Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 20/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 20/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, da Ibrahim Yusuf Mohammed da Isiyaku Muhammed

  1. Rufewa

    To jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan za mu rufe shafin na yau, Laraba - 20/11/2024.

    A madadin kowa da kowa ni Muhammad Annur Muhammad nake fatan za ku kasance da mu gobe, Alhamis, 21/11/2024.

    Mu rufe da wannan karin maganar da ke cewa - Harbi ga ɗan jaki gado ne

  2. MDD ta buƙaci kafa asusun taimaka wa waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa

    António Guterres

    Asalin hoton, AP

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira da a samar da wani asusu na musamman domin taimaka wa waɗanda tashe-tashen hankali na ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi ya shafa.

    Majalisar ta nuna cewa hare-haren Boko Haram da sauran ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi sun haifar da tsananin wahala da tagayyara da tilasta wa dubban mutane barin muhallinsu.

    Darektan cibiyar yaƙi da ayyukan ta'addanci ta Majalisar, Mauro Miedico, shi ne ya bayyana haka a yau Laraba, a cibiyar yaƙi da ta'addanci ta Najeriya a Abuja, a lokacin ƙaddamar da shirin irin tsarin dokokin, tallafa wa rayuwar waɗanda ta'addanci ya shafa domin sake gina rayuwarsu.

    Jami'in na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi alkawarin haɗa gwiwa da gwamnatin Najeriya domin ganin an tallafa wa rayuwar waɗanda ta'addanci ya shafa.

  3. Sojojin Mali sun kori firaminista tare da rushe gwamnatinsa

    Kanar Assimi Goïta

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban gwamnatin mulkin sojin Mali ya kori firaministan ƙasar, Choguel Kokalla Maiga, tare da rushe gwamnatinsa.

    Matakin ya biyo bayan sukar da Mista Maiga ya wa, gwamnatin sojin a kan rashin inda aka dosa kan alƙawarin da sojojin suka yi a baya na mayar da ƙasar ga mulkin dumukuraɗiyya.

    Wata dokar soji da shugaban mulkin sojin, Kanar Assimi Goita ya yi wadda aka karanta a tashar talabijin ɗin ƙasar ta ce an soke ayyukan firaministan da mambobin gwamnatinsa.

    Firaminista Choguel Kokalla Maiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Firaminista Maiga ya nemi sojin su fayyace matsayarsu kan dawo da mulkin farar hula

    Tsawon shekaru Mali na fama tashin hankali na masu iƙirarin jihadi da 'yan a-ware, abin da ya haddasa mata juyin mulkin soji a 2020 da 2021.

    Sojojin sun yi alƙawarin gudanar da zaɓe tare da mayar da mulki ga farar hula zuwan watan Maris na wannan shekara ta 2024, to amma kuma daga baya suka ɗage yin zaɓen.

  4. Shugaban Nicaragua na son matarsa ta zama daidai da shi a shugabancin ƙasar

    Daniel Ortega da matarsa Rosario Murillo

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Nicaragua, Daniel Ortega, ya gabatar da wasu ƙudurce-ƙudurce masu tsauri da za a yi tsarin mulkin ƙasar kwaskwarimar da za ta bai wa shugaban ƙasa ƙarin iko.

    Daga cikin sauye-sauyen akwai ƙara wa'adin shugaban ƙasa daga shekara biyar zuwa shida, da kuma sauya matsayin mataimakin shugaban ƙasa - matsayin da matarsa, Rosario Murillo, take yanzu - zuwa matsayin shugaban ƙasa na biyu.

    Rahotanni sun ce sauye-sauyen kusan za su bai wa shugaban ƙasar iko fiye da dukkanin rassan gwamnati.

    Mista Ortega ya farmaki 'yan hamayya da masu suka tun bayan da aka yi zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a 2018.

    An tsare ɗaruruwan mutane ko kuma tilasta musu gudun hijira daga ƙasar ta Nicaragua.

    Mista Ortega, mai shekara 79, wanda tsohon ɗan yaƙin sunƙuru ne mai ra'ayin kawo sauyi na aƙidar ƙasar Cuba ta gurguzu, ya ƙwaci mulkin ƙasar ne a 1979, bayan da ya jagoranci juyin-juya-hali na kawar da gwamnatin kama-karya ta iyalan Somoza da suka mulki ƙasar tsawon shekara 40.

  5. Majalisar dokoki ta cire shugaban kotun ɗa'ar ma'aikata na Najeriya

    ..

    Asalin hoton, NTA

    A Najeriya, majalisar dattawan ƙasar ta amince shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke shugaban kotun ɗa'ar ma'aiakata ta kasar, wato Code of Conduct Tribunal, Ɗanladi Umar daga muƙaminsa.

    Matakin ya zo ne sakamakon abin da majalisar ta kira wasu halaye na rashin ɗa'a da ba za a taɓa amincewa da su ba, da suka haɗa har zargin da ya shafi cin hanci da rashawa.

    Kuma majalisar ta amince da naɗin wanda zai gaji shugaban kotun da ta sauke.

    An dai kwashe shekaru da dama ana ta kai ruwa rana da shugaban kotin da ɓangarorin gwamnati da dama.

    Bayanai daga zauren majalisar dattawan Najeriyar, sun ce 'yan majalisar sun yi amfani ne da tanadin sashe na 157 na kundin tsarin mulkin ƙasar, wajen sauke shugaban kotun ɗa'ar ma'ikatan daga muƙaminsa, a zamansu na ranar Laraba.

    Majalisar dattawan, ta ce ta ɗauki wannan mataki ne, domin kare martaba da ƙimar kotun ta ɗa'ar ma'ikata.

    Bayan ta sami jerin ƙorafe-ƙorafe da zarge-zarge masu yawa kan shugaban kotun, waɗanda suka shafi cin hanci da rashawa da dai sauran wasu laifuka da suka yi hannun riga da ɗa'ar ma'aikata.

    Hakan kuma ya sa majalisar dattawan ta gayyaci shugaban kotun a lokuta da dama, don ya bayyana a gaban tarukan bin ba'asin zarge-zargen da ake yi masa. Amma ko da ya halarci zaman kwamitin bin ba'asin sau ɗaya, sai ya ɗage ƙafa.

    A ƙarshe dai, yau 'yan majalisar dattawan Najeriyar suka amince da ƙudirin da ya nemi sauke shugaban kotun ɗa'ar ma'aikatan, da gagarumin rinjayen mutum tamanin da uku cikin ɗari da tara.

    Nan take kuma 'yan majalisar dattawan suka amince da naɗin AbdulLahi Usman Bello, wanda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa majalisar sunansa, don ya maye gurbin wanda aka sauke. Kana suka umarci sabon naɗin ya kama aiki ba tare da ɓata lokaci ba.

  6. Diddy yana fuskantar gomman shari'o'i yayin da yake zaune a gidan yari

    Sean "Diddy" Combs

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Laifukan da ake tuhumar Mista Combs da aikatawa na iya kai shi fuskantar ɗaurin rai-da-rai

    Fitaccen Mawaƙin Hip-hop Sean "Diddy" Combs a halin yanzu yana tsare a hannun gwamnatin Amurka yana jiran shari'a kan zargin yin lalata da kuma safarar mata domin tilasta masu aikata jima'i.

    Kama shi da aka yi a New York ya zo ne a lokacin da ya ke fuskantar jerin ƙararrakin da ke da alaƙa da zargin, da wasu ma ake zargin ya aikata tun sun shekarun1990s.

    Sama da mutane goma sha biyu ne suka shigar da ƙara a kan mawaƙin, inda suka zarge shi da yin amfani da tasirinsa a harkar nishadantarwa wajen aikiat abubuwan da suka haɗa da tilastawa mutane shan kwaya da cin zarafi da kuma fyade.

    Ƙararrakin na baya-bayan nan sun hada da zargin wasu maza biyu masu ƙaranocin shekaru a lokacin da ake zargin ya yi lalata da su. Dukansu sun bayyana cewa sun kusance shi ne da fatar cewa zai taimaka masu a masana'antar nishaɗi.

    Mawaƙin haifaffen Ungwar Harlem da ke birnin New York, ya musanta duka laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

  7. Kotu ta samu baƙon haure da kisan ɗaliba a Amurka

    Jose Antonio Ibarra

    Asalin hoton, Clarke County Sheriff’s Office

    An samu wani baƙon haure da laifin kisan wata ɗalibar karatun aikin jinya a jihar Georgia, ta Amurka, a wata shari'a da ta zama abar nuni a zaɓen shugaban ƙasar na wannan shekara.

    Jose Antonio Ibarra, mai shekara 26, ɗan Venezuela, ya kashe Laken Riley mai shekara 22 a watan Fabarairu, lokacin da take gudun motsa jiki na safe a harabar jami'ar da take.

    An samu Ibarra - wanda ya kawar da damarsa ta shari'ar masu taimaka wa alƙali yanke hukunci, da laifi a kan tuhuma goma, da ta haɗa da kisan kai da hayyaƙe wa mace da nufin yi mata fyaɗe.

    Sunan Ms Riley ya zama wani abin nuni ga masu ra'ayin riuƙau , waɗanda suka ce kisanta ya nuna irin gazawar da aka samu ta tsaro a iyakar ƙasar Amurka.

  8. Ana zargin mayaƙan RSF da kashe mutum aƙalla 40 a jihar Gezira ta Sudan

    Hoton gawarwaki a likkafani

    Asalin hoton, Gezira state residents

    Rahotanni daga Sudan na cewa waɗanda ake zargin mayakan RSF ne sun kashe mutane aƙalla 40 a jihar Gezira.

    Shaidu sun ce mayaƙan RSF sun kai hari a ƙauyen Wad Oshaid a jiya Talata da daddare kuma aka ci gaba da ba-ta-kashi har zuwa yau Laraba.

    Wani jami'in lafiya ya ce galibin waɗanda suka mutu an harbe su ne da bindiga.

    Ƙungiyoyin agaji suna zargin mayaƙan ƙungiyar da zafafa hare-hare a kan farar hula a jihar Gezira tun daga watan da ya wuce.

    Yaƙin basasan da ake yi a Sudan tsakanin mayaƙan RSF da dakarun sojin ƙasar ya janyo mutuwar dubban mutane a yayin da miliyoyi suka rasa matsugunanasu.

    Ana zargin ɓangarorin biyu da aikata laifukan yaƙi kuma rabin al'ummar Sudan miliyan 48.11 na buƙatar agajin gaggawa.

  9. Ukraine ta kai wa Rasha hari da makamin Birtaniya - BBC

    Makami mai linzami na Birtaniya

    Asalin hoton, Getty Images

    BBC ta fahimci cewa an yi amfani da makamai masu linzami da ke cin dogon zango ƙirar Birtaniya wajen kai wa Rasha hari daga Ukraine a karon farko.

    Rahotanni sun nuna cewa makaman sun faɗa wasu yankuna a kudu maso yammacin yankin Kursk.

    Masu yaɗa labarai a intanet na Rasha sun sanya wasu hotuna na abin da suka kira tarkacen makaman masu linzami na Birtaniya daga ƙauyen Maryino.

    Ana iya jin wata babbar fashewa a wani hoton bidiyo da ba a tabbatar da sahihancinsa ba, wanda aka ce na harin ne.

    Rasha ta sha alwashin mayar da mummunan martani a kan duk wani hari da aka kai cikin yankinta da makamai masu linzami da ke cin dogon zango na wata ƙasa ta yamma.

  10. Mun zura ido mu ga gudun ruwan Isra'ila kan tsagaita wuta a Lebanon - Sheikh Qassem

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabon shugaban ƙungiyar Hezbollah, Naim Qassem, ya ce ƙungiyar za ta sa ido ta ga iya gudun ruwar Isra'ila dangane da yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon ko hakan zai samar da mafita.

    Ya ce Hezbollah ta bayar da bayaninta kan ƙudurin yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta tsara.

    Ministan ƙasashen waje na Isra'il, Gideon Saar ya ce duk wata yarjejeniyar tsagaita wuta da za a cimma da Lebanon to dole ne ta tabbatar wa Isra'ila ƴancin ƙaddamar wa Hezbollah.

    Mista Gideon na magana ne kafin jakadan Amurka na musamman, Amos Hochstein ya kai ziyara Isra'ila dga Lebonon.

    Mista Hochstein ya ce ana samun cigaba da kuma zai iya yinsa wajen ganin an "kammala yaƙin nan."

  11. Isra'ila ta kashe mutum 36 a harin da ta kai Syria - Rahoto

    Hoton hari

    Asalin hoton, Syrian Observatory for Human Rights

    Aƙalla mutum 36 ne suka mutu a wani tari da Isra'ila ta kai ta sama a yankin gidajen jama'a da wani yanki na masana'antu a garin Palmyra da ke tsakiyar Syria, kamar yadda kafar yaɗa labaran gwamnatin Syria ta bayyana.

    Kamfanin dillancin labarai na Syriar, Sana, ya ruwaito wata kafa ta soji da ta ce jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari ne daga ɓangaren iyakar Jordan da misalin ƙarfe 13:30 (10:30 GMT), kuma hare-haren sun yi illa sosai.

    Wata ƙungiya da ke Birtaniya da ke sa ido a kan al'amuran da ke wakana a Syria ta ce mutum 41 ne suka mutu, kuma harin ya samu wata ma'ajiya ta makamai da kuma wasu wurare da ke kusa da inda iyalan mayaƙan sa-kai da Iran ke marawa baya suke.

    Sojojin Isra'ila ba su komai ba a kan rahotannin na waje kan wannan hari.

    Sai dai rahotanni na cewa a baya Isra'ila na amincewa da hare-haren da take yawan kaiwa Syria tun lokacin da aka fara yaƙin Gaza a watan Oktoba na 2023.

  12. Amurka ta ƙi yarda da shirin dakatar da yaƙin Gaza

    Joe Biden

    Asalin hoton, EPA

    Amurka ta hau kujerar na-ƙi a kan shawarar da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya gabatar don dakatar da bude wuta nan take kuma ba tare da wani sharadi ba a yakin Gaza.

    Shirin ya kuma jaddada bukatar sakin dukkanin mutanen da aka yi garkuwa da su tare da bai wa fararen hula a Gaza damar samun ruwa da abin da duk abin da suke bukata na rayuwa da kuma taimako.

    Dukkanin sauran mambobin kwamitin su 14 sun jefa kuri'ar amincewa da shirin, illa Amurka ita daya da ta ki amincewa da shi.

    Darektan kungiyar kare hakkin dan'Adam na majalisar dinkin duniya, Louis Charbonneau, ya zargi Amurka da abin da ya kira amincewa da miyagun laifukan keta haddin dan'Adam da Isra'ila ke yi.

  13. Ƴan tawagar Trump na da manufofin da suka ci karo da juna

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Idan da gaske yanayin ma'aikata shi ke nuni da yanayin manufofi, to babu shakka mun fahimci abubuwa da dama a wannan makon game da yadda Donald Trump ke da niyyar yin mulki a wa'adinsa na biyu.

    Fiye da manyan muƙamai 12, waɗanda wasu daga cikinsu za su buƙaci amincewar majalisar dattawa, sun ba da ƙarin haske game da tawagar da aka ba wa alhakin tafiyar da manufofinsa yayin da yake shirin komawa fadar White House.

    A fuska dai akwai alamun abin da ya haɗa su - aminci ga shi shugaban.

    Amma a ƙarƙashin ƙasa, akwai wasu manufofin da ke cin karo da juna.

  14. Biden ya amince a bai wa Ukraine nakiyoyin da ake binnewa a cikin ƙasa

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Joe Biden ya amince da bai wa Ukraine nakiyoyin da aka binne wa ƙasa, kamar yadda wani jami'in tsaron Amurka ya shaida wa BBC, matakin da ake ganin wani yunkuri ne na daƙile sojojin Rasha da ke ci gaba da kutse a yankin gabashin Ukraine.

    Jami'in wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce nan ba da jimawa ba za a kai irin waɗannan nakiyoyin kuma Washington na sa ran za a yi amfani da su ne a cikin Ukraine.

    Haka kuma Ukraine ta yi alƙawarin ba za ta yi amfani da nakiyoyin a wuraren da jama'a ke da yawa ba, in ji jami'in.

    A gefe guda kuma, Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce za ta rufe ofishin jakadancinta da ke Kyiv bayan ta "samu takamaiman bayani na yiwuwar kai wani hari ta sama a ranar 20 ga Nuwamba".

    A baya dai ofishin jakadancin ya ba da irin wannan gargadi na yiwuwar kai hare-hare ta sama a lokacin bikin sabuwar shekara da kuma zagayowar ranar ƴancin kai na Ukraine a watan Agusta.

  15. Gwamnatin tarayya za ta kawo karshen hukuncin kotuna da ke karo da juna - Minista

    Taron lauyoyi a kotu

    Asalin hoton, Nigerian Bar Association

    Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin Najeriya, Lateef Fagbemi (SAN), ya ce gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar kawo karshen yadda kotunan kasar ke yin hukunce-hukunce masu karo da juna, abin da tsawon wani lokaci ya addabi bangaren na shari'a.

    Ministan ya bayyana haka ne a jiya Talata a Ilori wajen bude taron kwana uku na neman kawo sauye-sauye a harkokin shari'a a Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Ma'aikatar shari'a ta Najeriya tare da taimakon Kungiyar Tarayyar Turai ne ta shgirya taron.

    Mista Fagbemi ya ce sabon alkalin alkalan Najeriya a shirye yake kuma shi ma a shirye yake ya bayar da hadin kai wajen yin wannan gyara.

    Kuma ya ce shugabancin kungiyar lauyoyi ta Najeriya ya nuna cewa lalle akwai bukatar kawo karshen wannan matsala.

    Fagbemi sya ce sauye-sauyen da ake matukar bukata a bangaren shari'a suna da muhimmanci sosai ga tsari da shirye-shiryen gwamnatin yanzu na raya Najeriya.

  16. Trump ya ci gaba da naɗa waɗanda za su riƙe muƙamai a gwamnatinsa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump ya zaɓi tsohuwar shugabar kamfanin kokawa ta WWE, Linda McMahon, a matsayin wadda za ta zame masa sakatariyar ilimi.

    McMahon wanda ta daɗe tana goyon bayan Trump, ta jagoranci hukumar kula da kananan ƴan kasuwa a lokacin mulkin Trump na farko kuma ta bayar da gudummawar miliyoyin daloli a yaƙin neman zaɓensa na shugaban ƙasa.

    Trump ya soki ma'aikatar ilimi, kuma ya yi alƙawarin rufe ta - aikin da zai rataya a wuyar McMahon bayan Trump ya koma fadar White House a watan Janairun 2025.

    Tun da farko Trump ya zaɓi Mehmet Oz, mashahurin likita kuma tsohon mai gabatar da shirye-shiryen talabijin, ya jagoranci shirin tabbatar da ingantacen kiwon lafiya, Medicaid.

    Zaɓen mutanen biyu da aka yi a ranar Talata - tare da zaɓin Trump na Howard Lutnick a matsayin sakataren kasuwanci - sun bi tsarin zaɓaɓɓen shugaban miƙa wa magoya bayansa masu aminci manyan muƙamai a majalisar ministocinsa.

  17. Ɗangote ya fara fitar da man kamfaninsa zuwa ƙasashen Afirka ta yamma

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Matatar man Ɗangote ta fara fitar da mai daga matatar zuwa ƙasashen Afirka ta yamma masu maƙwabtaka, a wani sabon yanayin kasuwanci da ka iya sauya kasuwar mai a Afirka.

    Wani rahoto da mujallar Bloomberg ta fitar ranar Talata inda ta ambato wasu bayanai da aka samu daga Vortexa da Kpler da Priecise Intelligence da ke bin diddigin bayanan jiragen ruwa, ya ce wani jirgin ruwa ɗauke da mai daga kamfanin Ɗangote inda ya nufi ƙasar Togo mai maƙwabtaka.

    Rahoton ya ce jirgi mai suna CL Jane Austen ya yi lodin mai fiye da ganga 300,000 daga matatar Ɗangoten.

    A watan da ya gabata ne dai shugaban kamfanin man ƙasar Ghana, Mustapha Abdul-Hamid ya ce ƙasar tasa na shirin sayen man daga hannun Ɗangote domin taimakon ƙasar rage yawan kuɗaɗen da take kashewa wajen shigar da mai daga nahiyar Turai kimanin dala 400 a kowane wata.

  18. Mahama: Tsohon shugaban ƙasar da ke neman sake komawa kan karagar mulkin Ghana

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    John Dramani Mahama ya taɓa zama shugaban ƙasar Ghana wa'dai ɗaya a baya - kuma a halin yanzu yana harin sake komawa kan karagar mulki.

    Tsohon shugaban mai shekaru 65 da haihuwa, ya jagoranci Ghana daga shekarar 2012 zuwa 2017 kuma yana ɗaya daga cikin gogaggun ƴan siyasar ƙasar da ke yammacin Afirka.

    Ya yi aiki a matakan gwamnati da dama, da suka haɗa da ɗan majalisa da mataimakin minista da minista, da mataimakin shugaban ƙasa da kuma shugaban ƙasa.

    Tun kafin ya ɗauke ta a matsayin sana'a, siyasa ta taka rawar gani a lokacin ƙuruciyar Mahama. Lokacin da Mahama yake ɗan shekara bakwai, an ɗaure mahaifinsa wanda a lokacin minista ne a gwamnati, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, kuma daga baya ya tafi gudun hijira.

  19. Ƙudurin zaɓe daga ƙetare ya tsallake karatu na biyu a majalisar Najeriya

    ...

    Asalin hoton, NASS

    Ƙudirin da zai yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima domin bai wa ƴan ƙasar mazauna ƙasashen waje damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓe ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai a ranar Laraba.

    Ƙudirin wanda shugaban majalisar, Abbas Tajudeen da Sodeeq Abdullahi suka ɗauki nauyinsa, na neman yin gyara ga dokar zaɓe ta 2022 domin a bayar da dama ga ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje su kaɗa ƙuri’a.

    An amince da karanta ƙudurin karo na biyu a watan Yuli, kuma an miƙa shi ga kwamitin da ke kula da harkokin zaɓe don ci gaba da nazarinsa.

    Sai dai bayan tsallake karatu na biyu a ranar Talata, an miƙa shi ga kwamitin gyaran kundin tsarin mulki don ci gaba tattaunawa a kansa.

  20. 'Za mu yi rashin nasara idan Amurka ta juya mana baya' - Zelensky

    ...

    Asalin hoton, UN

    Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya shaida wa manema labarai cewa Ukraine za ta sha kashi a yaƙinta da Rasha idan Washington, babban mai mara mata baya, ta janye tallafin da ta ke ba ta.

    Shugaban na Ukraine ya ce ''zai yi matuƙar haɗari idan muka rasa haɗin kai a Turai, kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne haɗin kai tsakanin Ukraine da Amurka''.

    Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya yi yakin neman zaɓe kan alƙawarin kawo ƙarshen shigar Amurka cikin yake-yake a maimakon haka zai yi amfani da kuɗaɗen masu biyan haraji wajen inganta rayuwar Amurkawa.

    Ya ce zai kawo karshen yaƙin Rasha da Ukraine cikin sa'o'i 24, ba tare da bayyana yadda za a cimma hakan. "Idan za su yanke tallafi, ina tsammanin za mu yi asara," Zelensky ya faɗa wa Fox News.

    Da aka tambaye shi ko Trump zai iya shawo kan Putin don kawo ƙarshen yaƙin, Zelensky ya amsa da cewa: "Ba abiu ne mai saukƙ ba amma eh, zai iya saboda ya fi Putin jajircewa.''