Yadda rikicin cikin gida ya turnuƙe APC a Kano bayan saukar Ganduje

Asalin hoton, APC
Wata sabuwar dambarwa ta sake tasowa a cikin gidan jam'iyyar APC a jihar Kano, kwanaki kaɗan bayan saukar Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin APC na ƙasa.
Wasu ƴaƴan jam'iyyar sun fito suna neman shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas wanda na hannun daman Ganduje ne, ya sauka daga muƙaminsa, lamarin da ɓangaren Abdullahi Abbas ke zargin jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano da ingiza wa domin cimma wani buri nata.
Ko da yake ba ba wannan ne karon farko da APCn ke fama da rikicin cikin gida a Kano ba, wannan karon rikicin ya ɗauki sabon salo kuma ana alaƙanta shi da saukar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar a matakin tarayya.
A cikin yunƙurin da wasu ƴaƴan jam'iyyar ke yi a baya-bayan nan, har da gabatar da takarda ga shugabancin riƙo na APC na kasa, inda suka buƙaci a sauke Abdullahi Abbas daga shugabancin APCin Kano.
Ƙungiyoyi biyu ne da suka haɗa a 'APC kadangaren bakin tulu da kuma ƙungiyar 'ƴan takwas’ ke wannan fafutuka, kuma jagoran su, Nura Na'annabi ya shaidawa BBC cewa suna wannan fafutuka ne saboda wa'adin mulkin Abdullahi Abbas ta zo ƙarshe a bisa dokar, kuma ''muna zargin yana son neman shugabancin jam'iyyar karo na uku, wanda kuma ya saɓawa dokar APC''.
Ya ƙara da cewa ''Sannan akwai zarge-zarge da muke da shi a kansa na rashin iya tafiyar da mulki ko jagoranci na jam'iyya, sannan akwai zancen kalamai marasa gamsarwa waɗanda suke tayar da hankalin al'umma a cikin jam'iyya da kuma al'ummar da ake ƙoƙarin a jagoranta na jihar Kano''.
To sai dai ɓangaren shugaban jam'iyyar APCn na jihar Kano, ya ce wannan ba wani sabon abu ba ne, kuma ya zargi ƴan kwankwasiyya da ƙoƙarin haddasa musu fitina.
Sale Kala Kawo wani na hannun daman Abdullahi Abbas ne, kuma ya ce ''Duk cikin su babu wanda ke da damar yin wannan abu, domin jam'iyyar APC ai ba ƙaramar jam'iyya ba ce.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya jaddada cewa APC jam'iyya ce wadda ta gallabi gwamnatin jiha, kuma suna zargi cewa gwamnatin Kanon ce ta ɗauki nauyin su, ''Ƙarshe ma dai wai sunan ƙungiyarsu kadangaren bakin tulu, wanda suna cikin jam'iyyar kuma suke mata zagon ƙasa saboda wani abu da suke nema daga gwamnatin da muke zargin ta saka su''.
To sai dai jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano ta ce hawainiyar APC ta kiyayi ramarta, kuma idan har suna rikicin su na cikin gida, to kada su sanya NNPP a ciki, kamar yadda Ali Muhammad Bichi na NNPP ke cewa.
''Koke-koke da jam'iyyar APC ke yi, za a yi mata uziri domin ya kamata dama su koka, domin suna cikin zaman makoki musamman na sutale shi jagoran su da aka yi. Ba mamaki wannan zafin ne ke damun su suke neman ɗora wa wasu mutane laifin da ba su ji ba, ba su gani ba'' in ji Ali Bichi.
Bisa ga dukkan alamu dai jam'iyyar APC duk da kasancewar ta mai mulki a Najeriya, tana fama da nata rikicin na cikin gida, kuma masharhanta na ganin tilas sai ta sake lale, saboda waɗannan abubuwa da suke faruwa alama ce cewa muddin ba ta ɗinke ɓarakar da ke tsakanin ƴaƴanta ba, mai yiwuwa su fuskanci ƙalubale yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.










