'Muna fatan 'yansiyasa su tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaɓen Ghana'

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar raya tattalin arzikin yankin Afirka ta Yamma, Ecowas ta ce tana fatan 'yansiyasa Ghana za su tabbatar da zaman lafiya a tsawon lokacin zaɓen shugaban asar.
Shugaban tawagar ta Ecowas - wanda shi ne tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan - ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a gundumar Ayawaso West Wuogon.
Mista Jonathan ya ce tawagarsa za ta yi aiki da masu ruwa da tsaki wajen magance duka matsalolin da za su taso a lokacin zaɓen.





























