Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 31/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 31/05/2025

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Ahmad Bawage

  1. Trump zai ƙaƙaba haraji kan ƙarafa

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa zai ninka harajin ƙarafa da Samfolo zuwa kashi hamsin a ranar Larabar wannan makon, domin kare waɗannan sassa biyu na Amurka.

    Ya bayyana hakan ne a wani taro da aka yi a wani kamfanin sarrafa ƙarafa na Amurka da ke Pennsylvania, inda ya kuma sha alwashin dakatar da duk wata ƙasa da ta nemi yin bara'a ga sabon matakin.

    Ya ce idan ƙasa ba ta da ƙarafa, ba ta cika ƙasa ba, ba za ta iya samar da makamai ba, don haka zai zamana ba ta da wani zaɓi illa zuwa ga China don neman taimakon makamai da jiragen ruwa da sauran abubuwan da ake samarwa da ƙarafa.

    A makon da ya gabata ne wata kotu a Amurkar ta yanke hukuncin cewa harajin da ya saka kan kayayyakin da ake shigo da su daga ƙetare ya saɓa wa doka, ko da yake an dawo da shi na wucin gadin bayan ɗaukaka ƙara.

  2. Fubara ya buƙaci magoya bayansa su yi godiya ga Tinubu

    Fubara

    Asalin hoton, X/@SimFubara

    Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yaba da ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu ya samar da maslaha a jiharsa.

    Fubara ya bayyana haka ne a wani taro da magoya bayansa suka shirya a Fatakwal, inda ya ce matakin na Tinubu ya taimaka sosai, wanda a cewarsa hakan ne ya har ya zama zai cigaba da kasancewa a matsayin gwamna.

    Tashar Channels ta ruwaito shi yana kira ga magoya bayansa da su yi godiya ga shugaban, inda ya ƙara da cewa ba don Tinubu ya shiga tsakani ba, da rikicin ya wuce abin da ake tunani.

    Fubara ya kuma yi godiya ga magoya bayansa da sauran ƴan Najeriya bisa nuna masa ƙauna, "ina godiya sosai da addu'o'inku."

    "Babu dalilin da za a ce ba za mu zauna lafiya da ogana ba," in ji shi a lokacin da yake bayyana alaƙarsa da Ministan Abuja. Nyesom Wike.