    'Yanwasan gaba: Ademola Lookman (Atalanta BC, Italy); Samuel Chukwueze (AC Milan, Italy); Victor Osimhen (Galatasaray FC, Turkey); Simon Moses (Paris FC, France); Cyriel Dessers (Glasgow Rangers, Scotland); Tolu Arokodare (KRC Genk, Belgium)

  3. Bukayo Saka zai yi jinyar makonni, in ji Arteta

    Bukayo Saka

    Asalin hoton, Reuters

    Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce "abin damuwa ne" saboda yadda Bukayo Saka ya ji rauni a bayan gwiwarsa sau biyu cikin wata takwas.

    Ɗanwasan gefen na Ingila ya yi jinyar wata uku da rabi a kakar da ta gabata bayan yi masa tiyata a gwiwarsa ta dama a watan Disamba.

    Yanzu ɗanƙwallon mai shekara 23 ya sake tafiya jinyar "makonni" saboda wani raunin - wannan karon a ƙafarsa ta hagu - a wasan da Arsenal ɗin ta doke Leeds ranar Asabar.

    Arteta ya tabbatar cewa ba za a yi wa Saka tiyata ba a wannan karon "saboda bai kai munin na farko ba".

    "Ya ji wani abu, saboda haka zai yi jinyar wasu makonni," in ji kocin a yau Juma'a.

    "Amma tabbas abin damuwa ne babba, musamman idan muna maganar ɗanwasan da ke taka leda irin tasa, mai kutsawa cikin abokan hamayya da ƙirƙirar fargaba akai-akai."

  4. Man United ta ƙi amincewa da bayar da aron Mainoo

    Kobbie Mainoo

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗanwasan tsakiyar Manchester United Kobbie Mainoo ya nemi ya bar ƙungiyar domin buga wasannin aro a wani kulob ɗin daban.

    Sai dai United ta ƙi amincewa da buƙatar, inda ta faɗa wa ɗanwasan cewa tana buƙatar ya ci gaba da zama domin neman gurbi a tawagar.

    Babu tabbas ko an yi wata tattaunawa fiye da haka game da batun kafin rufe kasuwar saye da musayar 'yanwasa ranar Litinin.

    An ce ƙungyiyo da yawa na son samun sa, ciki har da zakarun gasar Serie A ta Italiya Napoli.

    Da yake magana a yau Juma'a, kocin Man United Ruben Amorim ya ce yana son Mainoo ya zauna ya "fafata" da sauran abokan wasansa.

  5. Sudan da Senegal za su buga wasan neman na uku a gasar CHAN

    Sudan da Senegal

    Asalin hoton, @CAF_Online

    Sudan da Senegal za su nemi gurbi na uku a gasar kofin ƙasashen Afirka ta 'yanwasan cikin gida wato CHAN a yau Juma'a.

    Madagascar ce ta doke Sudan 1-0 a wasan kusa da ƙarshe da suka fafata a ranar Talata, yayin da Morocco ta fitar da Senegal mai riƙe da kofin gasar a bugun finareti bayan tashi 1-1.

    A gobe Asabar ne kuma za a buga wasan ƙarshe tsakanin Madagascar da Morocco da misalin ƙarfe 4:00 a birnin Nairobi na ƙasar Kenya.

    Duk tawagar da ta yi nasarar cin kofin za ta samu kyautar kuɗi dala miliyan 3.5, yayin da ta biyu za ta koma gida da dala miliyan 1.2.

  6. Tottenham na dab da kammala cinikin Xavi Simons

    Xavi Simons

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham na dab da ɗaukar Xavi Simons daga RB Leipzig kan fan miliyan 51.8.

    Ɗanwasan na ƙasar Netherlands yana Ingila yanzu haka, inda majiyoyi ke nuna cewa ya kammala gwajin lafiya kafin zama ɗanwasan ƙungiyar ta Spurs.

    Ƙungiyoyin biyu sun amince da mafi yawan abin da yarjejeniyar ɗanwasan mai shekara 22 za ta ƙunsa, yayin da ake shirin ƙarƙare sauran batutuwan cikin awa 24 masu zuwa.

    Chelsea ta tattauna da Leipzig da zimmar ɗaukar Simons a farkon bazarar nan, amma alamu na nuna sun kusa kammala cinikin ɗanwasan Manchester United Alejandro Garnacho.

    Ɗanƙwallon zai fi sawun Joao Palhinha da Mohammed Kudus da Tottenham ta saya a wannan bazarar.

  7. Fenerbahce ta kori Mourinho bayan shekara ɗaya

    Jose Mourinho

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Fenerbahce ta kori mai horarawa Jose Mourinho bayan aikin shekara ɗaya da 'yan watanni.

    Tafiyar ɗan ƙasar Portugal ɗin ta zo ne kwana biyu bayan kulob ɗin ya kasa samun gurbi a gasar zakarun Turai ta Champions League, inda Benfica ta cire su a wasannin neman gurbi.

    Cikin wata sanarwa, Fenerbahce ta ce Mourinho "ya bar kulob ɗin" kafin daga baya ta gode wa mai shekara 62 ɗin. Daga baya wani jami'i a kulb ɗin ya faɗa wa BBC cewa korarsa suka yi.

    Mourinho, wanda ya horar da ƙungiyoyi 10 ciki har da Chelsea da Real Madrid da Manchester United da Tottenham, ya jagoranci Fenerbahce ta Turkiyya wajen ƙarewa a mataki na biyu a babbar gasar Turkiyya ta Super League a kakar wasa ɗaya da ya yi.

    Mourinho ya sha sukar alƙalan wasan Turkiyya, har ma an taɓa dakatar da shi wasa huɗu - wanda aka rage zuwa biyu - game da kalaman da ya yi kan alƙalan wasa bayan wasansu da babbar abokiyar hamayya Galatasaray.

  8. West Ham ta sayi Mateus Fernandes daga Southampton

    Mateus Fernandes

    Asalin hoton, Reuters

    West Ham ta amince da ɗaukar Mateus Fernandes kan fan miliyan 40 daga Southampton.

    Ɗanƙwallon mai shekara 21 ya samu izinin zuwa birnin Landan domin gwada lafiyarsa, inda zai zama na uku mafi tsada da West Ham ɗin ta taɓa saya.

    Cinikin zai zama ƙaimi mai girma ga mai horarwa Graham Potter, wanda ya yi rashn nasara a wasansa uku na farkon kakar bana a duka gasanni.

    Ɗanwasan na Portugal mai shekara 21 ya taka wa Southampton leda sau 46, inda ya ci ƙwallo huɗu da kuma bayarwa a ci wasu bakwai a kakar bara.

    Haka nan, West Ham na shirin kammala cinikin ɗanwasan Monaco Soungoutou Magassa mai shekara 21 kan kuɗi fan miliyan 17.3.

  9. Man City ta faɗa wa Tottenham Savinho ba na sayarwa ba ne

    Savinho

    Asalin hoton, Reuters

    Duk da yadda Tottenham Hotspur ta dinga kai tayi game da ɗanwasan gaba Savinho, Manchester City ta riƙe wuta cewa ɗanwasan ba na sayarwa ba ne.

    Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC Sport cewa mahukuntan City sun faɗa wa masu Tottenham cewa ba za su saurari wani tayi ba kan ɗanwasan a wannan bazarar.

    Ana ganin rashin samun ɗanwasan mai shekara 30 naƙasu ne ga Tottenham bayan ta gaza ɗaukar Eberechi Eze daga Crystal Palace. An yi imanin cewa City na neman fan miliyan 15 kan sa.

    Sai dai ana tunanin Ikay Gundogan na cikin 'yanwasan da za su bar filin wasa na Etihad a bazarar nan bayan barin sa a benci a wasan da Tottenham ta doke su 2-0 ranar Asabar.

  10. Man United ta ci gaba da ɓalɓalcewa ƙarƙashin Ruben Amorim

    Ruben Amorim

    Asalin hoton, PA Media

    Rashin nasarar da Manchester United ta yi a hannun Grimsby Town ya jawo cecekuce a faɗin duniya bayan doke ta 12-11 a bugun finareti ranar Laraba da dare a kofin Carabao.

    Har yanzu tawagar ta Ruben Amorim ba ta ci wasa ba a gasar bana, abin da ya ƙara jefa shi cikin matsi.

    Magoya bayan Man United sun tsammaci abin kirki a karawar da suka yi da ƙungiyar da ke buga gasa matsayi na uku a Ingila bayan kashe kusan fan miliyan 200 wajen cefane.

    Amorim ya fi kowane mai horarwa na Man United yawan kaso na rashin nasara tun bayan tafiyar koci Alex Ferguson.

    Kocin ɗan ƙasar Portugal ya ci wasa 16, da canjaras 12, da kuma rashin nasara 17 cikin wasa 45 da ya ja ragama zuwa yanzu.

    Hatta Ralf Rangnick, wanda ya jagoranci ƙungiyar tsakanin watan Disamban 2021 zuwa Mayun 2022, ya fi samun kaso mai yawa na nasara da kashi 38 cikin 100.

  11. Za a raba jadawalin Champions League ranar Alhamis

    Champions League

    Asalin hoton, Getty Images

    Birnin Monaco dake Faransa ne zai karbi bakuncin raba jadawalin Champions League ranar Alhamis.

    Za a yi bikin ne kamar na bara yadda aka raba ƙungiya 36, inda kowacce za ta yi wasa takwas huɗu a gida da huɗu a waje a matakin lik.

    Za kuma a raba su zuwa tukunya huɗu ɗauke da ƙungiya tara kowacce tun daga matakin wacce take da maki mafi yawa a ƙwazo wato coefficient ranking.

    Kowacce ƙungiya za a haɗa ta rukuni da biyu daga tukunyar farko da biyu daga tukunya ta biyu da wasu biyun daga tukunya ta uku da kuma biyu daga tukunya ta huɗu.

    Kungiya ba za a haɗa ta rukuni da wadda suke buga gasa tare ba, kuma ƙungiya ba za ta fuskanci ukun da suke gasa ɗaya ba.

    Paris St Germain ce ke rike da Champions League a karon farko da ta lashe a tarihi, bayan doke Inter Milan a kakar da ta wuce.

  12. Ƴan wasan da West Ham ta ɗauka da waɗanda suka bar ƙungiyar

    West Ham

    Asalin hoton, Getty Images

    Waɗanda ta ɗauka a bana:

    • Jean-Clair Todibo (Nice) £36.3m - after loan with obligation to buy
    • El Hadji Malick Diouf (Slavia Prague) £19m
    • Mads Hermansen (Leicester City) £20m
    • Daniel Cummings (Celtic) £250,000
    • Kyle Walker-Peters (Southampton) Free
    • Callum Wilson (Newcastle) Free

    Waɗanda ta rabu da su:

    • Mohammed Kudus (Tottenham) £55m
    • Aaron Cresswell (Stoke City) Free
    • Vladimir Coufal (Hoffenheim) Free
    • Danny Ings (Released)
    • Lukasz Fabianski (Released)
    • Michail Antonio (Released)
    • Patrick Kelly (Barnsley) Free
    • Kamarai Swyer (Northampton) Free
  13. Isak

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Sweden Alexander Isak mai shekara 25, ya faɗa wa Newcastle yana son rabuwa da ita zuwa Liverpool duk da shiga tsakani da shugaban ƙungiyar, Yasir Al-Rumayyan da kuma tattaunawa da ɗaya daga cikin masu ƙungiyar, Jamie Reuben. (Telegraph - subscription required, external)

    Manchester United ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan Real Betis mai shekara 25, Antony wanda za ta ba shi damar ya je zaman aro kafin daga bisani a yanke hukuncin zaman dindindin. (Telegraph - subscription required, external)

    Manchester United na kuma fatan nasarar saye mai tsaron raga, Senne Lammens daga Royal Antwerp kafin a rufe kasuwar cinikin 'yan wasa. (Telegraph - subscription required, external)

    Real Madrid da Atletico Madrid na bibbiyar ɗan wasan Manchester United da Ingila, Kobbie Mainoo mai shekara 20. (Mail, external)

  14. Man United za ta sayar da Hojlund ga Napoli

    Hojlund

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana ci gaba da tattaunawa kan sayar da Rasmus Hojlund ga Napoli daga Manchester United.

    Hojlund baya cikin ƴan wasan da Ruben Amorim zai yi amfani da su a kakar nan, har ma bai yi wa United wasa biyu ba da fara kakar bana ta Premier League.

    Shi dai kociyan Napoli, Antonio Conte na neman wanda zai maye gurbin Romelu Lukaku, wanda zai yi jinyar wata huɗu.

    Ranar Litinin za a rufe kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo a wasu kasashen Turai,

  15. Danny Ings

    Asalin hoton, Getty Images

    Sheffield United ta ɗauki Danny Ings, bayan da kwantiragin tsohon ɗan wasan tawagar Ingila ya kare a West Ham a karshen kakar da ta wuce.

    Mai shekara 33 ya amince da yarjejeniyar kaka ɗaya da cewar za a iya tsawaita masa da zarar ya taka rawar gani.

    Ings ya ci ƙwallo 15 a Premier League a West Ham, wanda ya koma can daga Aston Villa a Janairun 2023.

    Sheffield ba ta da maki ko ɗaya a Championship kuma ta karshe a teburi da cin ƙwallo ɗaya daga wasa uku da ta fara a bana.

  16. Dan wasan Newcastle, Isaka yana cikin tawagar Sweden

    Isak

    Asalin hoton, Getty Images

    Alexander Isak yana cikin tawagar Sweden da aka bayyana, duk da bai buga wasa ba da fara kakar bana, wanda ke son barin Newcastle United zuwa Liverpool.

    Mai shekara 25 yana yin atisaye shi kadai, bayan da ya dage sai ya koma Anfield a bana, duk da saura yarjejeniyar kaka uku ta rage masa a Newcastle.

    Shima sabon ɗan wasan Arsenal, Viktor Gyokeres yana cikin tawagar ta Sweden.

    Har yanzu Liverppol ba ta kara taya Isak ba, bayan da Newcastle ta ƙi sallama tayin fam miliyan 110 tun farko.

  17. Celtic ta kusan kammaala sayen Balikwisha da Saracchi

    Celtic

    Asalin hoton, Getty Images

    Celtic ta kusan kammala cinikin ɗan wasan Royal Antwerp, Michel-Ange Balikwisha da ɗaukar aron dan ƙwallon Boca Juniors, Marcelo Saracchi.

    Balikwisha, mai shekara 24, ya ci ƙwallo ɗaya a wasa huɗu a kakar nan, amma bai buga wa ƙungiyar karawa da Mechelen a babbar gasar tamaula ta Belgium.

    Mai tsaron baya, Saracchi, mai shekara 27, ya buga wa tawagar Uruguay karawa tara, wanda ya buga wasannin aro a Galatasaray da RB Leipzig da kuma Levante.

    Ana sa ran za a auna koshin lafiyar ƴan wasan a Glasgow a cikin makon nan.

  18. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Alejandro Garnacho ya yi watsi da tayin Saudiyya sa'o'i 48 da suka gabata yayin da ake tattaunawa tsakanin Manchester United da Chelsea kan ɗan wasan mai shekara 21 daga Argentina. (Fabrizio Romano, external)

    West Ham na gab da cimma yarjejeniyar fam miliyan 17.3 da ɗan wasan AS Monaco, Soungoutou Magassa. (Guardian, external)

    Ana tunanin ɗan wasan Nottingham Forest da Ivory Coast, Ibrahim Sangare mai shekara 27, ya je West Ham, yayin da ƙungiyar ke nazari kan Junior Mwanga mai shekara 22, da mai taka leda a Middlesbrough Hayden Hackney, ɗan shekara 23. (Sky Sports, external)

    Nottingham Forest ta gabatar da tayin fam miliyan 10 kan ɗan wasan Italiya, Nicolo Savona, mai shekara 22, amma Juventus ta yi fatali da tayin. (Gianluca di Marzio - in Italian, external)

    Crystal Palace ta cimma yarjejeniya da Villarreal kan ɗan wasanta na Sifaniya mai shekara 22, Yeremy Pino kan £26m. (AS - in Spanish, external)

    Ɗan wasan tsakiya a Liverpool James McConnell mai shekara 20, zai je Ajax. (Athletic - subscription required, external)

  19. Wolves ta kara ƙin sallama tayin Larsen daga Newcastle

    Larsen

    Asalin hoton, Getty Images

    Wolverhampton ta kara ƙin sallama ta yi na biyu da Newcastle United ta yi wa Jorgen Strand Larsen.

    Ƙungiar St James ta yi tayi na biyu kan fam miliyan 55, bayan da tun farko ta taya shi kan fam miliyan 50.

    Ita dai Wolves ba ta da niyyar sayar da ɗan ƙwallon Norway, saboda tana gani lokaci ya kure ba za ta samu madadinsa ba.

    Newcastle tana neman sayen sayen gurbin ɗan wasan dake buga gaba, bayan da Alexander Isak ya dage sai ya koma Liverpool da taka leda.

    Kenan Newcastle na fatan sayen Larsen, mai shekara 25, wandfa ya ci ƙwallo 14 a Premier League a kakar da ta wuce.

    Har yanzu Isak bai yi wa Newcastle tamaula ba a Premier League, bayan da ta fara tashi ba ci a Aston Villa da rashin nasara 3-2 a hannun Liverpool ranar Litinin a St James Park.

  20. Potter ya bukaci a samu haɗin kai tsakanin magoya baya da Bowen

    West Ham

    Asalin hoton, Reuters

    Kociyan West Ham, Graham Potter ya bukaci samun haɗin kai bayan da ƙyaftin Jarrod Bowen ya kalubalanci magoya baya a Molineux, bayan da Wolves ta yi waje da su a League Cup ranar Talata.

    Da kansa Bowen ya je wajen zaman magoya baya yana tafa musu, sai aka ga ya harzuka kamar dai an faɗa masa wata wagana da ta ɓata masa rai.

    West Ham ta kasa cin wasa uku da fara shiga gasar bana, wadda Sunderland ta doke 3-0 a makon farko da rashin nasara 5-1 a hannun Chelsea duk a Premier League.

    Ranar Talata Wolverhampton ta doke West Ham 3-2 ta kuma yi waje daga Carabao Cup na kakar nan.

    West Ham za ta je Nottingham Forest ranar Lahadi a wasan mako na uku a babbar gasar tamaula ta Ingila.