'Muna fatan sabon shugaban ƙasar Ghana ya kawo mana guraben aiki'
Kasuwanci da harkokin yau da kullum na gudana a Accra
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage
Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Amma za ku iya ziyartar shafin mu na bbchausa.com domin ci gaba da karanta labarai da kuma kallon bidiyo.
Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.
Ba zai yi wu a bar ƴan ta'adda su ƙwace Syria ba - Lavrov
Ministan
harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya ce ba zai yi wu ba a bari wata ƙungiya da ya kira ta ƴan ta'adda, ta ƙwace Syria.
Mr Lavrov na magana ne bayan ganawa da takwarorinsa
na Iran da Turkiyya da kuma Qatar.
Rasha ta kasance ƙawar shugaba Assad, kuma ta shige
gaba wajen tabbatar da ganin ya ci gaba da zama kan mulki a lokacin da ƙasar ta yi fama da rikici kusan
shekaru goma da suka wuce.
Sai dai kawo yanzu ba a ga ta bayar da irin wannan
tallafi ba ga Syria, duk da barazanar da shugaba Assad ke fuskanta daga ƴan tawaye a cikin makon nan.
Ana ci gaba da kidaya da tattara sakamakon zaɓen shugaban Ghana
Ana can ana ci gaba da kidaya da kuma tattara kuri'u a zaɓen shugaban ƙasar Ghana da aka gudanar yau Asabar.
Ana sa ran za a kwashe dare ana aikin tattara sakamakon
zaɓen.
Hukumar zaɓen ƙasar ce dai kawai ke da hurumin ayyana sakamakon
shugaban ƙasa.
Zuwa gobe Lahadi ake sa ran fara samun sakamkon a matakin
mazaɓu da gundumomi da kuma jihohi.
Bidiyo: Yadda aka watsar da filin jirgin saman soji a birnin Hama na Syria
Hotunan jirgi mara matuki da aka ɗauka, suna nuna yadda aka watsar da jirage a filin jirgin saman soji da ke birnin Hama na ƙasar Siriya.
Ƴan tawayen sun bayyana a ranar Alhamis cewa sun karɓe iko da birnin.
Hama dai na da mutane miliyan ɗaya kuma yana a kudancin Aleppo, wanda ƴan tawayen suka ƙwace a makon da ya gabata, bayan da suka kaddamar da wani harin ba-zata daga tungarsu da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon
Man City ta sake ɓarin maki a gidan Palace a Premier
Asalin hoton, Getty Images
Sau biyu ana fara cin Manchester City tana farkewa a Crystal Palace da ta kai sun tashi 2-1 a wasan Premier League ranar Asabar.
City, wadda ta kawo karshen kasa cin wasa daga karawar bakwai a jere ta doke Nottingham Forest a tsakiya mako, kenan an sa ran za ta yi abin kirki a Selhurst Park.
Ƙungiyar da Oliver Glasner ke jan ragama ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Daniel Munoz, saura minti 15 su je hutu Erling Haaland ya farke na 13 da ya zura a raga a bana.
Ɗan wasan Norway ya yi kan-kan-kan da Mohamed Salah na Liverpool a jerin waɗanda ke kan gaba a cin ƙwallaye a Premier League a kakar nan.
'Sojojin mu sun kafa shingaye a faɗin Damascus, babu wanda ya isa ya ratsa'
Ministan harkokin cikin gidan Syria ya ce jami'an tsaron gwamnati sun kafa shingaye a faɗin Damascus, babban birnin ƙasar, kuma babu wanda ya isa ya ratsa ciki, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.
Mohammed al-Rahmoun, da yake magana a gidan talbijin ɗin ƙasar a Damascus, ya ce: "Sojoji sun kasa sun tsare a dukkan wurare a faɗin Damascus da kewaye, kuma babu... wanda ya isa ya shata iyakar da muka yi, sojoji na shirye."
Ana kirga kuri'a a wasu rumfuna a birnin Kumasi
Ana can an fara kirga kuri'a a birnin Kumasi, bayan kammala kaɗa kuri'a a zaɓen shugaban ƙasar Ghana.
Mutane da dama ne dai suka fito a Ghana domin kaɗa kuri'a a zaɓen.
An fara kidaya kuri'u a wasu mazaɓu da ke birnin Accra
An fara kidaya kuri'u a wasu mazaɓu da ke Accra, babban birnin Ghana.
Kidaya kuri'un na zuwa ne bayan kammala kaɗa kuri'a a zaɓen shugaban ƙasar.
Ƴan sanda a Ghana sun kama mutum huɗu kan zargin harbi a arewacin ƙasar
Ƴan sanda a Ghana sun ce sun kama wasu mutum huɗu bisa zargin harbi da ya kai ga hallaka wani mutum a arewacin ƙasar.
Wata sanarwa da ƴan sandan suka fitar, sun ce ƙarin mutum guda ya samu rauni a harbin.
"Mutumin da ya jikkata na ci gaba da samun kulawar likitoci, sannan an kai gawar wanda lamarin ya rutsa da shi zuwa mutuware,"| a cewar sanarwar.
An kuma aika da jami'an soji zuwa yankin domin kwantar da hankali.
Faɗan Syria bai shafe mu ba, a yi duk abin da za a yi - Trump
Asalin hoton, Reuters
Zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump ya ce "Syria na cikin wani yanayi, sai dai ba ƙawar mu ba ce".
A wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta (Trump Social), ya ce "Abin da ke faruwa a Syria bai shafi Amurka ba. Wannan ba faɗan mu bane. A yi duk abin da za a yi. Ba za mu saka baki ba".
NNPCL na gudanar da jarrabawar ɗaukar ma'aikata
Asalin hoton, NNPCL
Babban kamfanin mai na Najeriya NNPCL na gudanar da jarrabawar ɗaukar sabbin ma'aikata.
Cikin wani saƙo da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce kimanin mutum 45,689 ne suke gudanar da jarrabawar wadda aka yi da kwamfuta.
''A yau NNPCL ya fara gudanar da jarrabawar ɗaukar ma'aikata da ake gudanarwa ta hanyar kwamfuta a cibiyoyi da dama a faɗin ƙasar nan'', in ji sanarwar.
NNPCL ya bayyana tsarin ɗaukar ma'aikatan da cewa tsari ne da yake gudanarwa a bayyane domin bai wa kowa dama.
''Domin damawa a kowa wajen ɗaukar aiki, NNPCL ya yi tanadi na musamman domin tabbatar da masu lalurar buƙata ta musamman da ke cikin masu neman aikin, sun samu damar gudanar da jarrabawar ba tare da wata matsala ba'', kamar yadda kamfanin ya wallafa a shafinsa na X
Ƴan sandan Ghana sun kama jami'in hukumar zaɓe da laifin aikata ba daidai ba
Asalin hoton, Electoral Commission Ghana
Ƴan sanda a Ghana sun ce sun kama wani jami'in hukumar zaɓen ƙasar da bayar da takardun kaɗa kuri'a guda 15 waɗanda aka cire sunan wani ɗan takarar shugaban ƙasa a mazaɓar Ampesika- Bayere.
Wata sanarwa da ƴan sandan suka fitar a ranar Asabar, sun ce sun kama jami'in ne mai suna Dery Joseph a mazaɓar da ke lardin gabashi na ƙasar ta Ghana, kuma suna ci gaba da gudanar da bincike.
"Muna riƙe da jami'in a halin yanzu domin ci gaba da yin bincike," in ji sanarwar.
Labarai da dumi-dumi, Shugaba Bashar al-Assad ya musanta tserewa daga birnin Damascus
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Shugaba Bashar Al- Assad na Syria (ɓangaren dama) ya musanta tserewa daga babban birin ƙasar
Ofishin shugaba Bashar al-Assad na Syria ya musanta rahotanni da ke cewa ya tsere daga Damascus, babban birnin ƙasar, a daidai lokacin da ƴan tawaye ke ci gaba da dannawa kan hanyar zuwa babban birnin da kuma Aleppo.
Ofishin ya yi Alla-wadai da "labaran karya da ake yaɗa wa", inda ya ƙara da cewa shugaban na ci gaba da gudanar da ayyukansa daga Damascus ɗin.
Shugaban Ghana ya yaba da yadda zaɓen ƙasar ke tafiya
Shugaban ƙasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya ce 'yan ƙasar sun nuna kishinsu yayin da zaɓen ƙasar ke gudana cikin kwanciyar hankali da lumana.
Yayin da yake jawabi bayan kaɗa ƙuri'arsa a mazaɓarsa ta East Akim da ke jihar Eastern Region, Mista Akufo-Addo ya ce zaɓen na tafiya bisa kwanciyar hankali da lumana.
Shugaban ƙasar ya ƙarfafa wa 'yan ƙasar da ba su fita zaɓen ba su gaggauta hakan kafin rufe rumfunan zaɓen.
''Duk wanda bai yi zaɓe ba ya gaggauta ya je ya kaɗa ƙuri'arsa, saboda kowace ƙuri'a na da muhimmanci,'' in ji shi.
'Yantawayen Syria sun danna zuwa birnin Damascus
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyoyi 'yantawayen Syria na dannawa zuwa Damascus, babban birnin ƙasar daga arewaci da kudancin ƙasar, yayain da dakarun soji ke ci gaba da rasa yankunan da ke hannunsu.
Rahotonni daga lardin Daraa da ke kudancin ƙasar sun ce 'yantawayen sun ƙwace iko da lardin, bayan da sojojin gwamnati suka fice daga lardin bisa alƙawarin ba su damar janyewa.
Bayanai da ke shigowa a yanzu sun nuna cewa a yanzu 'yantawayen da suka danno daga kudancin ƙasar suna tazarar kilomita 10 aga birnin.
A can ma yankin arewacin babban birnin, ƙungiyar IS da ke jagarantar tawayen sun ƙaddamar da hari kan birnin Homs.
Bayanai na cewa 'yantawayen sun ƙwace iko da birnin Quneitra da ke kusa da tuddan Golan da ke kusa da kan iyakar ƙasar da Isra'ila.
Ina hasashen samun kujerun majalisa fiye da 150 - John Mahama
Dan takarar jam'iyyar NDC, mai hamayya a zaɓen shugaban ƙasar Ghana, John Mahama ya ce yana cike da fatan samun nasara a zaɓen da ke gudanarwa yau a ƙasar.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri'arsa a mazaɓarsa ta North Tongu, John Mahama ya yaba da yadda hukumar zaɓen ƙasar ta shirya zaɓen ba tare da wata rufa-rufa ba.
''Wannan zaɓe ne da kowa zai iya hasashen abin da zai faru, saɓanin na baya da aka sha yi'', in ji shi.
John Mahama ya kuma yi fatan samun gagarumar rinjaye a majalisar dokokin ƙasar.
''Ina sa ran samun da kujerun majalisa fiye da 150'',
Asalin hoton, Sam Okudzeto Ablakwa/X
Ɗan takarar hamayyar ya kuma zargi gwamnatin Nana Akufo da mataimakinsa Bawumia da jefa ƙasar cikin halin matsain tattalin arziki.
''Sun lalata komai a ƙasar nan, don haka 'yan Ghana na buƙatar samun wani da zai ceto su daga halin da suke ciki.
Za a bar 'yanjarida su shiga zauren tattara sakamako - hukumar zaɓen Ghana
Asalin hoton, JeanMensa/Facebook
Hukumar zaɓen Ghana (EC) ta ce za ta bai wa 'yanjarida damar shiga rumfunan zaɓe da cibiyoyin tattara sakamakon zaɓen a duka faɗin jihohin ƙasar.
Shugabar hukumar, Jean Mensa, ta ce sun fara bai wa 'yanjaridar damar zuwa cibiyoyin tattara sakamakon zaɓen.
Yayin da take jawabi a taron manema labarai, Ms Mensa ta ce za a gudanar da komai a idan jama'a ta hanayar bai wa 'yanjarida damar shiga wurin zaɓen da ma cibiyoyin tattara sakamakon.
"Kun sani cewa a tun shekarar 1992, akan bar 'yanjarida su shiga cibiyoyin tattara sakamakon ne kawai idan za a abbayan wanda ya yi nasara, amma a wannan karo al'amarin ya sauya, a yanzu 'yanjarida za su samu damar shiga cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe a duka faɗin ƙasar nan', in ji ta.
Amurka da Birtaniya sun aike da saƙonni kan zaɓen Ghana
Ofishi jakadancin Amurka a Ghana ya yi kira ga masu zaɓe a ƙasar su tabbatar da gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana.
"Muna kira ga duk wanda ke da hannu a zaɓen na yau, ciki har da masu aikin sa-kai da masu sanya idanu da jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki su tabbatar an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, ba tare da rufa-rufa ba''
A nasa ɓangare shi ma ofishin jakadancin Birtaniya a Ghanar ya yi kira ga masu zaɓe su taimaka wajen samar da sahihin zaɓe a ƙasar.
'Yar takarar mataimakiyar shugaban ƙasa ta NDC ta koka kan ƙarancin fitowar masu zaɓe
Asalin hoton, Opoku Agyemang/X
'Yar takarar mataimakiyar shugaban ƙasa ta jam'iyyar NDC mai hamayya, Opoku Agyemang, ta kaɗa ƙuri'arta.
Yayin da take jawabi ga ,manema labaran bayan jefa ƙuri'ar tata, Ms Agyemang, ta yi kira ga al'ummar ƙasar su fito domin gudanar da zaɓen kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.
"Kuna jin haushin abin da ke faruwa a ƙasarmu yanzu, to ai don haka ne ma ya kamata ku fito ku yi zaɓen, me ya sa kuke jin haushi? To ai wannan ne dalilin da ya kamata ku fito ku yi zaɓen'', in ji ta.
"Wannan rana ce mai muhmmanci a gare mu, kuma sakamakon wannan rana zai shafi kowa. Ba wani don kaina ba, ina kira ga mutane su fito domin kaɗa ƙuri'a.''
'Yantawayen Syria sun ƙwace iko da manyan yankunan kudancin ƙasar
Asalin hoton, AFP
Rahotonni daga Syria na cewa 'yantawayen ƙasar sun ƙwace manyan garuruwa a kudancin ƙasar.
'Yantawayen sun ƙwace mafi yawan yankin Deraa - inda aka fara tayar da guguwar ƙin jinin shugaba Bashar al-Assad a 2011.
Wata cibiyar da ke lura da yaƙin mai mazauni a Birtaniya ta ce 'yantawayen sun kwace iko da mafi yawan sansanonin soji bayan 'gumurzu' da dakarun gwamnatin ƙasar.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ruwaito wata majiya daga 'yantawayen na cewa sun cimma yarjejeniya da sojojin ƙasar su janye daga yankin, inda su kuma 'yantawayen za su bar su su koma Damascus, babban birnin ƙasar, mai nisan kilomita 100 daga yankin cikin ruwan sanyi.
To sai da BBC ba ta iya tabbatar da waɗanan rahotonni ba, waɗanda ke zuwa a daidai lokacin da ƙungiyar IS da ke jagorantar 'yantawaye a arewacin Syria ke cewa ta ƙwace birnin Homs.
A ranar Juma'a ƙungiyar 'Observatory for Human Rights' ta ce 'yatawayen da ke kudancin ƙasar sun ƙwace kashi 90 cikin 100 na yankin Deera.