'Za mu hukunta masu hannu a kashe farar hula lokacin mulkin Assad'
A jawabin farko da ya yi wa ƴan kasa, aka kuma yaɗa a gidan talbijin ɗin ƙasar, shugaban gwamnatin riƙo a Syria Ahmed al-Sharaa ya yi alkawarin zai samar da ingantacciyar gwamnatin haɗaka da za ta yi tafiya da ƴan ƙasa maza da mata da kuma matasa.
Ahmad al-Sharaa ya yi alƙawarin hukunta masu hannu a kashe-kashen farar hula a zamanin mulkin shugaba Bashar al Assad, ko da kuwa sun tsere daga ƙasar.
A ziyarar da ya kai Syria, shugaban ƙasar Qatar Sheikh Tamim bin Hamad, ya ce ana buƙatar gaggauta samar da ingantacciyar gwamnati a Syria.