Ƴan tawaye sun ayyana tasu gwamnatin a Sudan

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan tawaye a ƙasar Sudan sun ayyana kafa gwamnati mai adawa da sojojin ƙasar, bayan shekara biyu ana gwabza faɗa a yaƙin da ya zama matsalar jin kai mafi girma a duniya.
Shugaban ƙungiyar Rapid Support Forces (RSF), Mohamed Hamdan "Hemedti" Dagalo, ya ce ƙungiyar na gina kyakkyawar makoma ɗaya tilo ga Sudan.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da aka gudanar da wani babban taro a birnin Landan domin tunawa da cika shekaru biyu da ɓarkewar yaƙin, inda sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy ya yi kira da a samar da "hanyar zaman lafiya mai ɗorewa".
An ci gaba da gwabza faɗa a ƙasar, inda sojoji suka ce sun yi ruwan bama-bamai a kan wuraren da ƙungiyar RSF ta mamaye a wajen birnin el-Fasher, lamarin da ya tilastawa dubban ɗaruruwan mutane tserewa daga sansanin ƴan gudun hijira na Zamzam.
Hemedti ya ce RSF tana ƙoƙarin tabbatar da ''yanayin doka" a ƙasar Sudan, ba irin gwamnatin da wasu tsirarun mutane ke mulki ba.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta samar da muhimman ababen more rayuwa kamar ilimi da kiwon lafiya a faɗin ƙasar baki ɗaya.
Tun da aka fara yaƙin shekara biyu da suka gabata, an zargi ɓangarorin biyu da aikata laifukan yaƙi, waɗanda suka haɗa da kisan ƙare dangi da kuma cin zarafin mata.
