Kamal Harris da Donald Trump za su fafata a jihar North Carolina

Asalin hoton, ...
A kwana na hudu a jere, Donald Trump da Kamala Harris za su yi yaƙin neman zaɓe a jiha guda, kwanaki kaɗan gabanin zaɓen shugaban ƙasar Amurka da za a yi ranar Talata mai zuwa.
North Carolina ita ce jiha ta baya-bayan nan da za ta karɓi baƙuncin abokan hamayyar biyu.
Ƴan jam'iyyar Republican na kallon jihar a matsayin wadda ta zame dole su lashe kuma suna matsa ƙaimi wurin tabbatar da cewa jami'iyyar Democrat ba ta bayar da mamaki ba.
Cikin Shekara 50 da suka gabata Barack Obama ne kadai ɗan takarar jam'iyyar Democrat da ya taɓa lashe zaɓe a North Carolina














