Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rawar da ƙungiyar ICRC ke takawa wajen musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas
- Marubuci, Alice Cuddy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News in Jerusalem
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Lamarin ya soma ne da kiran waya a wani wuri.
Da zarar an karɓi bayanai, wata tawagar ƙungiyar agaji ta Red Cross za ta saɓi hanya cikin motoci masu ɗauke da tambarin ƙungiyar domin ɗaukar Isra'ilawan a Gaza.
Kazalika sojojin Isra'ila da likitoci sun yi sahu-sahu a wurare da dama, suna jiran su dawo da su gida.
Sakin mutanen da ake tsare da su, wanda duniya ke bibiyar batun, ya zo ne bayan shafe tsawon watanni ana tattaunawa mai zafi da nufin kawo ƙarshen yaƙin da aka soma a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, lokacin da mayaƙan Hamas suka kashe wasu mutum 1,200 a Isra'ila tare da garkuwa da ƙarin mutum 251.
Watanni 15 bayan nan, fiye da Falasɗinawa dubu 47 aka kashe a Gaza, a cewar ma'aikatar lafiyar Hamas sannan wasu da dama sun rasa gidajensu a luguden wutar da Isra'ila ta yi.
A ƙarƙashin sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Isra'ila da Hamas, da aka soma aiwatarwa ranar 19 ga watan Janairu, za a saki Isra'ilawa 33 tare da haɗa su da iyalansu a zagayen farko, da zai ɗauki mako shida ana aiwatar da shi.
Za a yi haka ne domin musayar ɗaruruwan Falasɗinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila.
Idan aka saɓa sharuɗɗan yarjejeniyar, hakan barazana ce ga ragowar Isra'ilawan da har yanzu ke tsare wani lamari kuma da zai ƙara ingiza wutar yaƙin.
"Wannan ya wuce tuƙi kawai," in ji kakakin ƙungiyar ICRC, Sarah Davies.
"Ana ganin waɗannan ayyukan kamar masu sauƙi, amma a zahiri, suna da sarƙaƙiya kuma suna buƙatar tsauraran matakan tsaro domin rage hadarin da ka iya shafar mutanen da abin ya shafa.
Ƙungiyar agajin ta ICRC - wadda ke matsayin yar ba-ruwana kuma mai shiga tsakani a musayar, ta tanadi wata tawagar ƙwararru, wasu daga cikinsu sun taɓa yin irin wannan aikin a baya - duk da cewa wannan ya fi ƙalubale.
Tsari yana da muhimmanci
Akwai wasu bayanai da ƙungiyar ba za ta iya magana a kai ba a bainar jama'a saboda fargabar cewa hakan na iya barazana ga aikin ta fuskar tsaro.
Ms Davies ta ce yin tsari na da muhimmanci domin tabbatar da cewa an yi musayar lami lafiya.
Sun tanadi wasu hanyoyi na daban na zuwa yankunan Gaza, kasancewar hanyar da ta fi tsaro na iya sauyawa a kowane lokaci.
Daga cikin babbar fargabarsu ita ce barazana daga abubuwan fashewar da ba su tashi ba da gine-ginen da aka lalata da dandazon jama'a da suka zaku su koma gidajensu.
"Tawagarmu ta yi tsare-tsare don tunkarar abin da ka je ya zo," in ji ta.
"Muhimmin abu a gare mu shi ne mu iya mayar da duk mutanen da aka danka mana lami lafiya zuwa gidajensu."
"Daga abin da muka taɓa fuskanta a baya, a nan da wasu wuraren a duniya, mun san cewa batun zirga-zirga da samun bayanan ƙarshe na iya sauyawa a kowane lokaci, musamman a lokutan gudanar da ayyukan," in ji Ms Davies.
Likitoci da kwararru kan rage mummunan tasirin abubuwa masu fashewa, waɗanda suka samu horo wajen gano ɓurɓushin abubuwan fashewa, suna tafiya tare da tawagogin.
Yayin waɗannan ayyuka, wakilin ICRC zai riƙa tuntuɓar jami'an Isra'ila da Hamas da kuma masu shiga tsakani a kai a kai.
Hamas ta wallafa sunayen mutanen da ta saki a baya gabanin lokacin sakin su ta manhajar Telegram ba tare da bayyana takamaiman wurin da za a yi musayar ba.
"Na samu haske daga wani mai sayar da kaya cewa wani abu na faruwa a wata mahaɗa sannan mayaƙan al-Qassam na fareti," in ji wani ɗan jarida, game da mutanen farko da aka saki a Gaza a farkon watan nan.
Mutane sun taru domin kallo yayin da mayaƙan suka jeru - sahu-sahu, sai kuma aka soma yaɗa bayanai cewa mutum ukun farko da aka saki ƙarƙashin yarjejeniyar da aka cimma za su bayyana a nan.
"Da mutane suka gano cewa nan ne zai zama wajen da za su miƙa Isra'ilawan da Hamas ta tsare, sai mutane suka soma shewa," in ji shi.
"Sun riƙa yin kabbara cikin daga murya - wani abu da ke nuna cewa suna cike da farin ciki."
Dan jaridar yana wurin a lokacin da aka yi musaya ta biyu - a wani wuri na daban da ke Gaza - wanda ya bayyana ya fi tsari."
Mayaƙan sun samar da wani dandali da aka ajiye kujeru da tebura inda suka yi sahu-sahu domin raba Isra'ilawan da dandazon mutanen.
An yi amfani da motoci farare masu gilashi mai duhu wajen kai Isra'ilawan - sojoji mata huɗu - wajen.
An yi wa matasan matan bidiyo, yayin da suke yi wa Hamas godiya.
Sun hau dandalin inda suka ɗaga wa mutane hannu, daga nan kuma aka miƙa su ƙarƙashin kulawar ICRC.
Daga baya, kakakin Hamas Abdul Latif al-Qanou cikin wata sanarwa, ya ce "wuri da bayanan" musayar da aka shirya "na bayyana jajircewa da dagiya."
Ms Davies ta ce akwai wasu ɓangarorin musayar da suka fi karfin ikonmu.
"A kowane lokaci, ma'aikatan ICRC suna bakin ƙoƙarinsu don kare martabar mutanen da aka saki amma... yana da muhimmanci mutane su gane muna da iyaka kan abin da muke iya yi," in ji ta.
"Tabbatar da tsaro da kuma musayar mutanen da ke ƙarƙashin kulawarmu shi ne babban abin da muka fi bai wa fifiko."
An miƙa mutanen da aka saki ga dakarun IDF da ke wajen Gaza.
Kanar Dakta Avi Banov, mataimakin babban jami'in kula da lafiya na IDF, ya ce "Mun shirya tarbar mutanen da aka saki a wajen Gaza da wasu wuraren.
"Kullum muna cikin shiri saboda Hamas ba ta sanar da mu game da inda za su saki mutanen."
A tsallaken iyaka, an tanadi wuraren tarbar mutanen.
A wurin, akwai sojoji da likitoci da masu hidimta wa al'umma da kuma iyalan mutanen da aka saki.
Wani tsohon likita na rundunar sojin Isra'ila da ya yi aiki lokacin sakin wasu mutane a yarjejeniyar tsagaita wuta ta Nuwamban 2023 ya tuna yadda suka jira kusa da wata motar ɗaukar marasa lafiya a wani sansani da ke kusa da iyaka.
Yana cikin tawagogin ko ta kwana da aka tanada idan ɗaya daga cikin mutanen da aka saki suna buƙatar agaji inda ya ce akwai tsauraran dokoki game da yadda za a yi hulɗa da mutanen da suka dawo.
Ya tuna yadda aka shaida masu cewa idan suka kwashe su, kada ku yi masu tambayoyi, kada ku yi abubuwan da ba su dace ba, ku yi shiru kawai sannan idan mutanen da aka saki suka nemi wani abu ko suka tambaye ku, za ku ba su amsa kuma ku ba su abin da suke buƙata."
Ya ce yanayin sansanin na farin ciki ne. "Aiki ne mai muhimmancin gaske," in ji shi.
Kanar Dakta Banov ya ce aikin ya soma ne da gabatarwa tsakanin Hamas da likitoci.
Ana haɗa mutanen da aka saki da likita da malamar jinya da mai hidimta wa al'umma waɗanda ke masu rakiya har zuwa asibiti.
Ana shawartar iyalai da su bai wa mutanen ɗan lokaci tare da likitoci kafin haɗa su da yan'uwansu don ba su damar fahimtar cewa suna wurin da ke da tsaro.
Bai wa mutanen da aka saki kulawa
"Muna somawa da sinadarin vitamin, sai abinci da abin sha daidai gwargwado, sannan a yi batun iyali," in ji Kanar Dakta Banov.
Ya ce ana ƙoƙarin samar wa mutanen da aka saki wata kulawa don yin zaɓin kansu, da tambayoyi kamar: Za ka yi wanka kafin ko kuma bayan ka gana da iyayenka?"
Cikin mutanen da aka saki bakwai, ya ce galibinsu suna da rauni daga tashin bam, suna kuma fama da yunwa da matsalolin narkewar sinadaran gina jiki.
A yan makwanni masu zuwa, gawawwakin mutanen da suka mutu suma za su iso, inda aka yi tanadin miƙa su ɗakin gwaji domin gudanar da gwaje-gwaje kafin a yi jana'izarsu a Isra'ila.
Bayan samun kulawa ta farko, an miƙa mutanen da aka saki zuwa wani asibiiti cikin jirage masu saukar angulu.
Kanar Dakta Banov ya ce "Muna faɗa masu... za mu hau jirgi mai saukar ungulu don komawa gida. Sannan idan kuna so, za mu soma magana game da abin da kuka fuskanta."
A nan ne ake soma aikin farfaɗo da su daga tashin hankalin da suka shiga.