'Ƴan Najeriya ne za su zaɓi wanda zai yi takara a ADC'

Asalin hoton, ADC
Sabuwar haɗakar ƴan siyasa ta ADC a Najeriya ta ce ƴan ƙasar ne za su yanke hukunci kan wanda suke so ya yi wa sabuwar jam'iyyar takarar shugaban ƙasa a 2027.
Ibrahim Hussain Abdulkarim, Jigo a sabuwar tafiyar, kuma makusanci ga Peter Obi ya ce duk wanda zai yi takarar shugaban ƙasa a sabuwar haɗakar tasu sai ƴan Najeriya ta tantace shi sun kuma amince da shi.
''Za a bai wa ƴan Najeriya dama su zaɓi wanda suke so, wanda suke ganin zai taimaka wa talakawa, wanda zai magance matsalar tsaro, wanda zai fitar da ƙasar daga ƙangin talauci'', in ji shi.
Ibrahim Hussain Abdulkarim ya ce sabuwar haɗakar za ta bai wa duk wanda yake son tsayawa takara dama a fito ya bayyana wa talakawa abubuwan da zai yi musu.
Ya ƙara da cewa cikin masalaha sabuwar tafiyar za ta raba muƙaman da ke za jam'iyyar za ta tsaya takara.
















