Aston Villa na neman aron Rashford

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar Aston Villa ta shiga sahun ƙungiyoyin da ke neman aron ɗan wasan gaban Manchester United, Marcus Rashford.

Tun ranar 12 ga watan Disamban bara rabon da Rashford mai shekara 27 ya buga wa Man U wasa, inda kocin ƙungiyar, Ruben Amorim ya mayar da shi ɗan benchi.

Wakilan Rashford sun gana da manyan ƙungiyoyi a turai domin nema masa ƙungiyar da zai je, amma dai har yanzu ɗan wasan bai yanke shawarar ƙungiyar da zai koma ba.

Sai dai har yanzu ba a yanke tsammanin zai cigaba da zama a ƙungiyarsa ba, duk da an fi ganin zai tafi wata ƙungiyar a matsayin aro.

Rahotanni sun nuna cewa Barcelona ce kan gaba wajen zawarcin ɗan wasan, inda ake tunanin daga cikin abubuwan da suke kawo tsaiko kan tafiyar ɗan wasan akwai batun alawus ɗinsa na fam 300,000 a mako wanda ba kowace ƙungiya ba ce za ta iya biya.