Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 04/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Rabi'atu Runka da Isiyaku Muhammed

  1. Mutum biyu sun rasu a rikici tsakanin soja da ɗansanda a Nasarawa

    An tabbatar da mutuwar mutum biyu a ƙaramar hukumar Obi ta jihar Nasarawa a ranar Lahadi bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin soja da ɗansa da ke aiki a ofishin ƴansanda na Jenkwe a kasuwar Agyaragu.

    A wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansanda jihar, DSP Rahman Nansel ya fitar a ranar Lahadi, ya ce rikicin ya biyo bayan sace wani babur da aka yi.

    Sanarwar ta ce, bayan an kai rahoton satar, sai ƴansanda suka kama wanda ake zargi tare da taimakon wani ɗansandan sarauniya da ke aiki a ƙarƙashin ofishin.

    A lokacin da aka ɗauko wanda ake zargin za a tafi ofishin, sai wani soja wanda ke aiki a jihar Borno, amma ya zo hutu, ya tare ƴansanda domin hana su tafiya da wanda ake zargin.

    "Ana cikin hakan ne aka ci ƙarfin sojan, sannan rikici ya ɓarke, har dukansu suka samu raunuka da ɗansandan sarauniyar, amma daga baya sai sojan ya rasu," in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa daga baya wasu matasa sun zo sun ƙone ofishin ƴansanda, kamar yadda Channels ta ruwaito.

  2. Mu talakawa ne ba za mu iya yin belin yaranmu ba - Iyayen yaran da aka tsare

    Iyalan yaran da aka tsare kan zargin yin zanga-zanga a Kano da Kaduna sun koka kan a yi masu adalci.

    Iyaye da ƴan uwan yaran sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa yaran su basu da hannu kan zargin da ake masu na cin amanar ƙasa, inda suka roƙi hukumomi da su sakar masu ƴaƴansu.

    Mutanen sun bayyyana cewa su talakawa ne basu da ƙarfin da za su cika dukkan sharuddan beli da kotu ta bayar a Abuja.

    An kama masu zanga-zangar 76 a lokacin da aka yi zanga-zangar tsadar rayuwa daga ɗaya zuwa 10 ga watan Agusta, inda aka gurfanar da su a gaban babbar kotun Abuja a ranar Juma'a.

    Al'umma a faɗin Najeriya na ci gaba da bayyana takaicinsu kan bidiyon yaran da aka gurfanar gaban kotu daga wasu jihohin arewacin ƙasar.

    Yaran waɗanda gwamnati ta zarga da cin amanar ƙasa, sun bayyana a hotuna da bidiyo mabanbanta cikin yanayi na galabaita, ta yadda wasunsu ko tsayuwa ba sa iya yi.

    Masu ruwa da tsaki da kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun yi tir da wannan mataki na kai yara ƙanana gaban kotu, tare da bayyana shi a matsayin cin zarafinsu.

  3. 'Yanzu ba lokacin batun biyan diyyar bautar bayi ba ne'

    Sakataren harkokin wajen Biritaniya, David Lammy, ya ce manufar biyan diyya ga tsoffin ƙasashen mulkin mallaka da bautar bayi ta shafa ba abu ne da ya shafi kuɗi ba.

    Da yake jawabi a ziyararsa ta farko a Afirka, ya ce yana magana ne a wani lokaci da Burtaniya ke fama da matsin tattalin arziki da matsalolin kuɗi.

    Wannan dai shi ne kalamansa na farko kan batun tun bayan da shugabannin ƙasashe renon Ingila 56 suka rattaba hannu kan wata wasiƙa ta haɗin gwiwa a watan da ya gabata suna masu cewa lokaci ya yi da za a tattauna game da biyan diyya kan bautar da ƴan Afrika da Burtaniyar ta yi a baya.

    Sai dai Mista Lammy ya shaida wa BBC cewa ba wannan ba ce muhawarar da mutane ke so ba a yanzu. Ya ce Afirka na da damarmaki da yawa kuma a shirye Burtaniya ta ke don taimaka masu wajen cimma manufofinsu na ci gaba.

    Mr Lammy yana ziyara ne a manyan ƙasashen Afirka biyu masu ƙarfin tattalin arziki: Najeriya da Afirka ta Kudu.

  4. Remi Tinubu da Ribadu za su jagoranci yi wa Najeriya addu'a

    Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu za su jagoranci addu'a ta musamman domin neman sauƙin matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

    Za a gudanar da addu'ar ne ƙarƙashin jagorancin jagororin addinin Musulunci da Kirista, domin neman taimakon Allah a kan ƙalubalen da suka yi ƙasar dabaibayi.

    Chief Segun Balogun Afolorunikan, wanda shi ne darakta-janar na shirya addu'ar ta ƙasa ne ya sanar da hakan a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    Ya ce akwai buƙatar kowa ya bayar da nasa gudunmuwar domin magance matsalar da ƙasar ke fuskanta, inda ya nanata cewa haɗin kai na da muhimmanci wajen shawo kan dukkan matsala.

    "Bayan addu'ar, muna da yaƙinin Allah zai buɗe mana hanyoyin da za mu samu sauƙi," Afolorunikan, inda ya ƙara da cewa Najeriya za ta shiga shekarar 2025 cikin walwala.

  5. Zaɓen Amurka: Me ya sa jihar Iowa ke da muhimmanci?

    A daidai lokacin da hankali ya fara komawa ƙuri'a a zaɓen Amurka, an fara lissafa yadda ƙuri'ar za ta kaya, musamman a wasu jihohi da suke da muhimmanci.

    A zaɓen 2020, Trump ne ya lashe zaɓen jihar Iowa da ratar maki takwas, amma yanzu alamu na nuna zai iya faɗi a jihar.

    Jihar Iowa na da muhimmanci ne, inda take cikin jihohin da suke raba gardama tun daga shekarar 2012, wadda kuma ita ce shekarar ƙarshe da jam'iyyar Democrat ta lashe jihar. Hakan ya sa jam'iyyar Republican ke mamaki kan yiwuwar rasa jihar a bana.

    Zaɓen jin ra'ayin, Ann Selzer ne ya jagoranta, wanda kuma yana da nagarta.

    Selzer ya bayyana wa BBC cewa, "Lallai akwai wasu abubuwan lura. Dattawa ne ya kamata a ja ra'ayinsu, saboda su ne suka fi tabbacin kaɗa ƙuri'a, kuma Kamala Haris tana ƙoƙari a wannan fagen."

  6. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za kuma ku lekewa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.