KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa

Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni da kasuwar 'yan wasanni ta duniya daga nan BBC Hausa daga 24 zuwa 30 ga watan Agusta

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Abokan karawar Barcelona a matakin lig na gasar Champions League su ne:

    • Manchester City (a gida)
    • PSG (a waje)
    • Aston Villa (a gida)
    • Sporting Club (a waje)
    • Feyenoord (a gida)
    • Galatasaray (a waje)
    • Como (a gida)
    • Sabah (a waje)
    .

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Inter Milan za ta kara da:

    • Liverpool (a gida)
    • Real Madrid (a waje)
    • Club Brugge (a gida)
    • Borussia Dortmund (a waje)
    • Shakhtar (a gida)
    • Feyenoord (a waje)
    • Stuttgart (a gida)
    • Slovan Bratislava (a waje)
  3. Man City da PSG da Barcelona na rukini ɗaya

    Abokan karawar Manchester City a matakin lig na gasar Champions League su ne:

    • PSG (a gida)
    • Barcelona (a waje)
    • Sporting Club (a gida)
    • Porto (a waje)
    • Napoli (a gida)
    • Leipzig (a waje)
    • AEK Athens (a gida)
    • Lens (a waje)
    m

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Labarai da dumi-dumi, Real Madrid za ta fafata da Arsenal

    David Villa ya danna maballi domin bayyana abokan karawar Real Madrid.

    Su ne:

    • Inter Milan (a gida)
    • Arsenal (a waje)
    • PSV (a gida)
    • Roma (a waje)
    • Leipzig (a gida)
    • Shakhtar (a waje)
    • LASK (a gida)
    • AEK Athens (a waje)
    m

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Thierry Henry ya zaro ƙwallon farko. Real Madrid ce!

    Wa za ta kara da su?

  6. Me yasa Real Madrid ba za ta iya wasa da Liverpool ba a Anfield?

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool, Real Madrid, Inter Milan da Arsenal na cikin kungiyoyi 36 da za su shiga jadawalin zaɓen matakin lig na gasar Champions League ta kakar 2026-27 a ranar Alhamis.

    Wadannan kungiyoyi hudu, wadanda duk sun taba kaiwa wasan karshe na Champions League sau da dama, suna cikin tukunya ta farko a jadawalin zaɓen.

    Wannan na nufin suna cikin kungiyoyi tara da Uefa ta fi bai wa matsayi mafi girma da za su fafata a matakin lig na gasar bana.

    Sai dai wata sabuwar doka da Uefa ta gabatar a wannan kakar za ta takaita yiwuwar wasu wasanni da za su iya shafar dukkan kungiyoyin hudu.

    An fara amfani da tsarin matakin lig ne a kakar 2024-25, inda kowace kungiya ke buga wasanni takwas.

    Wadannan wasannin sun kunshi abokan hamayya takwas daban-daban, inda biyu ke fitowa daga kowace tukunya cikin tukwane hudu. Kowace kungiya tana buga wasa daya a gida da kuma daya a waje da kungiyar daga kowace tukunya.

    Amma daga wannan shekara, ba za a yarda wata kungiya ta karbi bakuncin kungiyar da ta taba karawa a gida a matakin lig a kowanne daga cikin kakar wasanni biyu da suka gabata ba.

    Wasanni biyu kacal ne suka cika wannan sharadi kafin zaɓen na ranar Alhamis. Su ne Liverpool da Real Madrid, da kuma Inter Milan da Arsenal.

  7. Tukunya ta huɗu

    • Viking (Norway)
    • Slovan Bratislava (Slovakia)
    • Slavia Prague (Czech Republic)
    • VfB Stuttgart (Germany)
    • LASK (Austria)
    • AEK Athens (Greece)
    • Como (Italy)
    • Lens (France)
    • Sabah (Azerbaijan)
  8. Tukunya ta uku

    • Feyenoord (Netherlands)
    • Lille (France)
    • Bodo/Glimt (Norway)
    • Napoli (Italy)
    • RB Leipzig (Germany)
    • Villarreal (Spain)
    • Shakhtar Donetsk (Ukraine)
    • Galatasaray (Turkey)
    • Fenerbahce (Turkey)
  9. Henry ya lashe kyautar shugaban Uefa ta shekara

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana bayar da wannan kyauta a kowace shekara ga mutanen da suka bayar da gagarumar gudunmawa ga ƙwallon ƙafa.

    Daga cikin waɗanda suka taba lashe ta a baya akwai Bobby Robson, Johan Cruyff, David Beckham da Didier Drogba.

    Da yake sanar da wanda ya lashe kyautar ta wannan shekara, shugaban UEFA Aleksander Ceferin ya ce "Na zaɓi Thierry Henry."

    Thierry Henry na nan a birnin Monaco domin karɓar wannan gagarumar karramawa.

    Tsohon ɗan wasan na Arsenal da Faransa ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasa a tarihin ƙwallon ƙafa, bayan ya lashe manyan kofuna tare da ƙungiyoyi da ƙasar Faransa, kuma ya kasance ɗaya daga cikin mafiya tasiri a wasan ƙwallon ƙafa na zamani.

  10. Ƙungiyoyin Premier biyar ne a cikin gasar

    Arsenal, Aston Villa, Liverpool, Manchester City da Manchester United za su san abokan karawarsu a gasar Zakarun Turai ta Champions League a yau.

    Akwai kungiyoyin Premier League biyar a cikin jadawalin zaɓen, tare da kungiyoyi biyar daga La Liga.

    Hakan ya faru ne saboda duka lig-ligen biyu sun samu guraben European Performance Spots, waɗanda ake bai wa ƙasashe biyu da suka fi kowa kyakkyawan sakamako a haɗe a gasar Champions League, Europa League da Conference League.

    Bayan kammala kakar wasa a matsayi na biyar a lig-ligensu, Liverpool da Real Betis su ne kungiyoyin biyu da suka amfana da waɗannan guraben.

  11. Tukunya ta biyu

    • Borussia Dortmund (Germany)
    • Roma (Italy)
    • Sporting (Portugal)
    • Aston Villa (England)
    • Porto (Portugal)
    • Manchester United (England)
    • Club Brugge (Belgium)
    • Real Betis (Spain)
    • PSV Eindhoven (Netherlands
  12. Tukunyar Farko

    • Paris St-Germain (France)
    • Bayern Munich (Germany)
    • Real Madrid (Spain)
    • Liverpool (England)
    • Inter Milan (Italy)
    • Manchester City (England)
    • Arsenal (England)
    • Barcelona (Spain)
    • Atletico Madrid (Spain)
  13. Ya ya tsarin rukunin Champions Lig zai kasance?

    Kungiyoyi 36 da suka samu gurbin shiga gasar an raba su zuwa tukwane hudu bisa ga matsayinsu a jadawalin ƙungiyoyi na Uefa.

    Za a fara da tukunya ta farko, inda za a zaro kowace ƙungiya daban-daban. Daga nan kuma manhajar kwamfuta ta Uefa za ta zaɓa mata abokan hamayya takwas.

    Paris St-Germain, Bayern Munich, Real Madrid, Liverpool, Inter Milan, Manchester City, Arsenal, Barcelona da Atletico Madrid duk suna cikin tukunya ta farko.

    Kowace ƙungiya za ta buga wasanni takwas gaba ɗaya, ciki har da ƙungiyoyi biyu daga kowace tukunya, wasa ɗaya a gida da wasa ɗaya a waje.

    Kungiyoyin Ingila ba za su iya karawa da wata ƙungiyar Ingila ba a wannan matakin na gasar.

    Ba za a iya shirya wasa da ƙungiya daga ƙasa ɗaya ba, haka kuma ba za a buga fiye da wasanni biyu da ƙungiyoyi daga wata ƙasa guda ba.

    Za a ci gaba da wannan tsarin har sai an tantance jadawalin wasannin dukkan ƙungiyoyi 36.

  14. Ko PSG za ta iya ɗauka karo uku a jere?

    Paris Saint-Germain ta ƙara jaddada girmanta a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa mafiya girma a tarihin Turai bayan ta zama ƙungiya ta biyu kacal da ta ɗauki gasar UEFA Champions League a jere.

    Bayan da ta doke Arsenal, PSG ta zama ƙungiya ta farko da ta yi nasarar kare kofinta tun bayan da Real Madrid ta lashe gasar sau uku a jere tsakanin shekarun 2016 zuwa 2018.

    Haka kuma, ita ce ƙungiya ta biyu kawai da ta cimma wannan nasara tun bayan da aka fara tsarin Champions League a shekarar 1993.

    A tarihin gasar wanda ya kai shekaru 71, PSG ta zama ƙungiya ta 10 kacal da ta lashe kofin nahiyar Turai sau biyu a jere.

  15. Fili ya ɗauki harama

    m

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwanaki 89 kacal bayan da Paris Saint-Germain (PSG) ta doke Arsenal a bugun fenariti domin lashe kofin Champions League karo na biyu a jere, lokaci ya kusa yi da za a san jadawalin wasannin zangon farko na kakar 2026-27.

    Masoya ƙwallon ƙafa a faɗin Turai suna ɗaukin jiran fitar da jadawalin, wanda zai bayyana waɗanne ƙungiyoyi za su kara da juna a sabon tsarin gasar Champions League.

    PSG ta kare kambunta ne bayan fafatawa mai zafi da Arsenal a wasan ƙarshe, kuma yanzu hankula sun koma kan sabuwar kakar wasa, inda manyan ƙungiyoyin nahiyar za su sake fafatawa domin neman lashe gasar.

    Da zarar an kammala fitar da jadawalin, ƙungiyoyi za su fara tsara yadda za su tunkari wasanninsu a zangon farko na gasar, wadda ake sa ran za ta sake kawo manyan wasanni masu kayatarwa a nahiyar Turai.

  16. Shugaban Hukumar kwallon Ƙafa ta Najeriya Gusau ya yi murabus

    ,

    Shugaban Hukumar Kwallon Ƙafa ta Najeriya Ibrahim Gusau ya yi murabus daga muƙamisa.

    Gusau ya shaida haka ne a yau Alhamis a shedikwatar Hukumar Kwallon Kafa ta kasar a wani taron manema labarai.

    An ta suka kan yadda tawagogin Najeriya na mata da maza suka gaza ƙoƙari a 'yan shekarun bayan nan, ciki har da gaza samun gurbi a gasar kofin duniya.

    Rahotanni sun ce hukumomin Najeriya na bincike kan hukumar ta NFF game da yadda ta kashe wasu kuɗaɗe naira 17bn don biyan albashi da sauran hidimar ‘yan wasa.

    A bangaren wasannin cikin gida kuma an yi zargin cewa alkalan wasa ba su samu kudadensu ba tun daga mako na 25 zuwa mako na 38, da dai sauran wasu korafe-korafe.

  17. Aston Villa na dab da sayan Jackson daga Chelsea

    Aston Villa na dab da cimma yarjejeniya da Chelsea domin daukar ɗan wasan gaba Nicolas Jackson a cinikin da zai kai darajar fam miliyan 65, wanda zai ba Villa damar sayar da Ollie Watkins.

    Akwai fahimtar juna tsakanin kungiyoyin biyu kan sharuddan cinikin Jackson mai shekaru 25. Chelsea na daf da samun adadin kudin da take nema, inda za ta karbi fam miliyan 47.5 daga farko, tare da karin fam miliyan 17.5 ta hanyar wasu kari cikin sharuddan yarjejeniya.

    Idan dan wasan na Senegal ya amince da sharuddan kwantiraginsa kuma ya kammala komawa Aston Villa, ana sa ran isowarsa za ta bude hanya ga dan wasan Ingila Ollie Watkins ya koma kungiyar Al-Hilal ta gasar Saudi Pro League.

    A wata yarjejeniya da za ta kai kimanin fam miliyan 51, Watkins mai shekaru 30 zai bar Villa Park bayan ya koma kungiyar daga Brentford a shekarar 2020.

    Tun bayan zuwansa Aston Villa, Watkins ya kafa tarihi a matsayin wanda ya fi kowa cin kwallaye a kungiyar a gasar Premier League, inda ya zura kwallaye 91 a gasar firimiyar, sannan 108 a dukkan gasa.

    a

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Ana samun ci gaba a cinikin Liverpool kan Barcola

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool na tattaunawa mai zurfi da Paris Saint-Germain PSG domin kammala cinikin ɗan wasan gaba da suka sanya a gaba a jerin burinsu, Bradley Barcola.

    Majiyoyi sun shaida wa BBC Sport cewa tattaunawar ta samu babban ci gaba a cikin sa'o'i 48 da suka gabata, kuma yanzu ɓangarorin biyu suna dab da cimma cikakkiyar yarjejeniya.

    PSG ta yi wa Barcola farashin fam miliyan 140, amma ana sa ran jimillar kuɗin da Liverpool za ta biya za ta kasance ƙasa da wannan farashi.

    Har yanzu akwai wasu ƙananan bayanai da ake kammalawa, amma ana sa ran yarjejeniyar za ta kai aƙalla fam miliyan 100, yayin da kuɗin zai iya ƙaruwa bisa wasu ƙarin sharuɗɗa da kari (add-ons) da aka tanada a cikin kwantiragin.

  19. Caicedo zai iya buga wasan Brighton

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Chelsea, Xabi Alonso, ya tabbatar da cewa Moises Caicedo da sabon dan wasa Marco Pallestra ba za su kasance cikin tawagar da za ta buga wasa na gaba ba, bayan dukkansu sun rasa wasan farko na Premier League da Fulham.

    Da yake magana game da lafiyarsu, Alonso ya ce "Ba dukkansu ba ne za su kasance a shirye gobe. Za mu gani, muna fatan Moi (Caicedo) zai iya dawowa a karshen mako. Muna bukatar mu sake duba yanayin Marco sosai."

    Kocin ya kuma bayyana cewa babu wani sabon rauni da kungiyar ta samu bayan nasarar da ta yi a Craven Cottage.

    A gefe guda, Alonso ya kwantar wa magoya baya hankali game da Cole Palmer, wanda aka ga yana dingishi lokacin da aka maye gurbinsa a rabin na biyu na wasan.

    Alonso ya ce Palmer yana cikin koshin lafiya kuma babu wata matsala mai tsanani game da lafiyarsa.

    Wannan labari ne mai dadi ga Chelsea, musamman game da Palmer, yayin da kungiyar ke kokarin gina kyakkyawan farawa a karkashin sabon koci Xabi Alonso.

  20. Har yanzu Barcelona ba ta yanke ƙauna ba kan Alvarez - Laporta

    m

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Barcelona, Joan Laporta, ya yi magana kan yunkurin da kungiyar ke yi na daukar dan wasan gaba na Atletico Madrid da kuma tawagar Argentina, Julian Alvarez.

    An dade ana rade-radin wannan ciniki tun farkon bazara, amma yayin da kwanaki kadan suka rage kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa, har yanzu babu wata alama ta cewa an kusa cimma matsaya.

    Laporta ya ce "Gaskiyar magana ita ce muna da matukar sha'awar wannan dan wasan kuma muna son a amince da tayin da muka gabatar."

    Ya kara da cewa "Muna fadin hakan ne cikin cikakken girmamawa ga Atletico Madrid, kuma muna son su sani cewa idan suna da niyyar sayar da shi a wannan kasuwar musayar 'yan wasa ta bazara, a shirye muke mu sayi dan wasan bisa ga tayin da muka mika musu."