Rufewa
Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafi na labaran kai-tsaye. Da fatan kun ji daɗin kasancewa tare da mu.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 31/01/25
Usman Minjibir, Ahmad Bawage da Aisha Aliyu Jaafar
Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafi na labaran kai-tsaye. Da fatan kun ji daɗin kasancewa tare da mu.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Ofishin Hukumar EFFC da ke Legas ya gurfanar da wasu ƴan ƙasashen waje guda 12 a kotu bisa zargin zamba ta intanet.
Hukumar ce ta bayyana haka a kafofinta na sadarwa, inda ta ce ta gurfanar da ƴan ƙasar China 11 da ɗan ƙasar Phillipines 1 da wani kamfani mai suna Genting International Co. Ltd a gaban mai shari'ai D.I Dipeolu na babbar kotun tarayya da ke Legas.
Waɗanda ake zargin su ne Wang Zheng Ming da Li Yin Hui da Xian Hong Will da Zhang Xiao Lei da Long Zhao Ming da Guo Xiao Fei da Yang Sheng da Wang Zheng Feng da Chen Wenyuan da Liu San Hua da Luo Jia You da Rheign Dela Vega.
Sanarwar ta ce waɗanda aka kama suna cikin wani gungun masu harƙallar cryptocurrency da ake zargi da zamba da aka kama a ranar 19 ga Disamban 2024 a Legas.
Alƙalin kotun mai shari'a Depeolu ya ɗage sauraron shari'ar zuwa 7 ga 14 da 21 ga Fabrairun 2025 domin cigaba da sauraron ƙarar, sannan ya yi umarni a ajiye waɗanda ake ƙara a kurkukun Ikoyi da Kirikiri.
Majalisar dokokin Jamus ta yi watsi da ƙudirin ɗaukar tsauraran matakai kan ƴan ci-rani, bayan wata zazzafar muhawara.
Masu adawa daga ɓangaren Friedrich Merz mai ra'ayin ƴan mazan jiya ne suka gabatar da ƙudirin.
Sai dai jam'iyyun masu sassaucin ra'ayi sun zargi Mista Merz da yi wa tsarin siyasar Jamus karan tsaye.
Ƙuri'un jin ra'ayoyin jama'a sun nuna batun ƴan ci-rani ne babban abin da ke damun ƴan ƙasar masu kaɗa ƙuri'u.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu matasa da ake zargi da yin aure ba tare da izinin iyayensu.
Mataimakin kwamanda-janar na hukumar na jihar Kano, Sheikh Mujahid Aminuddeedn Abubakar ne ya bayyana a haka, inda ya ce matasan sun yi aure ne a wajen wani biki, bayan wani mutum na daban ya amince da biyan sadaki.
Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa abin da suka yi ya saɓa da karantarwar addini, inda ya ƙara da cewa hukumar ba za ta lamunci hakan ba.
"Mun kama matasan biyu da abokansu da ma waɗanda suka taimaka musu domin hana sake aukuwar haka," in ji shi.
Sojojin Uganda sun ce za su ƙarfafa tsaro a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo, a daidai lokacin da rikicin ya ƙara tsanani a yankin.
Yadda ƴan tawayen M23 da Rwanda ke goyon baya ke ƙara matsawa Kudanci, ya haifar da fargabar yaƙin zai fantsama wasu yankunan, wanda Uganda wadda ta haɗa iyaka da yankin da ake gwabza yaƙin ta ɗauki matakan tsare yankunanta.
Ƙwararru a Majalisar Ɗinkin Duniya sun zargi Uganda da goyon bayan M23 kodayake dakarun Uganda na aiki da sojojin Congo wajen yaƙar ƙungiya mai gwagwarmaya da makamai mai ikirarin jihadi ADF.
Ya yinda ƴan tawayen ke barazanar ci gaba da kai hari, mahukunta a Congo sun zargi Rwanda da mamaye wasu yankuna ba bisa ka'ida ba.
Ƙungiyar Aston Villa ta shiga sahun ƙungiyoyin da ke neman aron ɗan wasan gaban Manchester United, Marcus Rashford.
Tun ranar 12 ga watan Disamban bara rabon da Rashford mai shekara 27 ya buga wa Man U wasa, inda kocin ƙungiyar, Ruben Amorim ya mayar da shi ɗan benchi.
Wakilan Rashford sun gana da manyan ƙungiyoyi a turai domin nema masa ƙungiyar da zai je, amma dai har yanzu ɗan wasan bai yanke shawarar ƙungiyar da zai koma ba.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta kama mata da kuma wasu mutum biyu da ke da alaƙa da mutumin da ake zargi da yunkurin kai harin ta'addanci a filin taron Maulidin mabiya Ɗarikar Tijjaniya a makon da ya gabata.
Kwamishinan ƴan sandan jihar CP Salman Dogo ya ce mutumin da ya kitsa kai harin, Ahmad Adam Abba ɗan asalin ƙasar Chadi ne, kuma ya tsere zuwa ƙasar Kamaru amman suna ci gaba da bincike domin kamo shi.
Da yake gana wa da manema labarai, kwamishinan ƴan sandan ya bayyana cewa bayanan sirrin da suka samu a ranar 24 ga wannan watan, ya sa suka gano wasu na kokarin kai hari filin taron maulidi, har ma aka fitar da sanarwa cewa jama'a su yi hattara.
CP Salman ya kuma ce sun ƙwato wasu abubuwan fashewa, inda ya ƙara da cewa wanda ake zargin kafin zuwansa Kano ya kashe mutum goma 17 a Chadin kuma mutumin na shirye-shiryen kafa sansanin ƴan ta'adda a jihar.
Ba lallai Najeriya ta cike kujerun da ƙasar Saudiya ta ware mata ba a hajjin bana sakamakon samun ƙarancin masu biyan kuɗi a yayin da wa'adin da aka sanya na biyan kuɗi ke cika a yau 31.
Rahotanni na nuna cewa akwai yiwuwar samun gagarumin giɓi a kujerun da hukumomin Saudiyya suka ware wa ƙasar.
Ko a shekarar da ta gabata ma mutum 51,447 ne kawai suka biya cikin kujeru 95,000 da aka ware wa ƙasar.
Hukumar aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta sanya kuɗin kujerar hajjin 2025 a kan naira miliyan 8.78 ga jihohin kudancin ƙasar, yayin da na arewa maso gabashin ƙasar za su biya nai miliyan 8.32 , sai kuma naira miliyan 8.45 na jihohin arewa maso yammaci.
A Najeriya, daga shekarar 2019 zuwa yanzu, farashin kujerar aikin hajji ya ninka fiye da sau biyar inda a shekarar 2019 kuɗin ya kama naira miliyan 1.5, lamarin da ake ganin ba ya rasa nasaba da faɗuwar darajar naira idan aka kwatanta da dalar Amurka.
Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Jigawa ta tabbatar da fashewar tankar mai a wani gidan mai da ke Dutse, babban birnin jihar a daren jiya Alhamis.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin rundunar SP Lawan Shiius Adam ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ko jikkata ba a haɗarin.
Ya ce tankar ta fashe ne da misalin ƙarfe 7 na dare a gidan man Shakkato da ke kan titin Kiyawa a Dutse a lokacin da tankar ke ƙoƙarin juye man cikin tankin ƙarƙashin ƙasa.
Kakakin rundunar ƴan sandan ya ce bayan samun labarin afkuwar lamarin, tawagar ƴan sandan yankin tare da masu kashe gobara suka yi gaggawar isa wurin inda aka yi nasarar kashe gobarar.
Fashewar tankar mai dai ba sabon abu bane a ƙasar baki ɗaya, inda ko a watan Janairun nan kaɗai an samu fashewar tankar mai aƙalla sau uku, wanda ya janyo asarar rayuka fiye da 80.
Ko a bara ma wata tankar mai ta faɗi a jihar ta Jigawa abin da ya kai ga mutuwar mutane 181.
Real Madrid da Manchester City za su sake fafatawa a kakar wasanni ta huɗu a jere kuma karo na biyar cikin shida a Gasar Zakarun Turai.
Kowace ƙungiya ta ci wasanni biyu, City ta doke Madrid har zuwa wasan karshe a shekarar 2020 - lokacin annobar korona - da kuma samun nasara kan Real ɗin a wasan kusa da karshe a 2023 inda suka je suka ɗauki kofin bayan doke Inter Milan.
Manchester City za ta gwabza da Real Madrid a neman tsallake wa zuwa gurbin ƴan 16 na Gasar Zakarun Turai.
Celtic kuma za ta fafata da Bayern Munich .
City da ta lashe Champions League a 2023, za ta karɓi bakuncin Real a filin wasanta na Etihad tsakanin 11 ko 12 na watan Febrairu, kafin balaguro zuwa Sifaniya makon da zai biyo baya.
Haka kuma Bayern Munich za ta ziyarci Celtic a zagaye na farko kafin ta karɓi bakuncinsu a Allianz Arena a wasan zagaye na biyu.
Ga yadda sauran jadawalin ƙungiyoyin ya kasance:
Majalisar dokokin Nicaragua ta amince da ƙudurin dokar da zai yi garanbawul kan yadda za a tafiyar da gwamnati da za su ƙarawa shugaba Daniel Ortega da maiɗakinsa sabbin karfi.
A watan Nuwamban bara ne dai Mr Ortega ya gabatarwa majalisar buƙatarsa, da sanar da ƙarin karfin ikon shi da maiɗakinsa a manyan jihohin Nicaragua.
Harwayau, garanbawul din zai ƙarawa rundunar sojin ƙasar ƙarfi, da tsoma bakin gwamnati kan ayyukan kafafen yaɗa labarai, da tsawaitsa wa'adin mulkin shugaban ƙasa zuwa shekaru 6.
A ƙarshe garanbawul ɗin ya ƙarawa mataimakiyar shugaban ƙasa Rosario Murillo, wadda mai dakin Shugaba Daniel Ortega ce, girma, wanda zai bata damar zama shugabar ƙasa ba tare da cikas ba idan Mr Ortega ya rasu kan karagar mulki kuma ba lokacin zabe ba.
Shugabannin ƙungiyar ƙasashen kudancin Afrika za su halarci taron gaggawa a yau Juma'a a birnin Harare na Zimbabwe, kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo.
An kashe da kuma jikkata wasu daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar SADC da aka tura Congo, a lokacin da ƴan tawayen M23 ke dannawa da ƙwace ikon birnin Goma.
Aƙalla dakaru 12 na kasashen Afrika ta Kudu da Malawi da Tanzania aka kashe a Congo.
Shugabannin za kuma su tattauna kan matakan da ya kamata a ɗauka domin kaucewa yaduwar rikicin a yankin, a daidai lokacin da M23 da ke samun goyon bayan Rwanda ke ƙara dannawa kudancin ƙasar.
Ministar harkokin wajen Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, ta ce Rwanda ta mamaye ƙasarta ba bisa ƙa'ida ba.
Therese Kayi-kwamba Wagner ta kara da cewa Rwanda na ƙoƙarin mamaye Congo da sauya gwamnatin da ke mulki.
Ta ce dakarun Rwanda ne suka mamaye arewacin yankin Kivu da ke birnin Goma, da kuma mayaƙan M23 amma ana fakewa da ƴan tawaye ne.
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan ƴan tawayen M23 sun karɓe iko da birnin Goma, da barazanar cigaba da dannawa domin karɓe babban birnin ƙasar Kinshasa.
Ms Wagner ta ce ana buƙatar sanya wa dakarun sojin Rwanda takunkumi, kuma MDD ta dakatar da dakarun wanzar da zaman lafiyar ƙasar daga ƙawancenta.
Shalkwatar tsaron Najeriya ta ce sojoji sun yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 358 tare da kama wasu 431 da ake zargi da ta'addanci a watan Janairun 2025 a cigaba da ayyukansu na yaƙi da ta'addanci a faɗin ƙasar.
A cikin sanarwar da daraktan yaɗa labaran shalkwatar Manjo Janar Edward Buba ya fitar, ya ce sojojin sun kuma kama mutane 59 da ake zargi da satar mai tare da ceto mutum 249 da aka yi garkuwa da su.
A yankin kudu maso kudu, Edward Buba ya ce dakarun sun daƙile satar mai da ya kai na fiye da naira biliyan biyu, sun kuma ƙwato makamai 370 da harsasai sama da dubu huɗu.
Manjo Janar Edwar ya kuma ce dakarun za su cigaba da yaƙi da ƴan ta'adda a faɗin ƙasar domin samar da yanayin tsaro ga ƴan ƙasa.