Me ya sa matan Arewa ke ɗari-ɗarin shiga aikin ɗamara?

Asalin hoton, Nigerian Army
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Shiga aikin tsaro ko kuma ɗamara ga ƴaƴa mata wani abu ne da ake yi wa kallon baƙo a arewacin Najeriya, wataƙila saboda tasirin al'ada da addini ko yanayin zamantakewar al'ummar yankin.
Ƙa’idojin aikin sun yi tanadin cewa kowane mutum na da damar shiga aikin, matuƙar ya cika sharuɗɗan da ake buƙata ba tare da la'akari da jinsi ko addini ko ƙabila ba.
Mafi yawan mutane a yankin arewacin Najeriya, musamman ƙabilar Hausa/Fulani, na kallon aikin samar da tsaro a matsayin na maza kawai.
A baya-bayan nan, wasu jagororin yankin na arewacin Najeriya sun fara yin kiraye-kiraye da jan hankali kan shigar mata aikin ɗamara domin a dama da su a rayuwa.
Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Abdussalam Abubakar mai ritaya, na cikin masu irin wannan kira ga masu ruwa da tsaki da su magance matsalolin da ke hana matan ƙasar shiga aikin soji a ƙasar.
"Babban burinmu shi ne samar da sojoji daga kowane ɓangare da kuma jinsi domin nuna yadda ƙasarmu ke da mutane daban-daban, inda kowane jami’in tsaro ke da damar hidimta wa ƙasar domin bayar da tasa gudunmowa, ba tare da la’akari da jinsinsa ba’’, in ji shi lokacin da yake jawabi a babban taron shekara-shekara da hedikwatar tsaron ƙasar ta shirya kan gudunmowar mata a harkar tsaro.
"Dole ne mu yi aiki tare domin magnace matsalolin da suka jima a kasar nan suna hana mata shiga aikin soji."

Asalin hoton, Nigerian Army
Dalilan rashin shigar mata aikin ɗamara a arewa
Akwai dalilai da dama da ke hana mata shiga ayyukan samar da tsaro, musamman matan na yankin arewacin Najeriya, kamar yadda Farfesa Muhammad Kabir Isah, malami a makarantar koyar da ƙananan hafsoshin soji ta Kaduna a Najeriya (NDA) ya bayyana.
Ya ce a ɗaya daga cikin azuzuwan da yake koyarwa akwai ɗalibai 40, amma mace ɗaya ce kacal a cikinsu, kuma ba 'yar yankin arewacin kasar ba ce.
Kodayake ya ce akwai wani aji da mace ɗaya ‘yar jihar Borno ke ciki.
- Al'ada
Farfesa Kabir ya ce manyan abubuwan da ke kashewa matan Arewacin gwiwa su ne al’ada da addini.
Abdullahi Yelwa, malami a sashen nazarin muggan ɗabi'u da daƙile yaduwarsu a kwalejin fasaha ta Tatari Ali a jihar Bauchi, ya ce yadda ake tsarin horaswa ya saɓa da al’alda da addinin wasu mutanen ƙasar, musamman na arewaci.
''Na farko shi ne, yadda ake ɗaukar aikin ma kansa ya saɓa wa al'ada. Misali shi ne irin binciken da ake yi wa waɗanda ke son shiga aikin, da kuma yadda ake gudanar da shi.
"Kazalika, ga suturar da ake amfani da ita wajen aikin," a cewar malamin.
- Yanayin Horaswa
Farfesa Kabir ya ce wani dalilin shi ne yadda ake horas da jami’an tsaron ta hanyar aikin wahala, wanda ke tsoratar da matan shiga aikin.
Shi ma Abdullahi Yelwa ya ce azabtarwa a lokacin horaswa na daga cikin abubuwan da ke sare wa matan da dama gwiwa
‘’Yadda ake yi wajen guje-guje da tsalle-tsalle da ɗaukar abubuwa masu nauyi, da birgima a ƙasa, da shiga cikin cakwali, da goga kai a ƙasa da askin ƙwalƙwal, da sauran abubuwa masu wahala na daga cikin abubuwan da ke sanyaya wa matan gwiwa, musamman a arewacin ƙasar, waɗanda ba su saba ganin aikin wahala gidajensu ba," in ji shi.
- Rashin wayar da kai
Wani dalilin da ke sanya mata kauce wa aikin soji ko ɗamara shi ne rashin masaniya game da aikin.
Abdullahi Yelwa ya ce: ‘’Iyaye da dama ba su san yaya aikin yake ba, don haka suka gwammace su aurar da ‘ya’yansu ko su ɗora su a hanyar wani aikin maimakon na jami’an tsaro.
"Mafi yawan matan da ke aikin soja za ka samu mutanen da suka yi aiki a barikin soji ne, ko suka yi rayuwa a kusa da bariki, suke da masaniya game da aikin, su ne kawai ke bari ‘ya’yansu shiga aikin."
Mece ce fa'idar shigar mata aikin ɗamara?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farfesa Kabir ya ce yana da mutuƙar muhimmanci mata su riƙa shiga aikin samar da tsaro saboda basirar da Allah ya huwace musu.
“’Akwai wasu bayanan da mata ne kaɗai za su iya tatsarsu daga wajen masu laifi, ko masu shirin aikata laifi’’, in ji shi.
Aisha Muhammad Yakasai, mai muƙamin Cif Sufuritenda a hukumar samar da tsaron farar hula ta NSCDC (Civil Defense), ta ce akwai wasu laifuka da dama da jami’an tsaro mata ne kawai za su iya gano su.
"Idan ka samu mai laifi ko wadda ake zargi mace, ba za ta iya sakewa ta yi bayani ba a gaban maza, kamar yadda za ta yi a gaban mata’," in ji ta.
Abdullahi Yelwa ya ce rashin shigar matan aikin tsaro a Najeriya ba ƙaramar illa take haifarwa ba wajen yaƙi da aikata laifuka.
‘’Mata na da tausayi, ga kuma iya zance da hilatar mutane. Hakan zai sa su samu bayanan da suke buƙata da wuri daga wajen masu laifi fiye da takwarorin aikinsu maza’’, in ji shi.
Ya ƙara da cewa matan na da jajircewa da za su iya samar da tsaron da ake buƙata, saboda hikimar da Allah ya yi musu.
‘’Idan za ka iya tunawa a shekarun baya, an jibge su kan hanyar Abuja zuwa Kaduna domin daƙile ayyukan ‘yan bindiga, kuma cikin ƙanƙannin lokaci mun ga yadda suka samu nasarar aiwatar da hakan’’, in ji masanin tsaron.
Ta yaya za a zaburar da mata su shiga aikin?
- Kwaɗaitarwa
Farfesa Kabir: Ya kamata gwamnati ta ɓullo da wani abu da zai kwaɗaita musu shiga aikin, kamar ware musu albashi mai gwaɓi, da ɗaukar nauyin karatunsu, da kayan horaswa, ko ɗaukar nauyin iyayensu, da sauran hidimdimunsu.
- Sassauta sharuɗan ɗaukar aikin
Farfesa Kabir: Wasu daga ayyukan tsaron kan saka ƙa’ida cewa mace ba za ta haihu ba sai bayan shekara biyar da fara aikin, kuma ƙila ta shiga tana da shekara 30. Idan ba a yi sa’a ba ko da ta yi auren bayan shekara biyar din ba lallai ta samu haihuwa ba, wanda kuma shi ne maƙasudin auren.
- Wayar da kai daga jagororin al’umma
Farfesa Kabir: Yana da kyau shugabannin al’umma su riƙa fitowa suna faɗarkawa kan buƙatar shigar mata aikin soji.
- Samar da daidaito wajen ɗaukar aiki
Cif Sufuridenda Aisha Yakasai: Wani dalilin da zai sa a ƙara samun mata shi ne a samar da daidaito idan aka zo ɗaukar aikin jami’an tsaro, yadda za a bai wa maza gurabe masu yawa, haka ma a bai wa mata, ko kuma dai kada giɓin ya yi yawa.
Sirrin nasarar CS Aisha Yakasai a Civil Defense
Aisha Muhammad Yakasai na ɗaya daga cikin matan arewacin Najeriya da suka bijire wa al’ada kuma suka shiga aikin ɗamara.
Kasancewarta a aikin yana burge ƴanmata, kuma suke ta tururuwar shiga aikin saboda ita.
Aisha mai matsayin Cif Sufiretenda ta kwashe shekaru fiye da 14 a wannan aiki.











