Ƙarshen rahotonnin kenan
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mun atafe da wasu sababbi gobe da safe.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Haruna Kakangi, Ibrahim Yusuf Mohammed da Muhammad Annur Muhammad
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mun atafe da wasu sababbi gobe da safe.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Wasu hotunan tauraron ɗan'adam da aka ɗauka na sansanin Zamzam sun nuna yadda mayaƙan RSF suka ɗaiɗaita mafi yawan sansanin.
Hare-haren da mayaƙan suka kai a ranar Lahadi sun yi sanadin konewar gidajen wucin gadin da aka yi a sansanin.
Masu fafutukar kare haƙƙin mata a Sudan sun ce mayakan RSF sun aikata fyade a yayin harin da suka kai sansanin 'yan gudun hijirar.
Masu fafutukar da ke rajin kare 'yancin mata a yankin ƙuryar gabashin Afirka da aka fi sani da Strategic Initiative for Women in the Horn of Africa, sun rawaito cewa mayakan sun yi garkuwa da akalla mata da yammata 25.

Asalin hoton, EPA
Shugabar hukumar cinikayya ta duniya, Ngozi Okonjo-Iwaela, ta ce ta damu matuƙa da hasashen da hukumarta ta yi cewa tattalin arzikin duniya zai fuskanci koma-baya a wannan shekarar.
Kazalika, hasashen ya ce kasuwannin hannun jari za su yi ƙasa sosai, yanayin da ke barazanar jefa duniya cikin matsin tattalin arziki.
Mrs Iweala ta ce hakan na da nasaba da haraje-harajen da Shugaba Trump ya ƙaƙaba wa ƙasashen duniya kan kayayyakin da suke shigarwa Amurka.
An yi wannan hasashen ne a wani taron da hukumar cinikayya ta Duniya da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke gudanarwa kan kasuwanci da cigaba.
Taron ya ce haraje-haraje da gwamnatin Amurka ke kakabawa, da rashin tabbas da duniya ta shiga kan manufofin kasuwanci za su fi yin naƙasu ga ƙasashe matalauta.
Wani alƙali a Amurka ya yanke hukuncin cewa akwai yiwuwar a samu gwamnatin Trump da laifin raina kotu bayan da ta ƙi bin umarni kan mayar da 'yan ciranin Venezuela ƙasarsu ƙarƙashin wata doka ta lokacin yaƙi.
Mai Shari'a James Boasberg ya ce gwamnatin Amurka ta bijire wa umarnin da ya bayar da baki na dawo da jiragen da suka kwashi 'yan ciranin.
Fadar gwamnatin Amurka ta ce an riga an makara lokacin da alƙalin ya bayar da umarnin domin tuni jiragen sun yi nisa a sararin samaniya.

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da kwamatin da zai tsara yadda za a gudanar da ƙidayar 'yan ƙasa a yau Laraba.
Shugaban wanda shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya wakilta ya bai wa 'yan kwamatin wa'adin mako uku da su gabatar da rahotonsu.
Karo na ƙarshe da Najeriya ta ƙidaya 'yan ƙasa shi ne a 2006, inda ƙididdigar ta nuna 140,431,790, inda aka samu maza 71,345,488 da mata 69,086,302.
Wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce Tinubu ya alaƙanta ƙidayar da cigaban ƙasa.
"Ku yi aiki da dukkan hukumomin da suka dace, ciki har da ma'aikatar kasafi. Dole ne wannan ma'aikatar ta jagoranci aikin saboda ba za ka iya yin kasafi ba idan ka san yawanmu ba," in ji shi.
Masu shigar da ƙara a Jamus na tuhumar wani likita a birnin Berlin da kashe marasa lafiya 15.
Sun zarge shi da sha'awar kashe mutane. Masu bincike sun ce likitan na amfani da wasu magunguna masu haɗarin gaske wajen kashe marasa lafiyan tsawon shekara huɗu.
Mutum biyar daga cikin waɗanda ya kashe ya ƙona gidajensu domin ɓatar da shaidar abin da ya aikata.
Masu shigar da ƙarar sun ce babu ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi ya kashe da ya yi mutuwa ta farat ɗaya.
Sun ce za a iya tuhumar sa da wasu laifukan na kisa yayin da ake ci gaba da bincike.

Asalin hoton, Reuters
Iran ta haƙiƙance cewa 'yancinta na ci gaba da inganta sinadarin Uranium domin shirinta na nukiliya ba abu ne da za a yi wata yarjejeniya a kansa ba.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Aaraqchi, ya ce: "Abin da yake tabbas shi ne cewa batun inganta sinadarin uranium na Iran haka yake, sannan abu ne da aka lamunta kuma batu ne na gaske, kuma a shirye muke mu kwantar hankalin masu damuwa a kai hankali.
"Amma maganar inganta sinadarin ba abu ne da za a yi wata yarjejeniya a kansa ba samsam."
Kalaman na Iran sun zo ne kafin fara zagaye na biyu na tattaunawa da Amurka a ranar Asabar mai zuwa.
Shugaba Trump ya yi barazanar tarwatsa tashoshin nukiliyar Iran da bamabamai idan har ta kafe cewa sai ta haɗa makamin na ƙare-dangi.
Iran ta ce shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne, amma hukumar nukiliya ta duniya IAEA ta ce Iran din ta inganta sinadrin Uranium da take da shi zuwa kusan matsayin wanda za a iya haɗa makami da shi.
Arsenal na shirin kare kwallaye uku da ta zura a ragar Madrid a Santiago Bernabeu gidan Real Madrid.
Wasan ya ja hankalin magoya bayan ƙungiyoyin biyu inda kowannensu ke da cika baki.
Wasu magoya bayan kungiyoyin biyu sun tafka muhawara.

Asalin hoton, Social Media
Ƴan tohuwar jam'iyyar CPC ta shugaba Muhammad Buhari sun jaddada goyon bayansu ga jam'iyyar APC da kuma shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Cikin wata sanarwa da suka fitar ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura sun yi watsi tare da musanta zargin rashin jin daɗin APC da kuma rahotannin da ke cewa za su fice daga jam'iyyar.
"Muna jaddada cewa ba mu fita ba ko niyyar ficewa daga APC," a cewar sanarwar mambobin tsohuwar CPC da suka ƙunshi har da ministocin gwamnatin Buhari.
Sai dai duk da sun jaddada goyon bayansu ga shugaba Bola Ahmed Tinubu amma ƴan tsohuwar CPC sun yi kira ga shugabancin APC ya yi tafiya da dukkanin ɓangarorin jam'iyyar a kowane mataki.
Najeriya ta rage wutar lantarkin da ta ke sayarwa Jamhuriyar Nijar da ke ƙarƙashin mulkin soja daga Megawatt 80 zuwa megawatt 46.
Hakan na nun cewa an raguwar wutar lantarki da kashi 42 cikin ɗari ga ƙasar. Ministar makamashi ta Nijar, Haoua Amadou, ta ce matakin ya sa wutar lantarkin ƙasar ya ragu da tsakanin kashi 30 zuwa 50 cikin 100, kuma ya tilasta wa kamfanin samar da wutar lantarki mallakar gwamnati Nigelec aiwatar da shirin rage wutar lantarki da ake rarrabawa zuwa sassan kasar wanda ka iya ɗaukar kwanaki da dama, musamman a birnin Yamai.
Najeriya ta dakatar da wutar lantarkin da take fitarwa zuwa makwabciyarta a wani ɓangare na takunkumin da aka ƙaƙabawa gwamnatin mulkin soji da ta hambarar da shugaban farar hula Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.
''Tuni dai Najeriya ta dawo samar da wutar lantarki amma tana samar da megawatt 46 maimakon megawatt 80 da aka saba," in ji Amadou
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ita kanta Najeriyar ke fama da ƙarancin wutar lantarki saboda karancin iskar gas da kuma ƙarancin zuba jari a ɓangaren makamshin ƙasar.
A halin yanzu ƙasar na samar da kimanin 5000mw, wanda da kyar ya ke isar al'ummarta,
Masana sun ce Najeriya na buƙatar aƙalla megawatt 30,000 kafin a samu wadatar wutar lantaki a ƙasar.

Asalin hoton, EFCC
A yayin da wasu ƴan Najeriya ke ci gaba da ƙorafe-ƙorafe kan asarar da suka tafka a dandalin saka hannun jari na CryptoBank Exchange (CBEX), hukumar yaƙi da cin hanci EFCC ta sanar da fara gudanar da bincike kan lamarin.
Rahotanni sun ce kuɗin da 'yan Najeriya suka yi asara a dandalin na CBEX sun kai sama da naira tiriliyan ɗaya.
Hukumar ta shaida wa BBC cewa ta haɗa hannu da rundunar ƴansanda ta ƙasa da ƙasa INTERPOL da hukumar FBI ta Amurka domin yunƙurin gano waɗanda ke da hannu a dandalin na CBEX tare da ganin yiwuwar karɓo wasu kuɗaɗen da suka maƙale.
Hakan na zuwa ne bayan ƙorafin da waɗanda suka sanya hannun jari a dandalin suka yi na cewar sun kasa cire kuɗaɗen da suka sanya.
Mutane da dama sun tafka mummunar asara bayan sun zuba maƙudan kuɗi a dandalin, sakamakon alƙawarin da aka yi musu cewa za su samu ribar kashi 100 bisa 100 na kuɗaɗen da suka sanya cikin wata guda.

Asalin hoton, Getty Images
An samu tsohon shugaban ƙasar Peru, Ollanta Humala da laifin halasta kuɗin haram tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari.
Wata kotu a Lima babban birnin ƙasar, ta ce Humala ya karƁi kuɗaɗe ba bisa ƙa'ida ba daga wani kamfanin gine-gine na Brazil Odebrecht domin ya gudanar da yaƙin neman zaɓensa a shekarun 2006 da 2011.
Ita ma matarsa, Nadine Heredia, wanda ta kafa jam’iyyar Nationalist Party tare da Humala, an same ta da laifin halasta kudin haram, inda ita ma aka yanke mata hukuncin ɗaurin shekara 15.
Ƙasar Brazil ta bai wa Heredia mafaka kuma za ta samu amintacciyar hanyar tafiya can tare da ɗanta, in ji ma'aikatar harkokin wajen Peru.
Bayan shari’ar da ta shafe fiye da shekaru uku ta na gudanarwa, kotun ta yanke hukuncin da aka daɗe ana jira a ranar Talata.
Humala ya halarci yanke hukuncin da kansa yayin da matarsa ta ji ta hanyar bidiyo.
Tsohon shugaban ƙasar mai shekaru 62 da matarsa sun musanta aikata ba daidai ba.

Asalin hoton, Médias Niger
Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ya jogoranci wata tawagar gwamnatin ƙasar domin kai ziyarar aiki zuwa Jamhuriyar Nijar.
Wannan shi ne karon farko da ministan harkokin wajen Najeriya ke ziyara a Jamhuriyar Nijar tun bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da gwamnatin Mohammed Bazoum a shekarar 2023.
An fara takun saƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu bayan dangantaka ta yi tsami tsakanin gwamnatin mulkin sojin Nijar da kuma ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afrika (ECOWAS) wanda shugaban Najeriya ke jagoranta.

Asalin hoton, Médias Niger

Asalin hoton, Médias Niger
Yayin da jinin kowa ke a ƙumba gabanin karawar Real Madrid da Arsenal a yammacin Laraba, wasu magoya bayan kungiyoyin sun bayyana ra'ayoyinsu kan yadda suke tunanin wasan zai kaya.

Asalin hoton, Caleb Mutfwang/X
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya sanar da haramta kiwo da daddare tare da taƙaita amfani da babura a faɗin jihar sakamakon yawaitar hare-haren da ake kai wa a wasu sassan jihar.
A cikin wani jawabi da ya yi a jihar a ranar Laraba, Mutfwang ya bayyana hare-haren a matsayin "ayyukan ta'addanci" da ke da nufin tarwatsa mazauna yankin da kuma tauye hakkinsu na kasancewa cikin lumana a yankunansu.
Gwamnan ya kuma haramta safarar shanu cikin ababen hawa bayan karfe 7 na dare.
Ya kuma hana amfani da babura daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safe a faɗin jihar har na wani tsawon lokaci inda ya ce umarnin zai fara aiki ne nan take.
Ya ce '' Ina jinjinawa masu ba da agajin gaggawa da jami’an tsaro bisa gaggarumin matakin da suka ɗauka, ina kuma gode wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya umurci jami’an tsaro da su tabbatar da adalci cikin gaggawa.''
Muftwang ya ce dole ne al'ummomi su ba da himma wajen kare kansu a cikin iyakokin da doka ta tanada.
Ya ce ''Ina kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin matasa da su sake farfaɗo da sintiri tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro. Dole ne mu haɗa kai don kare ƙasarmu, domin tabbatar adalci yayin da mu ke la'akari da kiyaye dokokin ƙasa.''
Aƙalla mutane 50 ne rahotanni suka ce an kashe bayan wasu ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Kimakpa da ke gundumar Miango a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar a ranar 14 ga watan Afrilu.
Harin ya zo ne makonni biyu kacal bayan da wasu ƴan bindiga suka kashe mazauna ƙauyuka biyar a ƙananan hukumomin Bokkos da Mangu.
Hukumomin ƙasar dai na ci gaba da ƙoƙarin ganin sun daƙile hare-hare a jihar da aka daɗe ana fama da rikicin kabilanci da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Asalin hoton, Getty Images
Takun saƙar da ake yi tsakanin shugaban kamfanin Starlink Elon Musk da gwamnatin Afirka ta Kudu kan gazawar kamfanin wurin fara aiki a ƙasar ya samo asali ne daga dokokin ƙarfafa baƙar fata na ƙasar, kuma yana iya kasancewa ɗaya daga cikin dalilan da ke haifar da taƙaddamar diflomasiyya tsakaninta da Amurka.
A wani saƙo da wallafa a shafinsa na X, Mista Musk ya yi zargin cewa ba a ba shi damar ƙaddamar da ayyukan kamfanin a ƙasar ba saboda shi ba baƙin fata ba ne.
Sai dai hukumar sadarwa mai zaman kanta ta Afirka ta Kudu (Icasa) - wanda ita ce hukumar da ke kula da harkokin sadarwa da watsa shirye-shirye - ta shaida wa BBC cewa Starlink bai taɓa miƙa buƙatar neman lasisi ba.
A ɓangaren ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, ta ce ana maraba da kamfanin ya yi aiki a ƙasar "idan har ya bi dokokin cikin gida".
Kafin ya samu damar aiki a Afirka ta Kudu, Starlink yana buƙatar samun lasisi, wanda ke buƙatar cewa sai ya samu mallakar kashi 30% daga mutanen da suka fito daga al'ummomin da aka bayyana a matsayin marasa galihu.
Hakan dai na nufin yawancin baƙaƙen fata a Afirka ta Kudu, waɗanda aka haramtawa shiga al'amuran da suka shafi tattalin arziki a zamanin tsarin wariyar launin fata.

Asalin hoton, Getty Images
Kotun ƙolin Birtaniya ta yanke hukunci a ranar Laraba cewa dokar daidaito ta Burtaniya ta bayyana mace a matsayin wadda aka haifa da halittar mace, inda ta yi watsi da hujjar gwamnatin Scotland na cewa ana iya ɗaukar waɗanda suka sauya jinsinsu daga maza zuwa mata, a matsayin mata.
Mai shari’a Patrick Hodge ya ce alƙalai biyar na kotun sun amince cewa “kalmomin ‘mace’ da ‘jinsi’ a cikin dokar daidaito suna nufin mace da aka haifa da halittar mace da kuma jinsin da aka haifi mutum a cikinsa.
Hukuncin yana nufin cewa waɗanda suka sauya jinsi, da aka bai wa takardar shaidar da ta amince da su a matsayin mata bai kamata a ɗauke su a matsayin mata ba.
Amma kotun ta ƙara da cewa hukuncin da ta yanke "bai ɗauke kariyar da ake bai wa waɗanda suka sauya jinsi ba", waɗanda "an kare su daga fuskantar ƙyama sakamakon sauya jinsin da suka yi."
Shari’ar dai ta samo asali ne daga wata doka ta shekarar 2018 da Majalisar Dokokin Scotland ta amince ita cewa ya kamata a samu wakilcin mata kashi 50 cikin 100 a majalisun hukumomin gwamnatin Scotland. Inda aka sanya waɗanda suka sauya jinsi cikin waɗanda aka bayyana a matsayin mata.
Ƙungiyar kare hakkin mata ta For Women Scotland wadda ta ƙalubalanci dokar, ta yi iƙirarin cewa majalisar dokokin Scotland ba ta da hurumin fayyace wanda za a ɗauka a matsayin mace, inda majalisar ta ce ma'anar mace ta haɗa da waɗanda ke da takardar shaidar sauya jinsi.
FWS ta yi nasarar ƙalubalantar wannan dokar.
Ƙungiyar ta ce hukuncin kotun zai yi matuƙar tasiri a Scotland da Ingila da Wales, musamman kan al'amuran da suka shafi ƴancin jinsi da kuma damarmakin shiga wasu wurare da suka haɗa da banɗaki da dakunan asibiti da kuma gidajen yari.

Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyar adawa ta Congress a Indiya ta ce za ta shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar a ranar Laraba bayan da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar ta tuhumi manyan shugabanninta, Sonia da Rahul Gandhi da laifin halasta kuɗaɗen haram.
Hukumar ta bayyana sakamakon bincikenta a wata kotun Delhi a ranar Talata, inda ta zargi Sonia da Rahul Gandhi da kafa kamfanin bogi da suka yi amfani da shi wurin mallakar kadarorin jaridar National Herald ba bisa ƙa'ida ba wanda ya kai sama da dala miliyan 233.
Mai magana da yawun jam'iyyar Jairam Ramesh ya kira tuhumar "bi-ta-da-ƙullin siyasa" daga ɓangaren gwamnati.
Iyalan Gandhi wanda a baya suka musanta aikata wani laifi ba su ce komai ba kan wannan sabuwar tuhumar.
Binciken ya kuma ambaci sunayen wasu mambobin jam'iyyar Congress, ciki har da shugabanta na ƙasashen ƙetare Sam Pitroda.
An shirya ci gaba da sauraren ƙarar ranar 25 ga Afrilu.

Asalin hoton, Reuters
Joe Biden ya yi amfani da jawabinsa na farko tun bayan barinsa mulki wajen sukar manufofin jin daɗi da walwalar al'umma na gwamnatin Donald Trump.
Tsohon shugaban na Amurka ya shaidawa wani taro a birnin Chicago cewa, gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakin ''ɗaiɗaita'' shirin jin daɗin jama’a, tsarin da Donald Trump da Elon Musk – wanda ke jagorantar shirin rage kashe kuɗaden gwamnati na fadar White House, suka ce zamba ta yi wa dabaibayi.
Gwamnatin Donald Trump na neman rage ma'aikata a hukumar da ke da alhakin biyan tallafin dala tiriliyan 1.6 kowanne shekara ga Amurkawa.
Biden bai ambaci sunan Trump ba yayin jawabinsa na ranar Talata, amma ya ce: "A cikin ƙasa da kwanaki 100, wannan sabuwar gwamnati ta yi mummunar ɓarna da ta wuce misali."
Biden - wanda ke magana a wani taron kare hakkin masu rayuwa da naƙasa - bai yi magana game da ficewarsa daga Fadar White House ko zaɓen shugaban ƙasa na 2024 ba yayin jawabin nasa.
Hukumar kula da jin daɗin Jama'a (SSA) ta kasance sanadiyar samun kudin shiga ga Amurkawa waɗanda suka yi ritaya ko ba za su iya aiki ba saboda rashin lafiya.
Tana da alhakin kula da kusan Amurkawa miliyan 67, wanda akasarinsu suka kasance tsofaffi.

Asalin hoton, Fellowship Baptist Church
An ceto wani fasto ɗan ƙasar Amurka da wasu mutane masu ɗauke da makamai suka yi garkuwa da shi a wani coci a ƙasar Afirka ta Kudu a makon da ya gabata bayan an yi wani ƙazamin artabu da ya yi sanadin mutuwar mutane uku.
An gano Josh Sullivan a garin Gqeberha da yammacin ranar Talata - yankin da aka sace faston mai shekara 45 a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.
Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan masu garkuwa da mutanen da ake zargin sun daɗe suna bibiyar al'amuran faston.
Alƙaluman ƴansanda sun nuna cewa a cikin shekaru goma da suka gabata, an samu ƙaruwar satar mutane da kashi 264 cikin 100 a Afirka ta Kudu.
A cikin wata sanarwa da aka fitar da safiyar Laraba, rundunar ƴan sandan Afirka ta Kudu ta musamman da aka fi sani da 'Hawks', ta ce an ceto Sullivan ne sakamakon “samun bayanan sirri inda wata tawagar haɗin gwiwa… ta hanzarta zuwa wurin da ake tsare da shi”.
Kakakin rundunar 'Hawks' Avele Fumba, ya ce a lokacin da jami’an suka isa gidan, waɗanda ake zargin sun buɗewa ƴansandan wuta yayin da suke yunƙurin tserewa cikin wata mota.