Garin da sarki ba zai sake ganin mahaifiyarsa ba idan ya hau karagar mulki a Najeriya

Asalin hoton, Joshua Adegbuyi, Olota of Odo Owa
- Marubuci, Ahmed Ambali
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist, Africa Planning
- Aiko rahoto daga, Lagos
- Marubuci, Opeyemi Adeoti
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Freelancer
- Aiko rahoto daga, BBC Yoruba, Lagos
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
‘’Gabanin bikin naɗina, masu zaɓen sarki suka rakani wajen mahaifiyata, a wata ziyara da nake ganin ita ce ta ƙarshe da zan ganta,” in ji sarki Joshua Adegbuyi Adeyemi, sarkin Odo Owa na ƙasar Yarabawa a jihar Kwara.
“Ta yi mini addu'o'i, kalamanta cike da tsantsar soyayya da nasiha. Tun daga wannan dare har yanzu ban sake ganin ta ba''.
Sarki Joshua na magana a kan daɗaɗɗun al'adun Yarabawa, waɗanda suka tanadi cewa dole ne a raba sarkin Odo Owa da mahaifiyarsa.
"Ban taɓa sha'awar zama sarki ba," in ji shi.
"Na san hakan zai raba ni da ganin mahaifiyata har abada."
Ƙaddarar sarauta
Odo Owa gari ne mai tarin manoma a jihar Kwara da ke tsakiyar Najeriya, inda rayuwa ke da sauƙi, idan aka kwatanta da sauran manyan garuruwa da biranen ƙasar.
Duk da cewa ya fito da babban gida, Sarki Joshua ya taso cike da fatan zama malamin jami'a, tare da kula da gonarsa a gefe guda, da kuma yin rayuwa cikin farin ciki tare da mahaifiyarsa da kuma 'ya'yansa.
A lokacin da yake matashi, wani shugaban coci ya faɗa masa cewa ya yi mafarkin ganin Joshua a kan wani babba muƙami.
Yayin da shugaban cocin ke labarta masa mafarkin, Joshua ya ɗauka cewa wataƙila zai zama limamin coci ne. Hakan ne ma ya ba shi ƙwarin gwiwar yin digirinsa na biyu a fannin ilimin Kiristanci.
Amma a yayin da yake ƙoƙarin bai wa mahaifiyarsa labarin karatunsa, sai ya samu labarin da ya girgiza shi.
‘’Masu zaɓen sarki ne suka zo suka gaɗa mana cewa sarki ya rasu,” in ji shi.
‘’Ban ma samu lokacin ba ta labarin ba, sai suka ce ni za a naɗa sarki. Bokanya ce ta fara maganar cewa lokacina ya yi da zan zama sarki.''
Sarki Joshua a yanzu na cikin tsaka mai wuya tsakanin martaba al'adar masarautar da kuma yin rayuwa ba tare da ganin mahaifiyarsa ba.
Abu ne da bai fiya yin tunaninsa ba. A cikin halin matsin lamba, ya gaggauta amincewa da matsayin kakanninsa ya kuma zama sarki.
Daɗaɗɗun al'adu
A ƙasar Yarabawa, akan zaɓi sarakuna daga gidajen sarauta, kuma sarakunan suna ci gaba da samun girmamawa. Sarautar gargajiya cike take da al'adu da abubuwan da al'adar ta haramta da ake gani a matsayin sirri.
‘’Sarki shi ne uba kuma jigo, wani bango da ke kare mutanensa daga cutarwa,'' in ji Ifayemi Elebuibon, fitaccen masanin harshe kuma ƙwararre kan al'adun Yarabawa.
‘’Akwai fa’idar zama sarki, amma sarki wani nau’in garkuwa ne ga duk wani sharri da zai samu mutanensa. Dole ne ya yi sadaukarwa domin tabbatar da al'ummarsa ta zauna lafiya''.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Elebuibon ya ce abin ƙi ne ke kare matsayi na musamman da ke kare sarki da kuma sanar da shi wasu sirrikan.
‘’Idan mutum ya zama sarki, to kowa ya koma ƙarƙashinsa, ciki har da iyayensa,'' in ji shi.
Dakta Reuben Akano na Jami'ar jihar Kwara, ya ce abubuwan na al'adu da camfe-camfe da suke kewaye da sarki, sun samo asali ne tun tale-tale da aka yi amanna cewa za su kare sarki daga cutuwa.
"Ba mutane ne kawai suka tashi rana guda suka ce suna son waɗannan camfe-camfe ba, gadarsu suka yi,” in ji shi.
"Ba za amince ka zama sarki, sanna ka ce za ka juya wa waɗannan al'adu baya ba, hakan ba zai taɓa yiwuwa ba.''
A lokaci na ƙarshe da Sarki Joshua ya ga mahaifiyarsa, masu zaɓen sarki sun gudanar da abubuwan al'adu da camfe-camfe da dama ciki har da buƙatarsa ya mayar mata da ''Oja'.
‘’Oja’’ shi ne majanyin da ta goya shi da shi a lokacin da yake jariri.
Mayar da majanyin na alamta kawo ƙarshen dangantaka tsakanin ɗa da mahaifinsa, wanda kuma hakan ne zai ba shi damar shirya wa babban aikin da ke gabansa.
''Wannan rabawar tsakanin ɗa da mahaifiyarsa ko iyayensa a wasu lokutan, wasu abubuwa ne da ke alamta komawar sarkin ''Kabiyesi'', wato wani mutum mai ƙarfin iko da ba za a iya tuhuma ba,'' in ji Elebuibon.

Asalin hoton, Joshua Adegbuyi, Olota of Odo Owa
Domin samun damar gudanar da mulkinsa cikin kwanciyar hankali da lumana, Elebuibon ya ce dole ne Sarki Joshua ya yi biyayya ga al'adun.
"Wani abu game da waɗanann camfe-camfe shi ne, mutumin da ya karya al'adar ba lallai ne ya zama shi ne zai girbi sakamakon ba,'' in ji shi.
‘’Yana iya zama 'ya'yansa ko a samu rashin zaman lafiya a ƙasarsa. A kodayaushe idan aka karya al'adar akan fuskanci ƙalubalen hakan. Kuma babu sarkin da zai so haka ga mutanensa''.
Baya ga rashin ganin mahaifiya, Sarki Joshua ba zai ga gawa ko jariri ba, ko ma keɓanta da matarsa da rana.
To amma haramcin ganin mahaifiyarsa, shi ne babban abin da ya fi damun Sarki Joshua.
"Babu abin da na sani a rayuwata, sai soyayyar mahaifiyata tun ina ƙarami,'' in ji shi.
“Ita ta biya min kudin makaranta, har na zama abin da na zama a yau. Ina jin baƙin ciki da takaicin rashin ganinta saboda wata al'ada kawai''.
A wani lokaci, sarkin kan yi sha'awar ganin mahaifiyarsa ta yi yawa har ya riƙa fatan bijire wa al'ada, ba tare da la'akari da sakamakon abin da zai faru ba.
“Na so haninta ta ɓarauniyar hanya," in ji shi.
Dangane da fargabar hakan ne ya sa masu zaɓen sarki a masarautar, suka ɗauki matakin da zai hana su haɗuwa, inda suka kulle shi a fadarsa tare da ɓoye mahaifiyar tasa.

Asalin hoton, King Abdulrasheed Akanbi
Sarki Joshua ya shahara a kafewa kan al'adun Yarabawa, a daidai lokacin da wasu sarakunan Yarabawa ke nisantar irin wannan al’ada.
Sarkin Iwo, Abdulrasheed Adewale Akanbi na garin Iwo, wanda ke cike da koyarwar ilimin addinin Musulunci, ya ƙalubalanci yadda wasu al'adun ke haramta musu abin da yake halas, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ‘yan gargajiya da ke kallon hakan a matsayin abin da ya saɓa al'ada.
A shekara ta 2016, Sarki Abdulrasheed ya ba da umarnin a cire wani gunkin Ogun, da wani gunkin Yarabawa na ƙarfe da wasu gumaka daga ƙofar shiga fadarsa, yana mai cewa, “dole ne a tsaftace gidajen sarauta daga tarin gumaka''.
A lokacin da aka ɗauke gunkin, masu bautar gargajiya na Ogun ba sa iya yin sadaukarwa ga gumakansu. Sun yi barazanar yin gangamin mutum miliyan guda domin nuna adawa da matakin sarkin, amma daga baya sun haƙura da matakin.
Har yanzu babau wani abu da ya samu Sarki Abdulrasheed , saboda ya saɓa al'ada, kuma ya ci gaba da sukar al'adun masu addinin gargajiyar.
A Odo Owa, babu sarkin da ya taɓa saɓa wa al'adar da ta haramta wa sarki ganin mahaifiyarsa.
"Idan na so zama irin sauran sarakuna, Kenan na saɓa wa wannan doka. Ni kuma na yarda da masu zaɓar sarkin masarautarmu domin ci gaba da martaba wannan al'ada a ƙasarmu,'' in ji Sarki Joshua.
‘’Da zan iya sauya wannan doka, da na sauyata, amma ba zan iya ba,” in ji shi.
Sarkin ya ce yanan fatan nan gaba a samu wani jarumin da zai kawo ƙarshen wannan al'ada, amma dai shi ba zai iya ba.
Cikin wani abu na ban tausayi, Sarki Joshua ya yi biyayya ga al'adar da ta tanadi cewa matuƙar mutum ya zama sarki ba zai ƙara ganin mahaifiyarsa ba, lamarin da ya sa har ta rasu bai sake arba da fuskarta ba.
Mahaifiyar tasa ta rasu a watan Yulin 2023.











