Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 04/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Rabi'atu Runka da Isiyaku Muhammed

  1. Kwale-kwale ya kife da ƴan cirani 25 a Comoros

    Hukumar kula da ƴan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce aƙalla mutane ashirin da biyar ne suka mutu bayan da masu safarar mutane suka kifar da wani kwale-kwale da gangan a tsibirin Comoros.

    Kwale-kwalen mai ɗauke da mutane kusan talatin daga kasashe daban-daban, ciki har da jarirai biyu, yana kan hanya ne daga Anjouan zuwa yankin Mayotte na Faransa.

    Masunta sun ceto mutane biyar da suka tsira da safiyar Asabar.

    Hukumar kula da ƴan cirani ta duniya ta ce wannan hanya ta yi sanadin mutuwar dubban mutane, yayin da mutanen da ke gudun hijira a yankin Afirka ke ƙoƙarin tafiya mai haɗari zuwa nahiyar Turai.

  2. An bai wa ƴan ciranin da suka maƙale a tsibirin Diego Garcia damar shiga Birtaniya

    Wani ƙudurin gwamnatin Birtaniya na shirin bai wa ƴan ciranin da suka maƙale na tsawon shekaru a tsibirin Diego Garcia mai nisa na tekun Indiya ƴancin shiga Birtaniya.

    Kimanin ƴan Tamil na Sri Lanka 60 ne suka shafe fiye da shekara uku a wani sansanin wucin gadi da ke tsibirin, inda yake da wani sansanin sojan Birtaniya da Amurka a asirce, bayan da suka zama mutane na farko da suka shigar da buƙatar neman mafaka daga can.

    A baya dai, gwamnati ta nuna adawa da shigar mutanen Birtaniya kuma an shafe shekaru ana gudanar da shari'a kan makomarsu.

    A wata wasiƙa ranar Litinin, lauyoyin gwamnati sun ce "bayan ƙarin nazari" gwamnati ta ba da shawarar "sauya matsaya".

    A ƙarƙashin wannan, "dukkan iyalai da yara da mazan da ba a same su da wani laifi ba, za a ba su damar tura su kai tsaye zuwa Birtaniya".

  3. APC ta lashe duka ƙananan hukumomi 13 a zaɓen jihar Nasarawa

    Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulkin jihar Nasarawa a Najeriya ta lashe kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 13 na jihar da aka yi.

    Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Nasarawa (NASIEC), Barr. Ayuba Usman, shi ne ya bayyana hakan a hedikwatar hukumar da ke Lafiya,babban birnin jihar.

    Ya bayyana cewa baya ga kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 13, ƴantakarar jam’iyyar APC sun lashe kujerun kansila 140, yayin da jam’iyyar SDP ta lashe biyar, sai kuma Zenith Labour Party (ZLP) ta lashe biyu.

    Kujerun kansilolin ZLP biyu suna cikin ƙaramar hukumar Doma, na SDP huɗu a Nasarawa-Eggon, da kuma ɗaya a ƙaramar hukumar Keffi.

    Ya ce jam’iyyun siyasa 14 ne suka fafata a zaben, yana mai cewa amfani da fasaha ya ƙara sanya zaɓen ya kasance mai inganci.

  4. Ambaliya ta mamaye sassan birnin Barcelona

    Barcelona ya zama birni na baya-bayan nan da aka fuskanci ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Sifaniya, inda ruwa ya kai ga shiga wasu sassan filin jirgin birnin.

    Wani bidiyo ya nuna matafiya suna yawo a sassan da ambaliyar ruwa ta mamaye suna jan akwatunansu.

    Lamarin ya shafi tashi da saukar jirage da dama, yayin da ambliyar ta mamaye har da manyan titunan da ke kusa.

    Hukumar kula da yanayi ta ƙasar ta sanya wasu sassan yankin Cataloniya cikin shirin ko-ta-kwana domin fuskantar mamakon ruwan sama.

    Kafofin yada labarai na ƙasar sun nuna hotunan wasu motoci da ke nutsewa a kan wata babbar hanya.

  5. Hatsarin mota ya kashe mutum 36 a Indiya

    Aƙalla mutum 36 ne suka mutu yayin da 27 suka jikkata bayan wata motar bas ta faɗa cikin wani rami a jihar Uttarakhand da ke arewacin ƙasar India.

    Jami’ai sun ce mutum 44 ne ke cikin motar a lokacin da ta fada cikin wani rami mai zurfin mita 50 a Marchula na gundumar Almora ta jihar.

    Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan hatsarin.

    Motocin bas-bas ne aka fi amfani da su wurin sufuri a jihar kuma hatsari irin wannan ba baƙon abu ba ne. Motar na kan hanyar zuwa gundumar Ramnagar ta jihar ne a lokacin da hatsarin ya afku da safiyar ranar Litinin.

    Fasinjoji da dama ne suka mutu nan take, yayin da aka kai waɗanda suka jikkata asibitocin da ke kusa, ana kuma ci gaba da gudanar da aikin ceto.

    Firaministan Indiya Narendra Modi ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa, ya kuma sanar da biyan diyyar rupee 200,000 ga iyalan waɗanda suka mutu, da kuma rupee 50,000 ga wadanda suka jikkata.

  6. Isra'ila ta kai harin bama-bamai a Syria

    Kafofin yaɗa labaran Syria sun ce Isra'ila ta kai wani hari ta sama a kudancin Damascus, babban birnin ƙasar.

    Bidiyon da aka wallafa a intanet ya nuna hayaƙi na tashi a gundumar Sayyeda Zeinab kusa da inda ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ke da kayan aiki.

    Babu cikakkun bayanai game da asarar rayuka, kuma ya zuwa yanzu Isra'ila ba ta ce uffan kan lamarin ba.

    Tun da farko dai rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari a wani ƙauye da ke kudancin ƙasar Lebanon, inda ta kashe kwamandan sashen yaki da makamai masu linzami na Hezbollah (Riad Rida Ghazzawi).

    A gabashin ƙasar kuma, kafafen yaɗa labarai sun ce an tabbatar da mutuwar mutum 21 a cikin birnin Khiam da kewaye bayan da sojojin Isra'ila suka janye daga wani samame da aka kwashe mako guda ana yi.

  7. Labarai da dumi-dumi, Tinubu ya ba da umarnin sakin yaran da aka gurfanar a kotu kan zanga-zanga

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin sakin dukkan ƙananan yaran da aka kama da zargin cin amanar ƙasa sakamakon shiga zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

    Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya ce an kuma kafa wani kwamati da zai bincika yadda aka kama su, da tsarewa, da kuma kula da su.

    "Shugaban ƙasa ya ce a sake su kuma a sadar da su ga iyayensu," in ji ministan lokacin da yake magana manema labarai a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

    Bayanan sun fito ne jim kaɗan bayan kammala rantsar da sababbin ministoci bakwai da Shugaba Tinubu ya naɗa a fadarsa a yau Litinin.

    A cewar ministan, umarnin ya shafi dukkan yara a faɗin ƙasar, sannan kuma kwamatin zai yi aikin zai kasance ƙarƙshin ma'aikatar agaji da rage talauci, in ji ministan.

  8. Ƴansanda sun gurfanar da masu zanga-zanga kan cin amanar ƙasa a jihar Borno

    Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Borno ta gurfanar da mutum 19 da suka haɗa da wasu ƙananan yara uku a gaban kotu bisa zargin hannunsu a zanga-zangar tsadar rayuwa a watan Agusta.

    An gurfanar da su ne a gaban Mai Shari’a Aisha Mohammed Ali a babbar kotun jihar da ke birnin Maiduguri a yau Litinin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake matsa wa gwamnatin tarayya lamba kan ta janye tuhumar da ake yi wa ƙananan yara da aka kama saboda gudanar da zanga-zangar.

    A cewar takardar da aka gabatar a kotun, yaran uku suna tsakanin shekaru 14 zuwa 17.

    Gwamnatin jihar Borno ta gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume biyu da suka haɗa da cin amanar ƙasa, da kuma amfani da kafafen sada zumunta wajen ɓata sunan gwamnan jihar, da kuma tunzura jama’a a su yi wa gwamnati karan-tsaye.

    A cewar masu gabatar da ƙara, yaran suna daga cikin mutum bakwai da suka haɗa baki wajen kafa wata ƙungiya mai suna "Zanga-zanga" ta dandalin sada zumunta na WhatsApp da Tiktok, inda ake zargin sun amince da ɗaukar makamai, wanda ya saɓa wa sashe na 79 na dokar jihar Borno ta 2023.

    Kazalika, an tuhumi wasu mutane 11 da laifin ɗaga tutar Rasha a bainar jama'a, amma sun musanta zarge-zargen.

    Mai shari'ar ta dage sauraron ƙarar zuwa ranar 18 ga watan Nuwamba, inda ta bayar da umarnin kai yaran wuraren tsare yara masu laifi, yayin da za a ci gaba da tsare manyan cikinsu a gidan yara.

  9. An fara shari'ar waɗanda suka tunzura fille wa wani malami kai a Faransa

    An soma zaman shari'a a Paris kan wasu mutane da suka haɗa da maza bakwai, da mace ɗaya da ake zargi da yaɗa labaran ƙarya da ya kai ga wani matashi mai tsattsaurar akida ya fille kan wani malamin makaranta a shekarar 2020.

    Lamarin ya girgiza Faransa sosai a lokacin.

    Mutanen da za su iya fuskantar zaman kurkuku na tsawon lokaci idan aka same su da laifi, ana tuhumarsu da haɗa baki da ƙungiyoyin ta'addanci da kuma rura wutar ƙiyayya.

    Abdoullah Anzorov ya kashe Samuel Paty, malamin tarihi a wata makarantar sakandare da ke kusa da birnin Paris.

    Anzorov ya kashe Paty ne bayan da aka yaɗa saƙonni a shafukan sada zumunta cewa malamin ya nuna wa dalibansa zane-zane na Annabi Muhammad S.A.W. daga mujallar Charlie Hebdo a wani darasi kan ƴancin faɗin albarkacin baki.

  10. Iran ta soki aika jiragen yaƙi Gabas ta Tsakiya da Amurka ta yi

    Iran ta soki abin da ta kira kokarin Amurka na kassara zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya bayan Washington ta aike da jirage masu sakin bama-bamai a yankin.

    A wani taron manema labarai a Tehran, kakakin ministan harkokin waje, Esmaeil Baghaei, ya ce hakan ba zai sanyaya gwiwar Iran wajen kare kanta ba.

    Amurka ta sanar da aike wadannan jirage a ranar Asabar bayan Iran ta yi barazanar kai hare-haren ramuwa kan Isra'ila, sakamakon kashe mata sojoji hudu da farar-hula ɗaya a sansanonin ayyukanta na soji.

  11. Ana ƙara samun ruwan sama a yankin da aka samu mummunar ambaliya a Sifaniya

    Ana ƙara samun ruwan sama a yankin Valencia da ya lalace a kasar Spain, inda jama'a suka jefi Sarki Felipe da Sarauniya Letizia da firaminista da laka, suna kiransu makasa.

    Daga karshe Sarkin ya ce ya fahimci fushinsu da bacin ransu kan bala’in ambaliyar ruwan da ta afku a can, yana mai cewa jihar za ta dauki dukkan matakin da ya kamata don taimaka musu.

    Fiye da mutane dari biyu ne suka rasa rayukansu a fadin yankin.

    Har yanzu ana ci gaba da ƙoƙarin gano wadanda suka yi ɓatan dabo, don haka ne ma rundunar kare al'umma ta ƙasar ta aike da ƙarin dakaru.

    Ƴan sanda sun rika amfani da makiropon wajen shelantawa jama'a sakon hukumomi na su zauna a gida a jiya Lahadi, bayan da hukumar hasashen yanayi ta Sipaniyar ta ba da sabon gargadi.

  12. Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci

    Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rantsar da sababbin ministocin da ya naɗa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

    Da yake jawabi jim kaɗan bayan rantsar da su, Tinubu ya ce, "mun fara ƙoƙarin dawo da tattalin arzikinmu cikin hayyacinsa," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa, "muna kan tafarki mai kyau domin cika burinmu, ba ma don mu kaɗai ba, har da jin daɗin ƴaƴanmu da jikokinmu."

    Shugaban ƙasan ya ce duk da ƙalubalen da ake fuskanta, ana ci gaba da aikin inganta tattalin arzikin ƙasar.

    Sai ya bayyana wa sababbin ministocin cewa an zaɓo su domin su bayar da gudunmuwarsu domin ceto ƙasar.

    A ranar 23 ga Oktoba ce Tinubu na cire wasu ministoci guda biyar, sannan ya naɗa wasu guda bakwai.

    A ranar 30 ga Oktoba kuma Majalisar Dattawa ta tantance tare da amincewa da sababbin ministocin wato: Ministan jinƙai da rage talauci Dr Nentawe Yilwatda da inistan ƙwadago, Muhammadu Maigari Dingyadi da ƙaramar ministar harkokin waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu.

    Sauran su ne; Ministan masana'antau da kasuwanci da zuba jari, Dr Jumoke Oduwole da ministan kula da dabbobi, Idi Mukhtar Maiha da ƙaramin minstan gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da ƙaramar ministar ilimi, Dr Suwaiba Said Ahmad.

  13. Haramta ayyukanmu da Isra'ila ta yi zai nakasa ayyukan agaji a Gaza - MDD

    Hukumar tallafawa 'yan gudun hijirar Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNRWA ta ce haramta ayyukanta da Isra'ila ta yi zai nakasa ayyukan agaji a zirrin Gaza.

    Kakakin hukumar, Jonathan Fowler ya ce Hukumar UNRWA ce karfin ayyukan agaji da taimakon da fararan-hula ke samu a Gaza.

    Ministan harkokin wajen Isra'ila, Israel Katz, ya yi watsi da damuwar da Majalisar Dinkin Duniya ke nunawa, tare da shaida cewa kashi 13 cikin 100 na ayyukan agaji hukumar UNRWA ke bayarwa a Gaza.

    A yau Litiniin, Isra'ila ta sanar a hukumance cewa zata yanke alaƙa da hukumar, bayan ta zargeta da taimakawa Hamas wajen kai hare-hare.

  14. Zaɓen Amurka: Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuwa cewa sakamakon na yin kan-kan-kan

    Donald Trump da Kamala Harris sun fi mayar da hankali kan jihohi bakwai da za a fi gwabzawa a kansu a sa'oi 48 na karshe kafin gudanar da zabe.

    Kuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuna cewa sakamakon na iya yin kan kan kan.

    Donald Trump da ke yakin neman zabe a Pennsylvania, ya koka da cewa ba duka jihohin ne ke bukatar masu kada kuri’a su nuna wata shaida ba, abun da a cewarsa zai iya haifar da cuwa cuwa.

    Ya kuma ce ko a jikinsa, da za a samu wani ya kutso ya bude wuta ta cikin yan jaridar da ke wajen yakin neman zaben, kalaman da kwamitinsa ya ce barkwanci ne kawai.

    Kamala Harris, abokiyar karawarsa kuwa na nata yakin neman zaben ne a Michigan, inda ta mayar da hankali wajen neman goyon bayan mara fararen fata na jam'iyyar Republican.

  15. 'Yaranmu na cikin ƙunci bayan kama su da gwamnatin Sokoto ta yi kan zanga-zanga'

    A Najeriya, wasu ‘yan uwa da iyayen matasan nan da gwamnatin jihar Sokoto ke ci gaba da tsarewa a gidan gyaran hali bisa zargin su da gudanar da wata zanga-zanga bayan da ƴanbindiga suka kashe Sarkin Gobir na Gatawa Alhaji Muhammad Bawa, sun koka game da irin halin da suka ce ‘ya’yansu ke ciki tun bayan tsare su da aka yi.

    "Wallahi yaran nan suna cikin ƙunci da kuma mawuyacin hali, kuma ana azabtar da yaran nan," in ji wani uba.

    Mutanen Sabon Birnin sun ce kama yaran na su ba zai rasa nasaba da siyasa ba, kasancewar akwai wadanda aka saki daga cikin wadanda aka kama bayan an tabbatar da jam'iyar kowane ɓangare.

    "Akwai wasu ma ƙananan yara ne, wasu ma basu nan amman saboda basu jam'iyar gwamnati shiyasa aka kama su aka daure kuma har yanzu ba a sake su ba."

    BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin gwamnatin Sokoto, sai dai haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.

    Sai dai gwamnatin jihar Sokoto a baya, ta bayyana tsare su da cewa yana da alaka da karya doka ta hanyar gudanar da zanga-zanga domin domin tayar da hankali.

    Kungiyoyin kare hakkin bil Adama ma sun bayyana ci gaba da tsare mutanen a matsayin abinda ya saba ma doka.

    Babban jami'in gudanarwa na ƙungiyar Human Right Watch a arewacin Najeriya,Ibrahim Adamu Tudun Doki, ya ce abin ya basu mamaki saboda sun yi rubuce-rubuce ga gwamnati kan kama mutanen, " Abu duk ya zama akwai ra'ayi na siyasa, wani lokaci duk yadda za su yi su murɗa abu ta yadda gwamnati take da ra'ayi."

  16. Zaɓen Amurka: Ra'ayoyin ƴan Afirka kan zaɓen

  17. Me ke faruwa a jam'iyyar NNPP a jihar Kano?

    Ɓarakar da ke cikin jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta fara ɗaukar hankali a siyasar Najeriya, bayan wasu ƙusoshin jam'iyyar, sun yi hannun-riga da tsarin Kwankwasiyya, lamarin da masana suka ce ba abun mamaki ba ne.

    Ɗanmajalisar wakilai mai wakiltar Dala, wanda ƙusa ne a jam'iyyar, kuma na gaba-gaba a tsarin Kwankwasiyya, Ali Sani Madakin Gini ya fito a wani faifan bidiyo yana cewa ya fita daga tsagin Kwankwasiyya, inda ya ce, "Daga yau, na daina harkar Kwankwasiyya."

    Ali Madaki ya ƙara da cewa, "Kwankwasiyya ƙarya ce, Kwankwasiyya yaudara ce."

    Da yake yi wa BBC ƙarin bayani, ya ce, "Na fahimci cewa an gina tafiyar Kwankwasiyya ce kawai domin ci gaban Kwankwaso".

    Haka shi ma takwaransa da ke wakiltar ƙananan hukumomin Kibiya da Rano da Bunkure, Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya sanar da ficewarsa daga tsarin.

    Shi ma Hon. Rurum ya bayyana wa BBC cewa ya fice daga tafiyar ne sakamakon ''rashin adalci'' daga ɓangaren jagoran tafiyar, Rabi'u Kwankwaso.

    Sai dai duka ƴan majalisar biyu sun bayyana cewa har yanzu suna nan a jam'iyyarsu ta NNPP, amma ba sa cikin tsarin Kwankwasiyya, wanda ke ƙarƙashin jagorancin Sanata Rabi'u Kwankwaso.

  18. Kotu ta ce bayanan sirrin Isra'ila da suka fita ka iya jefa ƙasar cikin haɗari

    Wata kotu a Isra'ila ta ce bayanan sirrin da aka kwarmata da suka shafi wani na kusa da Firaiministan ƙasar na iya kawo cikas ga kokarin ganin an sako Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su.

    Yanzu haka ana gudanar da bincike kan mutumin da ake kira Eliezer Feldstein.

    Alkalin kotun ya bayyana cewa an cire wasu muhimman bayanai na sojoji ba bisa ƙa'ida ba, wanda mai yiyuwa hakan na iya yin illa ga tsaron kasar tare da sanya hanyoyin samun bayanai cikin hadari.

    Firayim Minista, Benjamin Netanyahu, ya musanta aikata ba daidai ba daga wani ma'aikacin sa.

    Wani jigo a jam'iyyar adawa, Yair Lapid ,ya ce akwai bukatar a gudanar da bincike don gano ko Mista Netanyahu ya ba da umarnin fallasa labarin.

  19. Yadda ƴanbindiga suka hana direbobi sakat kan hanyar Togo zuwa Nijar

    A jamhuriyar Nijar gamayyar ƙungiyoyin direbobi da ma'aikatan hanya ne ke nuna rashin jin dadinsu, game da asarar rayukan ƴaƴan kungiyar da ke zirga-zirga daga Lome babban birnin ƙasar Togo zuwa Yamai da ake samu.

    Kungiyar ta ce sau tari ƴanbindiga na tare ayarin motocin direbobinta su kashe direbobi ko yaransu kana su kona motocinsu.

    Lamarin baya bayan nan dai inji kungiyar ya faru ne a makon jiya inda yan bigigar suka kashe drebobi da yaran mota da dama harma da sojoji tare kuma da ƙona motoci masu yawa.

    Gamatie Mahamadou shine magatakardar kungiyar, ya shaida wa BBC cewa, suna tafka asara mai tarin yawa ta dukiya ga kuma kashe mutanensu da ake yi.

    "Gaskiya abun yana bamu mamaki, ace ƙasa uku sun haɗa ƙarfi da ƙarfe na soji amman ace hanya guda ta gagaresu, kuma alhali ansan hanyar nan ita ƙdai ce muka dogara da ita."

    Gamatie Mahamadou ya ce ana tara motoci dubu bakwai ko biyar kafin a yi ayari a kama hanya amman duk da haka ana tare su.

  20. Shin wane farashi ne Ɗangote ke sayar wa ƴankasuwa fetur a Najeriya?

    Matatar man Ɗangote ta sanar da farashin da take sayarwa ƴankasuwa man fetur a Najeriya, inda ta ce tana loda man kan jiragen ruwa kan naira 960 yayin da take sayar da litar 990 a mota.

    Hakan na zuwa ne bayan ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya, IPMAN ta ce tana sawo man da sauƙi daga waje fiye da yadda farashin Ɗangote yake a Najeriya.

    A wata tattaunawa da ƙungiyar ta yi da ƴanjarida ta bayyana cewa tana samun sauƙi sosai a waje, inda kuma ta yi kira ga Ɗangote da ya zauna domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan farashin.

    A cikin wata sanarwa da wani babban jami'in kamfanin ya sanyawa hannu, Anthony Chiejina, a daren jiya Lahadi, ta ce farashin na kan ƙa'idar da kamfanin NNPCL ya bayar.

    "Idan har wani zai sawo mai ƙasa da farashin da muke sayarwa, to lallai suna shigowa da marar inganci ne ba tare da sun yi la'akari da lafiyar ƴan Najeriya ko lafiyar ababen hawansu ba," In ji sanarwar.